2025-11-16@18:18:03 GMT
إجمالي نتائج البحث: 32
«tinkarar sauyin yanayin duniya»:
Yanzu haka ana gudanar da taron bangarorin da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar tinkarar sauyin yanayin duniya ta Majalisar Dinkin Duniya, karo na 30, wato “COP 30” a takaice, a birnin Belem na kasar Brazil, inda a ranar Juma’a 14 ga wata aka kira wani taro a gefe mai taken “Dabarun Kasar Sin Na Tinkarar Sauyin Yanayin Duniya”, don bayar da fasahohin Sin a fannin daidaita al’amura a kokarin sabawa da sauyin yanayi. A wajen taron, shugaban tawagar kasar Sin a taron COP30, kana mataimakin ministan muhallin halittu na kasar, Li Gao, ya ce sauyin yanayin duniya wani babban kalubale ne da daukacin bil Adama ke fuskantarsa, inda a nata bangare, kasar Sin ta tsaya kan mai da hankali kan...
“Haka kuma an kama wata mata mai shekaru 34 da ake zargi da hannu a lamarin, tare da wasu masu gidan marayu guda biyu da ke Abuja da Jihar Nasarawa, inda aka gano wasu yaran da ake kyautata zaton an yi safarar su. Wasu daga cikin gidajen marayun da aka gano ana amfani da su ne a matsayin cibiyoyin ajiye yara, inda ake jiran ‘kwace’ ko sayar da su da sunan daukar nauyin marayu.” Ya ce, “An gano gidajen marayu guda hudu da ke Kaigini, Kubwa Edpressway Abuja; Masaka Area 1, Mararaba kusa da Abaca Road; da kuma Mararaba bayan Kasuwar Duniya suna da alaka da wannan kungiya, kuma ana ci gaba da bincike a kansu.” Ya kara da cewa,...
Wannan nasara mai ban mamaki ta sa kungiyar Niger Tornadoes ta koma matsayi na biyu a teburin gasar, inda yanzu take da maki 17 a kasan Nasarawa United. Hakazalika, sakamakon ya bar Kano Pillars a cikin mawuyacin hali a gasar yayin da ta ke matsayi na 19 da maki 8 kacal. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Gwarzon Kamfanin Samar Da Kayayyakin Gida Na Mai Da Gas Na Shekarar 2025 Kamfanin GEIL October 26, 2025 Manyan Labarai Gwarzon Ɗan Majalisa Na Shekarar 2025: Benjamin Okezie Kalu October 26, 2025 Manyan Labarai Gwarzon Banki Na Shekarar 2025 Bankin Providus October 25, 2025
Aƙidar Dr Bello abu ne mai saƙin gaske kuma akwai hikima a ciki sosai. Shi ne kuma samar da ingantacciyar kiwon lafiya wand aba wai sai kana da kuɗi mai yawa ba. Tsarinsa shi ne haɗa yi wa mutane aiki, ilimantar da su tared fda kuma tsugunar da su. Wannan mataki ne da yake tabbatar da an samun cikin gaggawa da kuma sauƙin gaske.. Daga Legas zuwa Kano, daga Ondo zuwa Kuros Riba, kungiyar CFDF tana tafiya da kayan aiki na tafi da gidanka da kuma rundunar likitoci masu tiyata na sa kai, masu aikin jinya, da ma’aikatan jinya. Kowace manufa asibiti ce mai motsi – duba marasa lafiya, yin hadaddun tiyata, da bayar da shawarwari da tallafin abinci mai...
“Gudanar da harkokin kuɗaɗe ba bayar da taimako ba ne, haƙƙi ne.” Ƙoƙarin Cike Gibi Tare Da Gina Makoma Mai Kyau Lokacin da OPay ya shiga fannin harkokin kuɗaɗe na zamani a Nijeriya, ƙalubalen ya kasance bayyane suke, kusan rabin yawan mutanen Nijeriya ba su da damar samun shiga harkokin kuɗaɗe. Waɗanda suka kafa kamfanin sun gano cewa yawancin ‘yan Nijeriya sun yin isa da bankuna, tsarin yana haifar da jinkiri, kuma tsarin yana da barazana mai yawa. OPay ta kasance mai sauƙin gudanarwa, wani tsarin kuɗi na wayar hannu da ya dace da rayuwar yau da kullum ba tare da tangarda ba. Daga biyan kuɗi ta walat zuwa biyan kuɗin kayayyakin more rayuwa, daga sayan katin waya zuwa mu’amaloli...
Fiye da gidaje dari biyu da tamanin (280) a Karamar Hukumar Lafia sun samu kwandunan ajiyar shara (trash bins) domin inganta kula da tsaftar muhalli da rage datti a babban birnin jihar. An gudanar da rabon ne a birnin Lafia, ƙarƙashin jagorancin Kwamishinar Muhalli da Albarkatun Ƙasa ta Jihar Nasarawa, Dr. Margaret Elayo. Shirin wayar da kai da rabon kwandunan ya shafi wasu kananan hukumomi da suka haɗa da Karu, Keffi, Akwanga, Wamba, Obi, da Keana, inda Lafia ta fi kowa samun masu cin gajiyar wannan shiri. A yayin taron, Dr. Margaret Elayo ta bayyana damuwarta kan yadda datti ke ƙaruwa a tituna da magudanan ruwa, lamarin da ke haifar da barazana ga lafiya da muhalli. ...
Lokacin da mai gabatar da shirin, Seun Okinbaloye, ya tambaye shi ko ya damu saboda yawancin ‘yan ƙabilar Ibo na goyon bayan Obi, Kalu ya cd, “A’a, kawai ban son yin magana a kansa.“Idan kana son na tattauna a kan Peter Obi, to ka gayyace mu duka mu biyun mu zauna a tattauna ta awa biyu; kai za ka zauna a tsakiya, shi a gefe ɗaya, ni kuma a ɗaya gefen. Sai mu tattauna.”“Peter Obi ba jagorana ba ne. Ni ne ɗan siyasa mafi shahara daga yankin Kudu maso Gabas. Na taɓa lashe jihohi biyu a ƙarƙashin jam’iyyar PPA, kuma na taɓa tsayawa takarar shugaban ƙasa.“Kuri’u na miliyan 4.9 na samu a shekarar 2007 har yanzu suna nan. Jam’iyyata ta...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A wani samame na kwanaki hudu na hadin gwiwa na yakar shaye-shayen miyagun kwayoyi da tashe-tashen hankula a kan tituna, rundunar hadin guiwa mai wanzar da zaman lafiya da farfado da matasa ta jihar Kano, ta kama wasu mutane 78 da ake zargi a manyan wuraren da ke jihar. A wata sanarwar manema labarai da jami’in hulda da jama’a na hukumar NDLEA a Kano Sadiq Mohammad Maigatari ya fitar, ya ce rundunar ta yi aiki tare da hadin gwiwar hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA da kuma rundunar ‘yan sandan Najeriya. Wannan farmakin dai ya shafi fitattun wuraren da ake aikata miyagun laifuka da suka hada da Mariri Yan’itace, Fagge, Badawa,...
Jarin Da Sin Ta Zuba Kai Tsaye A Kasashe Cikin Shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya Ya Karu Da Kashi 22.9% A 2024
A yau Litinin, wasu rahotanni na cewa, yayin wani taron manema labaru na musamman kan zuba jari ga sassan ketare da aka gudanar a taron tattauna harkokin cinikayya da zuba jari na kasa da kasa na Sin karo na 25, cewa a shekarar 2024 adadin jarin da kasar Sin ta zuba kai tsaye a kasashen da suka shiga shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” ya kai dalar Amurka biliyan 50.99, adadin da ya karu da kashi 22.9 bisa dari idan aka kwatanta da makamancin lokaci na shekarar 2023. A dai yau din, ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin, da hukumar kididdiga ta kasar, da hukumar kula da musayar kudin waje ta kasar, sun fitar da sanarwar “kididdiga ta shekarar 2024 kan...
