Iran: An Bayyana Taron Gundumomin Dake Gabar Ruwan ” Caspian” Da Cewa Yana Bunaksa Alakar Kasashen Yankin
Published: 18th, November 2025 GMT
Fira ministan jamhuriyar Kalmykia mai kwarya-kwaryar cin gashin kai a tarayyar Rasha, Utshir Janibinov ya fada wa manema labaru a wurin taron gwamnonin gundumomin dake gabar ruwan “Caspian” cewa; Taron da aka yi wanda shi ne irinsa na farko yana da tasiri mai kyau wajen bunkasa alaka a tsakanin gundumomin gabar ruwan “Caspian”.
Taron na gwamnonin gundumomin da suke a gabar ruwan “Caspian” an yi shi ne dai a garin Rasht a gundumar Gilan dake nan Iran.
Mataimakin Fira ministan jamhuriyar Kalmykia ta tarayyar Rasha, ya bayyana jin dadinsa na halartar wannan taron a nan Iran.
A Yau Talata ne dai aka bude wannan taron wanda aka bai wa taken: ” Tekun Caspian A Matsayin Wata Gada Ta Bunkasa Alaka A Cikin Yanki.” Kuma zai zai gaba har zuwa kwanaki biyu anan gaba.
A wani gefen mataimakin ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa, ana sa ran halartar shugaban kasar Rash Vladmir Putin zuwa taron kungiyar kasashen dake gabar ruwan “Caspian” da za a yi a nan Iran a nan gaba.
Mataimakin ministan harkokin wajen na Iran ya fada wa kamfanin dillancin labarun “RIA Novosti” cewa; Ziyarar shugaba Valadmir Putin zuwa Iran domin halartar taron kungiyar kasashen gabar tekun “Caspian” yana cikin jadawalin aiki.
Sai dai mataimakin ministan harkokin wajen na Iran bai bayyana wa’adin gudanar da wannan taron ba.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Nijar: An Dakatar Da Ayyukan Kungiyoyin Agaji Da Dama November 18, 2025 Lebanon: Mutum Daya Ya Yi Shahada Sanadiyyar Harin Sojojin “Sahayoniya A Garin Bint-Jubail November 18, 2025 Brazil: Al’ummun Yankunan Karkara Na Amazon Sun Yi Gangami A Wurin Taron MDD Akan Muhalli November 18, 2025 Sojojin Najeriya Sun Karyata Cewa “ISWAP” Ta Kashe Wani Babban Jami’i Mai Mukamin Birgediya November 18, 2025 Najeriya ta Fara tattaunawa da Amurka kan zargin yi wa Kiristoci kisan kiyashi November 18, 2025 Hamas Ta yi Watsi Da Amincewa Da Kudurin Amurka Da Kwamitin Tsaro Ya yi Kan Gaza November 18, 2025 Afrika ta Kudu Ta yi Gargadi Game Da Duk Wani Yunkuri Na Fitar Da Falasdinawa Daga Yankin Gaza November 18, 2025 Tsohon jami’an MDD Yayi Tir Da Amincewa Da Kudurin Amurka A Kwamitin Sulhu Kan Gaza November 18, 2025 Mataimakin Shugaban Iran Na Daya Ya Gana Da Prime Ministan Rasha A Birnin Mosko November 18, 2025 Ministan tsaron Iran na Ziyara a UAE don karfafa dangantakar tsaro tsakanin kasashen yankin November 18, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: gabar ruwan
এছাড়াও পড়ুন:
Firaministan Sin Ya Isa Rasha Domin Halartar Taron SCO
Firaministan kasar Sin Li Qiang ya isa birnin Moscow na kasar Rasha a yau Litinin domin halartar taro karo na 24 na majalisar shugabannin kasashe mambobin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai (SCO).
Bisa gayyatar da firaministan kasar Rasha Mikhail Mishustin ya yi masa, Li zai halarci taron na SCO a ranakun 17 da 18 ga watan Nuwamba. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
ADVERTISEMENT ShareTweetSendShare MASU ALAKA