ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Adadin Motocin Da Sin Ke Fitarwa Waje Ya Karu Da Kashi 15.7 Cikin Watanni 10 Na Farkon Bana November 17, 2025 Daga Birnin Sin An Bude Taron Tattaunawa Kan Wayewar Kai Tsakanin Sin Da Kasashen Larabawa Karo Na 11 A Beijing November 17, 2025 Daga Birnin Sin Firaministan Sin Ya Isa Rasha Domin Halartar Taron SCO November 17, 2025

.

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

An Yi Taron Karatun Sinanci Na Duniya Na 2025 A Beijing

An yi taron karatu na Sinanci na duniya na 2025 a Beijing daga ranar 14 zuwa 16 ga wannan wata. Taron ya samu mahalarta kusan mutane 2000 da suka fito daga fiye da kasashe da yankuna 160, wadanda suka hada da wakilan hukumomin ilimi, shugabannin makarantun jami’a na kasar Sin da na kasashen waje, da jakadun kasashen waje da ke zaune a Sin.

A wani bangare na taron da aka kira da “Musanyar ra’ayi tsakanin al’adu na Sin da na duniya da koyar da kwararru masu binciken Sin”, cibiyar hadin kan harsuna da musanyar ra’ayoyi tsakanin Sin da duniya na ma’aikatar ilimi ta Sin ta sanar da kafuwar cibiyar kwararrun matasa masu binciken al’adun Sinawa ta kasa da kasa. Kungiyar ta karbi jerin dalibai matasa a zagaye na farko na “Sabon shirin koyon al’adun Sinawa” daga kasashe da yawa, wadanda za su rika haduwa a-kai-a-kai don tattaunawa game da koyon Sinanci, da binciken al’adun Sin, da musanya ra’ayoyi tsakanin al’adu na Sin da na duniya. Wanna shiri shi ne sabon tsarin da aka yi don koyar da sabbin matasa masana al’adun Sinawa a ketare. Tun daga shekarar 2013 har zuwa yanzu, shirin ya koyar da dubun kwararru a wannan bangare.

Ban da wannan kuma, yayin taron, an gabatar da tsarin jarrabawar matakin Sinanci na HSK 3.0, wanda ya habaka matakan koyon Sinanci daga mataki na 6 zuwa na 9. A lokaci guda kuma, an fitar da dandamalin koyon Sinanci ta hanyar fasahohin zamani masu yawa.(Amina Xu)

ADVERTISEMENT ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Ana Mai Da Hankali Kan Dabarun Kasar Sin A Fannin Tinkarar Sauyin Yanayin Duniya A Taron COP30 November 16, 2025 Daga Birnin Sin Kuri’un Jin Ra’ayi Na CGTN Sun Shaida Adawar Sassan Kasa da Kasa Da Burin Masu Tsattsauran Ra’ayi Na Japan Na Ruguza Odar Kasa Da Kasa Ta Bayan Yakin Duniya Na 2 Dangane Da Batun Taiwan November 15, 2025 Daga Birnin Sin Sin Ta Bayyana Damuwa Dangane Da Matakin Amurka Na Ingiza Daftarin Tsawaita Aikin Tawagar UNISFA  November 15, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Adadin Motocin Da Sin Ke Fitarwa Waje Ya Karu Da Kashi 15.7 Cikin Watanni 10 Na Farkon Bana
  • An Bude Taron Tattaunawa Kan Wayewar Kai Tsakanin Sin Da Kasashen Larabawa Karo Na 11 A Beijing
  • Firaministan Sin Ya Isa Rasha Domin Halartar Taron SCO
  • NAJERIYA A YAU: Matsayar Doka Kan Taron Da Jam’iyyar PDP Ta Gudanar
  • Sin Ta Gargadi Philippines A Kan Ci Gaba Da Tayar Da Zaune Tsaye A Tekun Kudancinta
  • An Yi Taron Karatun Sinanci Na Duniya Na 2025 A Beijing
  • Yadda Za A Magance Yawan Faɗace-faɗace A Wasannin Gasar Firimiyar Nijeriya
  • MDD: Mutane 100,000 Ne Su Ka Fice Daga Birnin Al-Fasher Na Kasar Sudan
  • Wakilai Daga Jihohi 19 Sun Isa Ibadan Don Taron PDP Na Ƙasa