Babbar jam’iyyar adawa a Nijeriya, PDP, ta keɓe wa kudancin Nijeriya tikitin takarar kujerar shugaban ƙasa a Zaɓen 2027. Jam’iyyar ta tabbatar da haka ne a babban taron Kwamitin Zartarwa karo na 102 da ta gudanar ranar Litinin a Abuja. PDP ta tabbatar da Damagum a matsayin shugabanta na ƙasa Wata mata ta mayar da N4.8m da aka yi kuskuren tura wa asusunta a Maiduguri A baya-bayan nan dai wasu masu ruwa da tsaki kan sha’anin siyasa sun zafafa kiraye-kiraye ga tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya yi wa jam’iyyar takara a Zaɓen 2027. A yayin taron na yau ne kuma PDP ta tabbatar da Umar Damagum a matsayin shugabanta na ƙasa a hukumance. Damagum wanda ya shafe fiye da...
‘Yan Sama Jannatin Shenzhou-20 Za Su Gudanar Da Zagaye Na 3 Na Aiki A Wajen Cibiyar Binciken Sararin Samaniya Ta Sin
Hukumar kula da kumbuna ta kasar Sin ta ce nan ba da jimawa ba, ‘yan sama jannatin kumbon Shenzhou-20 dake cibiyar binciken sararin samaniya ta kasar, za su gudanar da zagaye na 3 na ayyuka a wajen cibiyar. ‘Yan sama jannatin 3 da suka hada da Chen Dong da Chen Zhongrui da Wang Jie, sun gudanar da irin wannan aiki har sau biyu, a watannin Mayu da Yuni. Baya ga haka, sun kammala ayyukan nazarin muhalli da kula da tantance da kayayyakin aiki a cikin cibiyar da jigilar kayayyaki. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp...
Shugaban ya kuma yabawa cibiyoyin koyon ilimi tare da bayyana cewa wadannan nasarorin da aka samu shaida ne na ingancin ilimin Nijeriya wanda ke kekkenshe yara masu basira a duniya. Tinubu ya yi imanin cewa, ilimi muhimmin abu ne ga ci gaban kasa; don haka, babbar hobbasar da gwamnatinsa ta yi a fannin, shi ne kawar da matsalolin kudi ga ‘yan Nijeriya marasa galihu da ke neman manyan makarantu ta hanyar ba su ba shi a ashirin Asusun ba da lamuni na ilimi na Nijeriya (NELFUND). Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki...
Ta sake kafa tarihi bayan da jaridar National Concord mallakar MKO Abiola ta naɗa ta a matsayin editan jaridar ta farko, inda A shekarar 1986, aka ɗaga darajarta zuwa matsayin Manajan Darakta kuma Babban Edita mace ta farko da ta riƙe wannan matsayi a tarihin jaridun Nijeriya. Ta auri MKO Abiola a shekarar 1981, kuma ta tsaya tsayin daka tare da shi wajen gwagwarmayar siyasarsa da rikicin da ya biyo bayan zaɓen 12 ga watan Yuni, inda ta bayar da gagarumar gudunmawa a fagen jarida, tare da shafe kusan shekaru 30 tana jan ragamar kafafen yaɗa labarai a Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye...
Rashin Nasarar DPP A Zagayen Farko Na Kuri’ar Kiranye Ya Nuna Rashin Amincewar Al’ummar Taiwan Da Salon Mulkin Jami’yyar
Kakakin ofishi mai lura da harkokin yankin Taiwan a majalisar gudanarwar kasar Sin Chen Binhua, ya ce kalaman da aka jiyo jagoran yankin Taiwan na kasar Sin Lai Ching-te na yi dangane da sakamakon zagayen farko na kuri’ar kiranye da al’ummar Taiwan suka kada, ya nuna rashin gamsuwarsu da salon mulkin jam’iyyar DPP mai mulkin yankin. Chen Binhua, wanda ya bayyana hakan ga manema labarai a Larabar nan, ya ce kalaman Lai na cike da yaudarar kai, sun kuma fayyace manufar da ya dage a kanta ta “neman ’yancin kan Taiwan”. Kazalika, mummunan kayen da DPP ta sha a kuri’un da aka kada ranar Asabar din karshen makon jiya, ya fayyace ajandarta ta yin fito-na-fito da Sin, tare da fafutukar...
