UNICEF: Akalla yara 28 ne ke mutuwa a kowace rana a Gaza sakamakon harin Isra’ila da yunwa
Published: 5th, August 2025 GMT
Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya fada a ranar Litinin cewa kimanin yara 28 ne ake kashewa a kullum a zirin Gaza sakamakon harin bama-baman Isra’ila da kuma yunwar da ta jefa a l’ummar yankin a ciki.
Kungiyar ta yi bayanin a cikin wata sanarwa da ta fitar cewa, yaran Gaza na fuskantar kisa “sakamakon tashin bama-bamai, rashin abinci mai gina jiki, yunwa, da kuma rashin muhimman kayan agaji da ayyukan kiwon lafiya.
UNICEF ta jaddada cewa yara a Gaza na bukatar abinci, ruwa, magunguna, da kuma kariya. Mafi mahimmanci kuma shi ne, suna bukatar tsagaita bude wuta cikin gaggawa.”
A wani labarin kuma, Majalisar Dinkin Duniya ta bayar da rahoton cewa, sama da mutane 1,500 ne aka kashe a zirin Gaza tun a watan Mayun da ya gabata, a lokacin da suke kokarin samun abinci, a hare-haren da Isra’ila ta ke kaiwa a wuraren da ake yin amfani da su wajen rarraba kayan agaji, ko kuma ta hanyar kai harin a kan ayarin motocin Majalisar Dinkin Duniya.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Baghaei : Ziyarar Pezeshkian a Pakistan ta bude wani sabon Shafin alaka August 5, 2025 Afirka ta Kudu ta zayyana matakan tallafi ga ‘yan kasuwa na cikin gida a matsayin martani ga harajin Trump August 5, 2025 Hamas ta musanta kalaman Witkoff game da batun mika makamanta August 5, 2025 Araqchi: Namijin kokarin al’ummar Iran abin yabawa ne August 4, 2025 Khatibzadeh: Iran ba za ta amince da saryar da hakkokinta ba a duk wata tattaunawa da Amurka August 4, 2025 Rahotonni: Agajin Jin kai Da Ake Jefawa Ta Sama A Gaza Ba Shi Da Tasiri August 4, 2025 Wa’adin Da Shugaban Amurka Ya Gindaya Na Kawo Karshen Yaki A Ukraine Ya Karato Ba Tare Da Alamun Karewarsa Ba August 4, 2025 Sojojin Somaliya Sun halaka Mayakan Kungiyar Al-Shabab Fiye Da Hamsin A Kudu Maso Yammacin Mogadishu August 4, 2025 Pakisatan: Iran Ce Madogara Ga Al-ummar Musulmi August 4, 2025 Wakilin Hukumar FAO A Iran Yace Sauyin Yanayi Ya shafi Dukkan Yankin August 4, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Dangantaka Na Kara Tsami Tsakani Faransa Da Isra’ila Kan Amincewa Da Falasdinu .
Matsayar kasar Faransa na amincewa da Falasdinu a matsayin kasa a hukumance a babban taron zauren majalisar dinkin duniya dake zuwa, ya kawo tarnaki sosai a alakar diplomasiya tsakanin ta isara’ila.
Shugaban kasar faransa Emmanuel Macron ya sanar tun a watan yuli cewa faransa za ta amince da falasdinu a matsayin kasa, za ta shiga cikin jerin kasashe da ke goyon bayan kafa kasashe biyu masu yancin kai.
Ana sa bangaren ministan harkokin wajen Isra’ila Gidion Saar ya gargadi Macron da cewa ba’a maraba da shi a Isra’ila har sai faransa ta canza shirinta na amincewa da falasdinu ,yace wannan shirin zai cutar da tsaron Isra’ila kai tsaye.
Shi ma wani babban jami’in tarayyar turai yayi gargadin cewa alaka tsakanin faransa da isara’ila tana kara tabarbarewa sosai, kuma ana kallon Macron a matsayin kanwa uwar gami.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Sojojin HKI 12 Ne Suka Halaka Ko Suka Ji Rauni A Gaza September 19, 2025 Amurka Ta Yi Amfani Da Kujeran Veto Don Hana Zaman Lafiya A Gaza September 19, 2025 HKI Ta Kai Hare-Hare Kan Wurare Har 5 A Kudancin Kasar Lebanon September 19, 2025 Majiyoyin Diblomasiyya Sun Ce Washington Zata Jagoranci Turawa A Tattaunawa Da Iran September 19, 2025 Iran Ta Bukaci Kwamitin Tsaro Na MDD Ta Zabi Diblomasiyya Kan Fito Na Fito September 19, 2025 Yahudawa Suna Ci Gaba Da Yin Hijira Zuwa Wajen HKI September 18, 2025 ‘Yan Gwgawarmaya Sun Kashe Sojojin HKi 4 A Gaza September 18, 2025 An Halaka Sojojin HKI Biyu Ta Hanyar Sukarsu Da Wuka A Kusa Da Iyakar Jordan September 18, 2025 Husi: Kai Wa Kasar Katar Hari Gargadi Ne Ga Al’ummar Musulmi September 18, 2025 Shugaban Kasar Iran Ya bayyana Yadda Hadin Gwiwa Tsakanin Iran Da Rasha Ya Kawo Ci Gaba Tsakaninsu September 18, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci