Babban lauya kuma mai kare haƙƙin ɗan Adam, Femi Falana (SAN), ya bai wa ƴan Nijeriya shawara da su kai Gwamnatin Tarayya ƙara don neman a mayar musu da kuɗin fansar da suka biya yayin da aka yi garkuwa da ƴan uwansu. Ya ce gwamnatin ta kasa sauke babban nauyin da kundin tsarin mulki ya ɗora mata na kare rayuka da dukiyoyin ƴan ƙasa.

Falana ya yi wannan jawabi ne a lokacin buɗe sabuwar shekarar Shari’a ta Tsangayar Shari’a ta Jami’ar Yakubu Gowon da ke Abuja. Ya ce yawaitar garkuwa da mutane a sassan ƙasar nan ya nuna gazawar gwamnati wajen tabbatar da kariya kamar yadda kundin tsarin mulki da Yarjejeniyar Afrika kan Haƙƙin Dan Adam suka tanada. Ya kuma soki bambancin yadda hukumomi ke tunkarar lamarin, yana mai cewa ana hanzari ne idan manyan mutane aka sace, amma an bar talakawa cikin tsoro da halin ƙaƙa-niki-ka-yi.

Falana Ya Kai Karar Gwamnatin Tarayya Da Jihohi Kan Yara Da Ba Su Zuwa Makaranta Tsauraran Manufofin Tattalin Arziƙin Tinubu Ya Ƙara Yawan Matalauta – Falana

Falana ya jaddada cewa kai gwamnati kotu zai taimaka wajen kare haƙƙin waɗanda suka biya kuɗin fansa, tare da matsa wa gwamnati ta inganta tsaro cikin gaggawa. Sabon rahoton Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ya nuna cewa ƴan Nijeriya sun biya Naira Tiriliyan 2.23 a matsayin kuɗin fansa tsakanin Mayu 2023 zuwa Afrilu 2024. Rahoton Crime Experience and Security Perception Survey (CESPS) na 2024 ma ya nuna cewa fiye da mutum miliyan 2.2 an yi garkuwa da su a wannan lokaci, tare da matsakaicin kuɗin fansa na kusan ₦2.7m ga kowane mutum.

ADVERTISEMENT

A cewar masana tsaro, garkuwa da mutane ya koma kasuwancin da ke samar da riba ga miyagu, lamarin da ke buƙatar tsauraran matakai daga gwamnati tare da ingantaccen tsari da haɗin gwuiwar jami’an tsaro.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ƴan Bindiga Sun Sace Mutane 14 A Wani Sabon Hari A Zamfara November 16, 2025 Manyan Labarai Wata Ƙungiya Ta Fara Bin Digdigin Takardun Karatun Matawalle November 16, 2025 Nazari Meke Kawo Yanke Hukunce-hukunce Masu Karo Da Juna Daga Kotuna? November 16, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Kotu ta sake hana PDP gudanar da babban taronta na ƙasa

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta sake hana jam’iyyar PDP gudanar da babban taronta na ƙasa da ta ke shirin yi.

Alƙalin kotun, Mai Shari’a Peter Odo Lifu, ya yanke hukuncin ne a ranar Juma’a.

Mutfwang ya musanta raɗe-raɗin sauya sheƙa zuwa YPP Mutfwang ya musanta raɗe-raɗin sauya sheƙa zuwa YPP

Ya ce taron da aka tsara yi a Ibadan a ranar 15 da 16 ga watan Nuwamba ba za a gudanar ba sai an bai wa tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, damar sayen fom ɗin takarar kujerar shugaban jam’iyyar na ƙasa.

Alƙalin ya kuma umarci INEC da kada ta sanya baki ko ido a kan taron har sai an bai wa Lamido damar sayen fom.

Lifu, ya ce PDP dole ta bi dokokinta ta kuma bai wa duk ’ya’yan jam’iyyar waɗanda suka cancanta damar yin takara.

Ya ce ba daidai ba ne a hana Lamido sayen fom ɗin takara.

Lamido, ya garzaya kotu ne bayan hana shi sayen fom ɗin takarar shugabancin jam’iyyar.

Alƙalin ya ƙara da cewa PDP ba ta fitar da sanarwar da doka ta tanada ba, kuma ba ta bayar da kwanaki 21 na sanarwa kafin gudanar da taron kamar yadda yake a tsarinta.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Laftanal Yarima Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Abuja
  • DRC: An Kulla Yarjejeniyar Zaman Lafiya A Tsakanin Gwamnati Da Kungiyar M23
  • Gwamnatin Gombe ta bai wa alƙalai da Khadi-Khadi kyautar sabbin motoci 16
  • Gwamnati, UNICEF da ’yan jarida sun haɗa don yaƙar cututtukan da aka manta da su a Gombe
  • Mayaƙan ISWAP sun sace Janar sun kashe sojoji a Borno
  • Yadda ’yan bindiga suka kashe banga 16 suka sace mutane 42 a Neja
  • ’Yan bindiga sun kashe ’yanga 16 sun sace mutane 42 a Neja
  • Gwamnati na jefa makomar ilimi cikin hatsari — ASUU
  • Kotu ta sake hana PDP gudanar da babban taronta na ƙasa