Babban Jami’in Hamas A Gaza; Makiya ‘Yan Sahayoniyya Suna Rufe Gazawar Sojojinsu Da Kisan Kare Dangi
Babban jami’in kungiyar Hamas a Zirin Gaza ya bayyana cewa: Makiya yahudawan sahayoniya suna rufe gazawar sojojinsu da kisan kare dangi Khalil al-Hayya babban jami’in kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas a zirin Gaza ya jaddada cewa: Makiya yahudawan sahayoniyya suna rufe gazawar sojojinsu ta hanyar kisan kare dangi da suke aiwatarwa kan fararen hula. A cikin wani jawabi kai tsaye ta gidan talabijin, Al-Hayya ya bayyana cewa: “Ya ku ‘ya’yan Dakarun Qassam, da na Quds Brigade, da kuma sauran kungiyoyin gwagwarmaya, abin da kuke yi ya kawo cikas ga farmakin da motoci masu sulke na makiya suke yi. Khalil ya jaddada cewa: Babban hafsan hafsoshin sojin makiya yana rufe gazawar sojojinsa da kisan kare dangi da suke aiwatarwa kan fararen...
Wani sabon salon gwamnatin mamayar Isra’ila na neman kashe Falasdinawa ‘yan gudun hijira da tsananta yunwa kansu Sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila sun rufe tekun ga masunta da ‘yan gudun hijira a zirin Gaza, matakin da ke kara dagula al’ummar Gaza da aka killace. Gabashin tekun kudancin Gaza shi ne mashigar da mazauna yankin da kuma ‘yan gudun hijira a dukkanin yankunan zirin Gaza, musamman a kudancin zirin Gaza, biyo bayan umarnin ficewa da sojojin mamayarr Isra’ila suka bayar ga mazauna yankin Al-Mawasi da ke yammacin yankin. Tekun ya zama mafaka daya tilo ga ‘yan gudun hijira da mazauna yankin saboda hare-haren da sojojin mamayar Isra’ila ke kaiwa kan Falastinawa. Sai dai rundunar sojin mamayar Isra’ila ta sanya sabbin takunkumi...
Kamfanin CRCC na Sin ya cimma nasarar kammala shimfida layin dogo mai tsawon kilomita 135 a jiya Litinin. Aikin ya kasance mataki na farko na shirin shimfida layin dogo na farko a hamadar Afrika, na jiragen kasa masu dakon kayayyaki mafiya nauyi, wanda zai hada jihar Bechar da yanki mai samar da karfe na Gala Jebilet a Jihar Tindouf dake yammacin kasar Aljeriya. Gwamnan jihar Tindouf Mustapha Dahou, da babban darektan CRCC Dai Hegen sun halarci bikin kammala aiki. A gun bikin, Dahou ya ce, CRCC da jiharsa, sun yi hadin gwiwar daga matsayin layin dogon zuwa masana’antu, matakin da ya ingiza bunkasar tattalin arzikin wuri zuwa mataki na gaba. Ya kuma yi fatan bangarorin biyu za su kara hada...
