Ɗaliba ’yar shekara 15 daga Yobe ta lashe Gasar Muhawara ta Duniya
Published: 5th, August 2025 GMT
Wata ɗaliba ’yar shekara 15 daga Jihar Yobe, Rukayya Muhammad Fema, ta zama Gwarzuwar Shekarar 2025 a Gasar Muhawara ta Duniya ta Teen Eagle.
Rukayya ta yi zarra ne a wannan babbar gasa da ta gudana a birnin Landan na ƙasar Birtaniya, inda zaƙaƙuran ɗalibai daga ƙasashe 69 a faɗin duniya suka fafata a tsakaninsu.                
      
				
Jami’in Sadarwar Zamani na Gwamnatin Jihar Yobe, Yusuf Ali, ya bayyana cewa Rukayya ta samu kafa wannan tarihi ne a dalilin zurfin tunani da kuma kaifin basirarta da kuma fahimtar al’amuran duniya, duk kuwa da ƙarancin shekarunta.
Ɗalibar daga Kwalejin Nigerian Tulip International (NTIC), Rukayya, ta ɗauki hankalin alƙalan gasar da sauran jama’a saboda ƙarfin hujjojinta da ta gabatar da kuma iya bayani mai ganawarsa cikin natsuwa, lamarin da ya ba ta damar doke duk abokan karawarta.
Nafisa ta cancaci kyautar Dala 100,000 da gida da OON —Pantami NAJERIYA A YAU: Yadda Ayyuka Suka Ragu A Jihohi Bayan Kudin Shiga Ya KaruIta ce mutum ya biyu daga Jihar Yobe kuma daga makaranta tare da Nafisa Abdullah Aminu wadda ta zama gwarzuwa a ɓangaren Harshen Turanci a yayin gasar, inda suka wakilci Najeriya, ƙasa mai yawan al’umma sama da miliyan 200.
Nasararta nuna irin basirar da Allah Ya yi wa matasan Najeriya inda suke yin zarra a sassan duniya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Ɗaliba Gasar Muhawara Muhawara Rukayya Girma
এছাড়াও পড়ুন:
Gumi Ya Nemi Nijeriya Ta Katse Hulɗa Da Amurka Idan Trump Bai Janye Barazanar Sa Ba
ShareTweetSendShare MASU ALAKA  Manyan Labarai Ƙasashen Da Ba Su Yanke Hukuncin Kisa A Duniya Ba November 2, 2025 
 Manyan Labarai 2027: Yadda Gwamnoni Suka Yi Fatali Da Mataimakansu Wajen Zaɓo Waɗanda Za Su Gaje Su November 2, 2025 
 Manyan Labarai Wadi Al-Salam: Maƙabartar Musulmai Mafi Girma A Duniya November 2, 2025