Aminiya:
2025-11-17@22:59:02 GMT

CAF ta fitar da ’yan wasa uku da suka rage a takarar gwarzon Afirka na bana

Published: 18th, November 2025 GMT

Hukumar ƙwallon ƙafar Afirka CAF, ta bayyana cewa bayan tankade da rairaya da ta yi, a yanzu ’yan wasa uku kacal ne suka rage a takarar gwarzon nahiyyar na bana.

A wata sanarwar da hukumar ta fitar a ranar Lahadi, ta bayyana Achraf Hakimi da Mohamed Salah da Victor Osimhen, a matsayin sauran ukun da suka rage a takarar gwarzon dan ƙwallon ƙafar Afirka na bana.

Gobara ta laƙume rayukan yara biyu ’yan gida ɗaya a Ribas Mayaƙan ISWAP sun kashe kwamandan soji a Borno

Hakimi, kyaftin din Morocco, ya lashe kofuna daga ciki har da Champions League a PSG — na farko a tarihin ƙungiyar — da Ligue 1, da European Super Cup, da kuma kai wa zagayen ƙarshe a FIFA Club World Cup da Chelsea ta lashe a Amurka.

Shi kuwa Mohammed Salah ya taka rawar gani a Liverpool a kakar da ta wuce da lashe Premier League, kuma shi ne kan gaba a zazzaga kwallaye mai 29 da bayar da 18 aka zura a raga, hakan ya sa ya karbi kyautar takalmin zinare, wato Golden Boot.

Mohammed Salah dan ƙasar Masar mai shekara 33 na fatan karbar kyautar gwarzon Afirka karo na uku bayan 2017 da kuma 2018.

Shi kuwa dan ƙwallon tawagar Super Eagles ta Najeriya, Victor Osimhen ya jagoranci Galatasaray ta dauki babban kofin tamaula na Turkiya da cin ƙwallo 26.

Osimhen ya taba zama gwarzon Afirka 2023 a lokacin da shi kuma Hakimi ya yi na biyu

To sai dai mai riƙe da kyautar a yanzu, wato Ademola Lookman na Nijeriya, bai kai bante ba a kakar nan sakamakon gaza taka rawar gani yadda ake buƙata.

Za a gudanar da bikin karrama gwarzon dan ƙwallon ƙafa na Afirka na bana ranar Laraba a birnin Rabat na Morocco.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Achraf Hakimi

এছাড়াও পড়ুন:

Afirka ta Kudu na Binciken shigar wasu ‘yan gudun hijirar Falasdinu 153 cikin kasar

Shugaba Cyril Ramaphosa na Afirka ta Kudu ya ce kasarsa na binciken wani jirgin sama da ya kawo ‘yan gudun hijirar Falasdinawa 153 kasar ba tare da takardun shiga ba.

“Wadannan mutane ne daga Gaza wadanda, ta wata hanya, suka tsinci kansu cikin jirgin sama da ya tashi daga Nairobi (babban birnin Kenya) kafin su iso nan,” in ji Ramaphosa ga manema labarai, yana mai cewa hukumomin leken asiri da Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida na kasar suna binciken lamarin.

A ranar Alhamis, Afirka ta Kudu ta ba Falasdinawan su 153 mafaka ta kwanaki 90, duk da cewa an hana su shiga saboda sun gaza amsa tambayoyin da aka musu kuma fasfo dinsu ba su da tambarin tashi, ko tikitan komawa in ji Ma’aikatar Harkokin Cikin Gidan Afrika ta kudu a cikin wata sanarwa.

A halin yanzu, ofishin jakadancin Falasdinu a Afirka ta Kudu ya bayyana a shafukan sada zumunta cewa ‘yan Falasdinu 153 sun iso ba tare da wata sanarwa ko hadin gwiwa ba.

An bayyana cewa wata kungiyar mayaudara ce ta shirya jirgin.

Ofishin jakadancin ya ce kungiyar ta yi amfani da mummunan halin jin kai na al’ummar Gaza, ta yaudari iyalai, ta karbi kudi gare su, ta samar musu tafiyar ta hanyar da ba ta dace ba, saidai kungiyar agaji ta Gift of the Givers, ta shaida wa tashar talabijin ta Afirka ta Kudu SABC cewa Isra’ila ce ke da alhakin shigar ‘yan gudun hijirar Falasdinawa cikin kasar ba bisa ka’ida ba.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Najeriya ba za ta buga kofin duniya ba karo na biyu a jere November 17, 2025 DRC: An Kulla Yarjejeniyar Zaman Lafiya A Tsakanin Gwamnati Da Kungiyar M23 November 16, 2025 An Yi Kira A Bai Wa ‘Yan Hijira Saboda Sauyin Muhalli Kariya November 16, 2025  An Amince Da  Sauye-sauye A Tsarin Mulkin Kasar Benin November 16, 2025 Isra’ila Ta Kai Wa Sojojin MDD Hari A Kasar Lebanon November 16, 2025 Makiya Sun Kulla Makirci kan Kasar Labanon Irin Wanda Suka Kulla Kan Siriya November 16, 2025  Kasar Afghanistan Na Kokarin Karkata Akalar Kasuwancinta Zuwa Iran November 16, 2025 Kanada Ta Tsare Tsohon Wakilin Majalisar Dinkin Duniya Mai Bincike Kan Laifukan Yakin Israila.   November 16, 2025  Zarfi: HKI Ce Kawai Take Ayyana Nukiliya Ba Bisa Kaida Ba A Yammacin Asiya. November 16, 2025 Shugaban kasar venuzuwela Yayi Tir Da Atisayan Soji Da Trinidad and Tobago Ke yi. November 16, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Adadin Motocin Da Sin Ke Fitarwa Waje Ya Karu Da Kashi 15.7 Cikin Watanni 10 Na Farkon Bana
  • ’Yan bindiga sun kashe mutum 3 sun sace 64 a Zamfara
  • Afirka ta Kudu na Binciken shigar wasu ‘yan gudun hijirar Falasdinu 153 cikin kasar
  • Gwamnatin Gombe ta bai wa alƙalai da Khadi-Khadi kyautar sabbin motoci 16
  • Yadda Za A Magance Yawan Faɗace-faɗace A Wasannin Gasar Firimiyar Nijeriya
  • NNPP Tana Da Ƙwarin Gwiwar Riƙe Kano Da Lashe Jihohin Arewa A Zaɓen 2027 – Ajuji
  • Hukumar Kwallon Kafa Ta Kasar Turkiyya Ta Dakatar Da ‘Yan Wasa 1024 Saboda Laifin Caca
  • An Gabatar Da Sabuwar Hanyar Raya Hadin Gwiwar Tattalin Arziki Da Cinikayya A Tsakanin Sin Da Afirka
  • Sojoji sun kashe ’yan ta’adda, sun kama mutum 94