Ibrahim ya bayyana cewa, sun rarraba mukamai na rikon jam’iyyar a tsakaninsu, kafin babban taro na kasa a nan gaba. Gwamnan Jihar Kaduna, Nasiru El-Rufai ya tabbatar cewa; hadakar ta ADC, ta zabi Aregbesola a matsayin sakatarenta na kasa na riko, har ma ya wallafa a jawabin karbar mukamin da ya yi a shafukan sada zumunta. Matakin ‘yan adawar na shiga ADC, na zuwa ne bayan kasa cimma bukatarsu ta yi wa sabuwar kungiyar mai suna ‘All Democratic Alliance’ (ADA), rajista a matsayin jam’iyyar siyasa, sakamakon jan kafa da suka rika samu daga babbar hukmar zabe ta kasa (INEC). Haka zalika, Atiku Abubakar da wasu manyan jam’iyar PDP, sun nemi ‘yan jam’iyyar da su hada hannu da su wajen shiga...
Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran ya bayyana cikakken shirin Iran na tunkarar duk wani mataki na wuce gona da iri a daidai lokacin da ake ci gaba da fuskantar barazanar daukar matakin soji kan kasar. Manjo Janar Hossein Salami ya bayyana hakan ne yau Alhamis, yayin da rahotanni ke nuni da cewa, Amurka ta sanya ofisoshin jakadancinta da sansanonin sojinta da ke yammacin Asiya cikin shirin ko-ta-kwana saboda fargabar yiwuwar kai wa Iran hari. “A wasu lokuta makiya suna yi mana barazana da daukar matakin soji, mun sha bayyanawa, kuma muna maimaitawa a yau, cewa mun shirya tsaf don fuskantar duk wani yanayi,” in ji shi. “Muna da kwarewa, mun karfafa karfinmu tare da samar...
Jam’iyyar APC A Najeriya Ta Tabbatar Da Tinubu A Matsayin Dan Takarar Shugaban Kasa A Jam’iyyar A Shekara Ta 2027
Jam’iyyar ‘All Progressives Congress” (APC) mai Mulki a tarayyar Najeriya ta tabbatar da shugaban Bola Ahmed Tinubu a matsayin dan takarar Jam’iyyar a zaben shugaban kas ana shekara ta 2027 mai zuwa. Shafin yada labarai na Afrika ya bayyana cewa a jiya Alhamis ce a taron Jam’iyyar wanda aka gudanar a Abuja, kuma wanda ya zo dai-dai da cika shekaru biyu da zagayensa na farko na shugabancin kasar Jam’iyyar ta nada shi Shugaba Bola Ahmed Tinubu dan shekara 73 a duniya a matsayin dan takararta a zaben na shekara ta 2027, don ya sami damar kamala shirinsa nag yare-gywaren tattalin arzikin kasar da y afara. Shugaban Tinubu dai ya kara farashin man fetur a ranar da ya hau kan kujerar...
Nahiyar Afirkan a karkashin tarayyar Afirka ta kafa cibiyar dake kula da sararin samaniya domin tattara bayanai, wacce ke da matsuguni a birnin “alkahira’ na Masar. Sabuwar cibiyar dai ta fara aiki ne a watan da ya gabata,kuma za ta rika musayar bayanan da take tattarawa da cibiyoyin kasashen da suke a fadin nahiyar. Haka nan kuma cibiyar za ta kyautata ayyukanta ta hanyar harba taurarin dan’adam a sararin samaniya da kafa cibiyoyin bibiyar yanayi domin yin musayarsu da kasashen nahiyar da kuma wajenta.
Masifar Gobara Tana Kara Bunkasa A Haramtacciyar Kasar Isra’ila Tare Da Fara Raba Yahudawa Da Muhallinsu
Ana sa alamar tambayar cewa: Shin gobarar da ta tashi a birnin Kudus… shin sako ne na ranar tunawa da kafuwar gwamnatin ‘yan sahayoniyya? Gobarar da ta tashi a tsaunin Kudus da aka mamaye ta bazu zuwa manyan yankuna a cikin haramtacciyar kasar Isra’ila, inda ta kewaye wani sansanin soji tare da cinye filayen masu girma da tsayi. Hakan ya sa hukumomin gwamnatin mamayar Isra’ila suka kafa dokar ta baci tare da neman taimakon kasashen duniya. Yayin da Ministan tsaron cikin gidan Isra’ila Itamar Ben-Gvir yake neman dora wa Falasdinawa, alhakin tashin gobarar. Gobarar ta kunno kai ne a daidai lokacin da yahudawan sahayoniyya suka fara gudanar da bukukuwan cika shekaru 77 da kafuwar gwamnatinsu ta mamaya a kasar Falasdinawa,...
