Aminiya:
2025-11-18@12:12:45 GMT

Yanzu-yanzu: Fada ya barke a Hedikwatar Jam’iyyar PDP

Published: 18th, November 2025 GMT

An ba wa hamata iska a Hedikwatar Jam’iyyar PDP da ke Abuja a tsakanin bangarorin da ke hamayya da juna.

Fadan ya barke ne bayan bangarorin sun halarci ofishin domin gudanar da tarukansu daban-daban a safiyar Talata.

Idan ba a manta ba, bangaren Ministan Abuja, Nyesom Wike, wadanda uwar jam’iyyar ta dakatar a yayin babban taronta na kasa da ya gudana  a karshen mako ya kira taron gaggawa a yau Talata a hedikwatar Jam’iyyar da ke Wadata Plaza a Abuja.

 

 

উৎস: Aminiya

এছাড়াও পড়ুন:

Fintiri ya yi watsi da korar Wike daga PDP

Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na Jihar Adamawa, ya yi watsi da hukuncin da Jam’iyyar PDP ta yanke na korar Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, daga jam’iyyar.

Aminiya ta ruwaito yadda PDP ta kori Wike, Sanata Samuel Anyanwu da tsohon Gwamnan Ekiti, Ayodele Fayose, a yayin babban taron PDP da aka gudanar a Ibadan, Jihar Oyo.

Cif Olabode George ne, ya gabatar da ƙudirin korarsu, kuma Shugaban PDP na Jihar Bauchi, Samaila Burga, ya mara masa baya.

Sai dai bayan sanarwar, Gwamna Fintiri ya fitar da wata sanarwa, wadda ya nesanta kansa daga matakin da jam’iyyar ta ɗauka.

Ya ce ba ya goyon bayan korar da aka yi wa Wike, domin hakan zai ƙara haifar da rikici a cikin jam’iyyar.

“Ina son na bayyana a fili cewa ba na goyon bayan korar Ministan Babban Birnin Tarayya, Wike daga PDP. Wannan mataki ba zai amfani jam’iyya ba. Ba zan shiga cikin abin da zai ƙara ruguza jam’iyya ba,” in ji shi.

Fintiri, ya ce yana ganin zaman lafiya da haɗin kai sun ɗore a jam’iyyar PDP.

Ya roƙi ’ya’yan jam’iyyar da su mayar da hankali kan yin sulhu maimakon ƙara haddasa rikice-rikice.

“Na yi imani cewa sulhu da fahimtar juna su ne hanyar da ta fi dacewa. Ina kira ga kowa ya yi aiki don ganin an samu haɗin kai a cikin jam’iyya.”

Fintiri, na cikin gwamnoni huɗu da suka halarci taron, kuma shi ne Shugaban Kwamitin Shirya Taron.

Gwamnonin Jihar Osun, Ademola Adeleke; Taraba, Agbu Kefas; da Ribas, Siminalayi Fubara ba su halarci taron ba.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • PDP Ba Ta Mutu Ba Duk Da Rikicin Da Ta Ke Fama Da Shi – Anyanwu
  • Kakakin Majalisar Taraba Da Ƴan Majalisa 15 Sun Fice Daga PDP Zuwa APC
  • Hamas Da Sauran Bangarorin Falasdinawa Sun yi Watsi Da Shirin Aikewa Da Dakarun Kasashen Waje A Yankin Gaza
  • Ba Mu Samu Labarin Kai Wa Laftanar Yerima Hari Ba – Ƴansanda
  • NAJERIYA A YAU: Matsayar Doka Kan Taron Da Jam’iyyar PDP Ta Gudanar
  • Laftanal Yarima Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Abuja
  • Ƴan Bindiga Sun Sace Mutane 14 A Wani Sabon Hari A Zamfara
  • Ba da yawuna PDP ta kori Wike ba — Muftwang
  • Fintiri ya yi watsi da korar Wike daga PDP