Aminiya:
2025-11-18@21:28:36 GMT

Mutane 7 sun mutu a hatsarin mota a Jigawa

Published: 18th, November 2025 GMT

Wani mummunan hatsarin mota da ya faru a Jihar Jigawa ya yi sanadin mutuwar mutane bakwai ciki har da direban motar tare da jikkata wasu 11.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Shiisu Lawan Adam, ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa da ya aike wa manema labarai a Dutse.

Anthony Joshua zai yi dambe da tauraron YouTube Jake Paul a Disamba Gwamnonin Arewa sun yi Allah-wadai da sace ɗalibai mata a Kebbi

Ya ce hatsarin ya afku ne da misalin ƙarfe 4:30 na yammacin Lahadi, 16 ga Nuwamba 2025, a ƙauyen Jigawan Kurma da ke kan titin Kiyawa zuwa Azaren Jihar Bauchi.

A cewar SP Shiisu, “Mota kirar Hummer ce da ta taso daga Kano zuwa Potiskum ɗauke da fasinjoji 18. Hatsarin ya faru ne bayan fashewar tayoyi biyu, sakamakon gudun wuce sa’a da direban yake yi.”

Ya ƙara da cewa sauran 11 da suka samu munanan raunuka an garzaya da su babban asibitin Birnin Dutse, inda aka sallami huɗu daga cikinsu bayan samun kulawa.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Hatsari Jihar Jigawa

এছাড়াও পড়ুন:

Hauhawar farashi ya ƙara raguwa a Nijeriya — NBS

Hukumar ƙididdiga ta Najeriya (NBS) ta ce hauhawar farashin kayyayaki a ƙasar ya ragu zuwa kashi 16.05 cikin 100 a watan Oktoban 2025.

Cikin rahoton wata wata da hukumar ke fitarwa, ta ce hauhawar farashin ya ragu ne da kashi 1.97 idan aka kwatanta da kashi 18.02 da aka samu a watan Satumba.

’Yan Majalisar Dokokin Taraba 16 sun sauya sheka daga PDP zuwa APC An ɗaura auren Sanata Kawu Sumaila da wata jami’ar soji a Kano

A watanin baya-bayan an riƙa samun raguwar hauhawar farashin kayyaki a ƙasar.

Aminiya ta ruwaito cewa, tun dai daga watan Yunin bana, hauhawar farashin kayayyaki ke ci gaba da sauka a ƙasar har kawo yanzu.

Ana iya tuna cewa, tun watanni kadan da suka gabata ne hauhawar farashin ya riƙa raguwa bayan umarnin da Shugaba Bola Tinubu ya bayar na karya farashin kayan abinci ƙasar.

Kafin umarnin shugaban ƙasar, an dai yi ta kiraye-kirayen gwamnatin Nijeriya ta ɗauki matakan rage hauhawarar farashi domin magance tsadar rayuwa da ake fuskanta a ƙasar.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • PDP Ba Ta Mutu Ba Duk Da Rikicin Da Ta Ke Fama Da Shi – Anyanwu
  • GGCSS Maga: Halin da iyaye ke ciki bayan sace ’ya’yansu
  • Mayaƙan ISWAP sun kashe kwamandan soji a Borno
  • Hauhawar farashi ya ƙara raguwa a Nijeriya — NBS
  • ’Yan Majalisar Dokokin Taraba 16 sun sauya sheka daga PDP zuwa APC
  • Masu ibadar Umara 42 sun mutu a hatsarin mota a hanyar zuwa Makka
  • Mutane 42 Sun Mutu A Wani Hatsarin Tankar Dizal Da Motar Masu Umrah A Hanyar Makka
  • Fasinjojin Da Kasar Sin Ta Yi Jigilarsu Ta Jirgin Kasa Daga Janairu Zuwa Oktoba Sun Kai Biliyan 3.95
  • Meke Kawo Yanke Hukunce-hukunce Masu Karo Da Juna Daga Kotuna?