Shugaba Xi Ya Jaddada Aniyar Kasarsa Ta Goyon Bayan Kudurorin Kyautata Yanayi Da Ci Gaba Marar Gurbata Muhalli
Ya ce, “Muddin muna da kwarin gwiwa, da karfin goyon bayan juna da hadin kai, za mu kai ga kawar da manufofi masu illa, da wanzar da daidaito da ci gaba a manufofin jagoranci a fannin kare yanayi da samar da ci gaba. ” (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A shekarar 2024, an kammala jigilar fasinjojin da yawansu ya kai biliyan 1.46 a filayen jiragen sama na kasar Sin yayin da yawan tashi da saukar jiragen sama ya wuce miliyan 12.4, adadin sun karu da kashi 15.9 bisa dari da kuma kashi 5.9 bisa dari, idan aka kwatanta da makamancin lokacin bara. Hakan ya nuna cewa, duka alkaluma masu alaka da harkokin sufuri sun kafa tarihi. Kazalika, a ranar 21 ga wata, kungiyar filayen jiragen sama masu daukar fasinja ta kasar Sin, da kwalejin nazarin kimiyya da fasahar jiragen sama masu daukar fasinja ta kasar Sin, da sauransu sun fitar da “Rahoton kimanta ingancin hidimar filin jirgin sama na shekarar 2024”, inda rahoton ya ce, akwai daidaito...
Wannan ya hada da darajar kayayyakin da ake shigowa da su daga waje da kuma fitar da su, wanda ke nuni da irin dimbin alakar kasuwanci da ke tsakanin kasashen biyu. Kayayyakin da Nijeriya ke fitarwa a cikin gida da na waje da jirgin ruwa ya kai dala miliyan 473.6 a watan Fabrairun 2025, kadan ya ragu daga dala miliyan 501 a watan Fabrairun 2024, wanda ke nuna raguwar kashi 5.5 cikin dari. A shekarar zuwa yau, fitar da kayayyaki na FAS ya ragu daga dala miliyan 792.8 a shekarar 2024 zuwa dala miliyan 687.4 a shekarar 2025, wanda ya nuna raguwar kashi 13.3 cikin dari. Amurka ta samu gibin ciniki a kan Nijeriya ne kawai a watan Janairun 2025,...
Sojojin Ruwa Na Kasashen Rasha Da China Sun Shigo Kasar Iran Don Fara Atisayen Sojojin Ruwa Mai Suna “Damarar Tsaro 2025”
Manya-manyan Jiragen ruwan yaki na kasashen Rasha da China sun isa tashar Jeragen ruwa ta Chabahar dake kudu maso gabacin kasar Iran a bakin tekun india don fara atisayen soje a tsakanin kasashen uku, wanda aka sanyawa suna ‘damarar tsaro na shekara ta 2025. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa wannan gagarumin atisayen sojojin ruwa tsakanin manya-manyan kasashen guda uku zai sami halattan wasu kasashe da dama a matsayin masu kallo. Labarin ya kara da cewa manya-manyan jami’an sojojin ruwa na sojojin Iran da kuma na dakarun IRGC ne suka tarbi jiragen ruwan yaki na wadannan kasashe. Sannan ana saran wakilai daga kasashen Azerbaijan, Iraki, Kazakhstan, Oman, Pakistan, Qatar, Afirka ta Kudu, Sri Lanka da Haddiyar...
“A karkashin Shugabancin Dantsoho, ya taimaka wajen ganin ana sauke sundukan kayan da aka yo jigilarsu a cikin sauki, musamman a Tashar Lekki wanda hakan ya taimaka, wajen rage cunkso a Tashar.” A cewar Mahukuntan Mullar. Mahukuntan Mullar sun kara da cewa, sun zabo Dantso ne, ganin cewa, shi ne, na farko da aka zaba a mukamin Shugaba na Kungiyar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Gabas da yankin Afirka ta Tsakiya PMAWCA, inda zabarsa, ta kara daga kima da darajar Nijeriya, a fannin harkokin tafiyar da Tashohin Jiragen Ruwa, a yankin. A yayin da yake karbar babbar lambar yabon Mullar Dakta Dantsoho ya bayar da tabbacin cewa, zai kara zage damtse wajen shugabantar Hukumar, daidai da tsare-tsaren Miniatan bunkasa...
Babban layin wutar lantarkin Najeriya, ya faɗi a karon farko a shekarar 2025, lamarin da ya haddasa ɗaukewar wuta a wasu sassa. Wannan matsala ta haifar da katsewar wuta a wasu sassan ƙasar, wanda ya jefa masu amfani da lantarki cikin damuwa. Na yi nadamar yi wa Tinubu kamfe a 2023 — Ɗan Bilki Kwamanda Yadda na ƙi karɓar cin hancin N5bn a gwamnatin Tinubu – Tsohon Hadimi Cikin wata sanarwa da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Abuja (AEDC), ya fitar a shafinsa na X, ya bayyana cewa matsalar ta faru ne da misalin ƙarfe 11:34 na safiyar ranar Laraba. Sai dai AEDC, ya ce ana aiki tare da masu ruwa da tsaki domin tabbatar da dawo da wutar da...
Bikin zagayowar cikan shekaru 46 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci a Iran ya jaddada kare tushen tsarin kasar da gwagwarmaya Dukkanin sassan kasar Iran sun gudanar da zanga-zanga da dukkanin bangarori na al’umma suka halartar domin tunawa da zagayowar cikan shekaru 46 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar. Tun daga wayewar garin jiya Litinin ne, al’umma sun fito kan manyan hanyoyi kasa a jihohi kasar tamkar kwararan kogi don gudanar da murnar cikan shekaru 46 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar, tare da tabbatar da aniyarsu ta yi riko da manufofin juyin juya halin na Musulunci da kuma sabunta mubaya’arsu ga tsarin Jamhuriyar Musulunci.
Iran tana gudanar da bukukuwan zagayowar nasarar juyin juya halin Musulunci yau tsawon shekaru 46 tare da samun nasarori da kalubale A yau Litinin ne, al’ummar Iran suke gudanar da bukukuwan tunawa da cika shekaru 46 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar, wanda marigayi Imam Ruhollah Khomeini (Yardan Allah ta tabbata a gare shi) ya jagoranta, a cikin wadannan shekaru da dama, juyin juya halin Musulunci ya fuskanci makirce-makirce masu yawa da cikas, kuma ya samu gagarumar nasara, mafi muhimmanci daga cikinsu shi ne hambarar da gwamnatin sarki Shah da kasashen yammacin duniya suke goya masa baya, kamar yadda Iran bayan samun nasarar juyin juya halin Musulunci ta yi nasarar kafa gwamnati da samar da ginshikanta da...
Daga cikin yara ‘yan makaranta miliyan 242 da matsanancin yanayi ya raba da muhallansu a kasashe 85 a shekarar 2024, dalibai miliyan 2 da dubu 200 ne a Najeriya suka rabu da muhallansu, lamarin da ya kawo cikas ga harkokin ilimi a shekarar. Rahoton wanda Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya fitar a daidai lokacin da duniya ke bikin ranar ilimi ta duniya ta shekarar 2025, ya nuna cewa a Najeriya baki daya dalibai miliyan 2,200,200 ne suka daina makaranta sakamakon ambaliyar ruwa. Da take gabatar da jawabi kan tasirin da sauyin yanayi ke da shi ga ilimin yara, shugaban ofishin UNICEF na Kano, Mista Rahama Farah ya bayyana cewa, ambaliyar ruwa da ta...