Masu shigar da kara na ICC sun bukaci hukuncin daurin rai da rai a kan kwamandan RSF
Published: 18th, November 2025 GMT
Masu gabatar da kara a kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa (ICC) a ranar Litinin din nan sun bukaci kotun da ta zartar da hukuncin daurin rai da rai kan Ali Muhammad Ali Abd-Al-Rahman, wanda aka fi sani da Ali Kushayb, kwamandan rundunar Rapid Support Forces (RSF), saboda rawar da ya taka a ta’asar da aka aikata a lokacin harin da aka kai a yankin Darfur na kasar Sudan.
An samu Kushayb da laifuka 27 da suka hada da laifukan yaki da cin zarafin bil adama da suka hada da kisan kai, azabtarwa, fyade, da dai sauran manyan laifuka. Shari’ar dai ita ce shari’ar farko da aka shigar a gaban kotun ICC dangane da yakin Darfur.
A farkon wannan watan ne kotun ta ICC ta samu kara da ke da alaka da ta’addancin da aka yi a yankin Darfur a lokacin rikicin 2003-2004. An samu Kushayb da laifin bayar da umarnin kisa ga jama’a tare da kashe fursunoni biyu da gatari da kansa.
Lauya mai gabatar da kara Julian Nichols, yana magana a yayin zaman yanke hukunci na musamman, inda ya fallasa tare da kuma caccakar Kushayb a matsayin mai kisan kai da gatari. Ya ce Kushayb da kansa ya yi amfani da gatari ya kashe mutane biyu kuma ya kasance a sahun gaba wajen cin zarafin da aka yi a yankin Darfur fiye da shekaru 20 da suka gabata.
Mai gabatar da kara ya jaddada girman laifuffukan, yana mai nuni da irin rawar da Kushayb ya taka a ta’asar da aka aikata a farkon shekarun 2000 a matsayin shaida cewa ya kamata a yanke masa hukunci mafi tsanani a kotun.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka MDD ta amince da kudurin tura dakarun kasa da kasa zuwa Gaza November 18, 2025 Congo ta tsawaita haramcin fataucin ma’adinai a gabashin kasar November 18, 2025 Rasha: An dakile wani yunkurin kisan gilla kan Sakataren Majalisar Tsaron kasa November 18, 2025 Aref: Iran Tana Da Kyakkyawar Alaka Da Mambobin Kungiyar Hadin Gwiwa Ta Shanghai {SCO} November 17, 2025 Na’ini: Jagora Ne Da Kansa Ya Jagoranci Lamurra A Lokacin Yakin Kwanaki 12 Da Aka Kaddamar Kan Iran November 17, 2025 Mahukuntan Gaza Sun Yi Gargadin Bullar Bala’in Jin Kai A Yankin Da Ba A Taba Ganin Irinsa Ba November 17, 2025 Sheikh Na’im: Gwamnatin Lebanon Zata Yi Babban Kuskure Matukar Tabi Hanyar Sassauci November 17, 2025 Rushewar Ramukan Hako Ma’adinai Ta Kashe Mutane 32 A Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango November 17, 2025 Alummar Kasar Ecodo Sun yi Watsi Da Batun Sake Dawo Da Sansanin Sojin Amurka A Kasar November 17, 2025 Sojojin HKi Sun Kashe Wasu Falasdinawa Guda 2 A Sansanin Yan Gudun Hijira November 17, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
MDD ta amince da kudurin tura dakarun kasa da kasa zuwa Gaza
Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da daftarin kudurin Amurka, don ba da izinin kafa Rundunar Tsaro ta Kasa da Kasa (ISF) a Zirin Gaza.
Mambobi 13 daga cikin 15 na Majalisar sun amince da kudurin, inda Rasha da China suka kaurace wa kada kuri’ar.
Kudurin yana da nufin tura sojojin kasashen waje na wucin gadi don kula da tsaro, tallafawa sake ginawa da kuma kiyaye tsari a yankin. Daftarin ya yi kira ga rundunar ta yi aiki na tsawon shekaru biyu, tare da yiwuwar kara sabunta wa’adin aikinta wanda ya danganta ne da ci gaban da ake samu a kasa.
Kudurin ya kunshi abubuwa da yawa, ciki har da kare iyakokin Gaza, kare fararen hula, kare hanyoyin jin kai, da kuma horar da sabbin ‘yan sandan Falasdinu da aka tantance. Hakanan ya ba da izinin amfani da “dukkan matakan da suka wajaba” don cimma wadannan manufofi, gami da wargaza kungiyoyi masu dauke da makamai da kwace makamai marasa lasisi.
Muhimmin fasali na kudurin shine ƙirƙirar hukumar wucin gadi, wacce wani lokacin ake kira “Hukumar Zaman Lafiya,” wacce za ta yi aiki tare da rundunar kasa da kasa don taimakawa wajen gudanar da harkokin Gaza. Shirin ya kuma yi kira da a shigar da cibiyoyin kuɗi na duniya, kamar Bankin Duniya, don ba da kuɗaɗen ayyukan sake ginawa da kuma kula da gudanar da asusun tallafi na musamman.
Daftarin kudurin ya jawo suka daga ƙungiyoyin Falasɗinawa, waɗanda ke bayayya cewa ya ƙunshi wani nau’i na mulkin mallaka da Rashin ‘yancin kai, daga cikin kungyoyin da suka nuna damuwa kan kudirin har da kungiyar Hamas.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Congo ta tsawaita haramcin fataucin ma’adinai a gabashin kasar November 18, 2025 Rasha: An dakile wani yunkurin kisan gilla kan Sakataren Majalisar Tsaron kasa November 18, 2025 Aref: Iran Tana Da Kyakkyawar Alaka Da Mambobin Kungiyar Hadin Gwiwa Ta Shanghai {SCO} November 17, 2025 Na’ini: Jagora Ne Da Kansa Ya Jagoranci Lamurra A Lokacin Yakin Kwanaki 12 Da Aka Kaddamar Kan Iran November 17, 2025 Mahukuntan Gaza Sun Yi Gargadin Bullar Bala’in Jin Kai A Yankin Da Ba A Taba Ganin Irinsa Ba November 17, 2025 Sheikh Na’im: Gwamnatin Lebanon Zata Yi Babban Kuskure Matukar Tabi Hanyar Sassauci November 17, 2025 Rushewar Ramukan Hako Ma’adinai Ta Kashe Mutane 32 A Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango November 17, 2025 Alummar Kasar Ecodo Sun yi Watsi Da Batun Sake Dawo Da Sansanin Sojin Amurka A Kasar November 17, 2025 Sojojin HKi Sun Kashe Wasu Falasdinawa Guda 2 A Sansanin Yan Gudun Hijira November 17, 2025 Tawagar Wasan Wushu Ta Kasar Iran Ta Samu Lambobin Yabo 4 A Saudiya November 17, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci