Gobara ta laƙume rayukan yara biyu ’yan gida ɗaya a Ribas
Published: 17th, November 2025 GMT
Gobara ta laƙume rayukan wasu yara biyu ’yan gida ɗaya a unguwar Rumuola da ke ƙaramar hukumar Obio/Akpor a Jihar Ribas.
Bayanai sun ce ibtila’in ya auku ne da misalin ƙarfe 10 na dare a ranar Lahadi, lokacin da gobarar ta tashi a ɗaya daga cikin wasu ɗakunan haya da mahaifiyar yaran ta kulle ’ya’yanta huɗu ta tafi sayen kayan girki.
A cewar mazauna yankin, cikin yaran huɗun, biyun da suka riga suka kwanta barci sun ƙone su kurmus, yayin da sauran biyun da ke farke suka samu damar tserewa.
Aminiya ta ruwaito cewa, mazauna yankin da sun ankara da gobarar ce bayan sun hangi yadda hayaƙi ya turnuƙe sararin samaniya, lamarin da ya sa suka gaggauta kiran ma’aikatar kashe gobara kuma suka kawo dauki domin tarar hanzarin lamarin na hana gobarar bazuwa zuwa sauran gidaje.
Haka kuma, wani mazaunin yankin ya musanta jita-jitar da ake yadawa a kafafen sada zumunta cewa gobarar ta tashi ne a harabar wata kwaleji ta Captain Elechi Amadi da ke Rumuola, yana mai bayyyan cewa lamarin ya faru ne a bayan makarantar, inda ake da dogayen gine-gine da ke ɗauke da iyalai sama da 27.
Ya bayyana takaicin cewa dubban mutane sun rasa matsugunni a sanadiyar gobarar wadda ta ƙone dukiyoyin da darajarsu ta kai miliyoyin naira.
Mai magana da yawun ’yan sanda a Jihar Ribas, SP Grace Iringe-Koko, ta tabbatar da faruwar lamarin, tana mai cewa yaran biyu da suka mutu shekarunsu na haihuwa ba su gaza biyar da tara ba.
Ta ce an fara bincike domin gano musabbabin gobarar, kana an gayyaci mahaifiyar yaran domin amsa tambayoyi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Gobara Jihar Ribas
এছাড়াও পড়ুন:
Masu ibadar Umara 42 sun mutu a hatsarin mota a hanyar zuwa Makka
Wasu masu ibadar Umara 42 sun mutu bayan da motarsu ta yi taho-mu-gama da wata tankar mai a kusa da birnin Madina da ke kasar Saudiyya.
Dukkan masu ibadar ’yan kasar Indiya ne, kuma hatsarin ya ritsa da su ne a kan hanyarsu ta zuwa Makka bayan kammala ziyara a birnin Madina.
Ministan harkokin wajen Indiya Dakta S. Jaishankar ya bayyana cewa mutum daya daga cikin fasinjojin ya tsallake rijiya da baya a hatsarin da ya auku da tsakar daren Litinin.
Hatsarin ya auku ne a bayan da motar safa mai daukar mutum 43 da masu ibadar suke ciki ta yi karo gaba-da-gaba da wata tankar mai.
’Yan ta’adda sun sace dalibai 25 a dakunan kwanansu a Kebbi NELFUND ya raba wa ɗalibai tallafin karatu na Naira Biliyan 116A sakon ta’azaiyyarsa ga iyalan mamatan, Ministan harkokin wajen Indiya, ya bayyaan cewa ofisoshin jakadancin kasar ke Saudiyya, na bayar da cikakken tallafi ga masu Umarar da hatsarin ya rusta da su.