Firaministan Sin Ya Isa Rasha Domin Halartar Taron SCO
Published: 17th, November 2025 GMT
Firaministan kasar Sin Li Qiang ya isa birnin Moscow na kasar Rasha a yau Litinin domin halartar taro karo na 24 na majalisar shugabannin kasashe mambobin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai (SCO).
Bisa gayyatar da firaministan kasar Rasha Mikhail Mishustin ya yi masa, Li zai halarci taron na SCO a ranakun 17 da 18 ga watan Nuwamba.
এছাড়াও পড়ুন:
An Sanya Hannu Kan Yarjejeniyoyin Cinikayya Na Biliyoyin Kudi Yayin Baje Kolin CHTF Na Kasar Sin
An sanya hannu kan yarjejeniyoyin cinikayya na biliyoyin kudi, a yayin baje kolin hajojin fasahohin zamani na kasar Sin ko CHTF, wanda aka kammala a jiya Lahadi a birnin Shenzhen dake kudancin kasar Sin. Wannan ne karo na 27 da aka gudanar da baje kolin na CHTF, inda aka kai ga daddale huldodin cinikayya da ayyukan zuba jari 1,023, wadanda darajarsu ta haura kudin Sin yuan biliyan 170, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 24.
Baje kolin na wannan karo ya gudana ne bisa taken “Fasahohi masu jagorantar ci gaba da dunkulewar masana’antu”. Kazalika, taron na yini uku ya hallara kamfanoni da hukumomi sama da 5,000 daga kasashe da yankuna sama da 100, ya kuma samu halartar baki sama da 450,000.
Yayin baje kolin na CHTF, an nuna sabbin kayayyaki sama da 5,000, da fasahohi da ayyukan kirkire-kirkire da dama. Har ila yau, an samar da manyan yankunan nune-nune 22, ciki har da na muhimman na’urorin gudanar da ayyuka, da na fasahar AI da mutum-mutumin inji, da manyan kayan ayyukan na kasa, da kayan laturoni, da na’urorin sufurin sama dake zirga-zirga kusa da doron kasa, kayayyakin da suka shaida halartar manyan masu ruwa da tsaki a harkokin binciken kimiyya na duniya, da nasarorin da Sin ta cimma a fannonin kirkire-kirkire. (Saminu Alhassan)
ADVERTISEMENT ShareTweetSendShare MASU ALAKA