Kwalejin NDA Ta Ce Jerin Sunayen Da Ke Yawo A Kafafen Sada Zumunci NA Jabu Ne
Published: 5th, August 2025 GMT
Kwalejin Horasda Hafsoshin Soja ta Kasa dake Kaduna -NDA ta karyata jerin sunayen wadanda suka yi nasara shiga kwalejin dake yawo a halin yanzu.
A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na makarantar, Manjo Mohammed Maidawa ya fitar ya ce jerin sunayen ba su fito daga Kwalejin NDA ba.
Don haka ya shawarci jama’a da su yi watsi da jerin sunayen da aka zayyana, domin za a buga sahihan jerin sunayen a cikin fitattun jaridu na kasa da kuma a yanar gizon NDA a kan https://NDA.                
      
				
PR/Usman Sani.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: jerin sunayen
এছাড়াও পড়ুন:
NARD Ta Yi Fatali Da Iƙirarin Gwamnatin Tarayya Na Ba Ta ₦43bn, Kuma Yajin Aiki Na Nan
“Wannan yajin aikin yana nan yana gudana, har sai an biya duk buƙatunmu mafi ƙaranci,” in ji shi.
NARD ta fara yajin aiki na sai baba-ta-gani a duk faɗin ƙasar a ranar Asabar, 1 ga Nuwamba, 2025, bayan abin da ta bayyana a matsayin gazawar gwamnati na cika jerin “mafi ƙanƙancin buƙatunta.” Wannan matakin dai tuni ya riga ya kawo cikas ga ayyuka a asibitoci mallakar gwamnatin tarayya da na jiha a faɗin ƙasar.
A halin yanzu, Ma’aikatar Lafiya da Jin Daɗin Jama’a ta Tarayya, a cikin wata sanarwa da Shugaban Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a, Alaba Balogun ya fitar, ya nace cewa, gwamnati ta saki kuɗaɗe kuma tana ci gaba da haɗin gwiwa da ƙungiyoyin ƙwadago don ganin an kawo ƙarshen yajin aikin ƙungiyar NARD.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA