Anthony Joshua zai yi dambe da tauraron YouTube Jake Paul a Disamba
Published: 18th, November 2025 GMT
Tsohon zakaran damben duniya a ajin masu nauyi, Anthony Joshua, zai fafata da tauraron YouTube, Jake Paul, a wani damben ƙwararru da za a yi a watan Disamba mai zuwa.
Joshua, ɗan ƙasar Birtaniya mai shekaru 36, wanda ya lashe kambun duniya ajin masu nauyi sau biyu, zai kara da Paul a cibiyar Kaseya Center da ke Miami.
Ana sa ran za a watsa damben kai tsaye a tashar Netflix a ranar 19 ga Disamba. Wadda za ta kasance fafatawa mai turmi takwas, kowanne na mintuna uku.
Joshua, wanda ya yi fafatawa uku a baya da nauyin sama da kilogram 113, yanzu dole ne ya rage nauyinsa zuwa ƙasa da kilogram 111.
Sannan dukkan abokan karawar za su saka safar hannu matsakaita, kamar yadda hukumar shirya gasar ta tanada.
Yanzu haka dai ana jiran samun tabbacin Joshua kan amincewa da wannan damben ko akasin haka, sai dai wasu rahotannin daga jaridar Sky Sports na nuna alamun tuni ya amince da tayin.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Kakakin Majalisar Taraba Da Ƴan Majalisa 15 Sun Fice Daga PDP Zuwa APC
Bonzena ya ƙara da cewa duk da cewa kafin yanzu APC ce ke da rashin rinjaye a majalisar, an ci gaba da aiki cikin zaman lafiya, amma yanzu yana farin cikin ganin cewa dukkan mambobin majalisar sun haɗe ƙarƙashin tsari daya da ya yi daidai da hangen shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA