2025-11-16@12:46:57 GMT
إجمالي نتائج البحث: 11647
«kasar venuzuwela»:
Wani tsohon dan majalisar kasar labanon ya bayyana cewa kasarsa ba ta bukatar wata yarjejeniya da zaa kulla kan ci gaba da keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta da hki take yi , kana yayi gargadin cewa makircin da aka kulla kan kasar siriya aka kai ta kasa irinsa ne ake kullawa akan kasar labanon, Hussain haj Hassan yace babu wani amfani kara tattaunawa kan wata yarjejeniya da isra’ila tun da ta kasa tsayawa ta yi aiki da yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka cimma a watan nuwambar shekarar da ta gabata. Daga karshe ya nuna cewa gwamnatin dake rike da kasar siriya ta haiati tahrir al sham abokiyar Amurka ce don haka har yanzu isra’ila na ci gaba...
Gwamntin daliban ta kasar Afghnistan ta sanar da sauya akalar harkokin kasuwancinta ta hanyar iran da tsakiyar asiya, domin rage dogaro da kasar Pakistan a lokacin da zaman tankiya ya kara Kamari tsakanin makwabtan guda biyu da ya kai ga rufe iyakokinsu. A wani yunkuri na kewaye kasar Pakistan da kuma kaucewa matsalolin da ake samu a iyakarta da Pakistan, kasar Afghanistan ta kara yawan lokacin aikewa da kayayyakinta zuwa tashar jigin ruwa ta chabahar ta kasar iran. Kakakin ma’aikatar kasuwanci ta kasar Afghanistan Abdus salam Jawad Akhundaze Ya ce a tsawon watanni 6 kasuwancinsu da iran ya kai dala biliyan 1.6. fiye da dala biliyan 1 na kayayyakin da take fitarwa ta hanyar Pakistan . Share 0 0 votes...
Ya ci gaba da cewa, “an kama masu laifuka da dama ta hanyar bayanai da muke bai wa jami’an tsaro wanda hakan ya taimaka sosai wajen magance aikata laifuka a POS”, domin a cewarsa “sun sanya tsauraran matakai yadda ko da an tura kudi kafin a zo karɓa mambobinmu suna ganewa idan an tura kudin ta hanyar da ya dace, idan ba su gamsu ba sai a sanar da jami’an tsaro a zo a kama mutum, an kama wasu a Abuja, an kama wasu a Maiduguri da wasu sassa na kasar nan”. Ya bayyana kungiyar a matsayin mai farin jini, inda ya ce dukkan jami’an Nijeriya sun santa kuma sun yi marhaban da ita ta hanyar kai musu ziyara...
Richard A falk Tsohon mai bincike kan laifukan yaki da HKI ta tafka kan alummar Gaza da majalisar dinkin duniya ta nada ya fuskanci matsalar a kasar kanada inda aka tsare shi tare da yi masa tambayoyi a wata tafiya da yayi don halartar taron dake da alaka da yankin Gaza. Falka dan shekara 92 da haihuwa, hukumar kula da hakkin dan adam ta majalisar dinkin duniya ta nada shi a shekara ta 2008 na tsawon shekaru 6 a matsayin dan rahoton musamman don gudanar da bincike kan laifukan yaki da HKI ta tafka a yankin falasdinu. Falk ya bayyana cewa dalilin yin tambayoyi na tsawon lokaci ga manyan masana da ba sa yin wata barazanar tsaro a filin saukar...
Rahotanni sun nuna cewa tsohon ministan harkokin wajen kasar iran mohammad Javad zarif yace isra’ila ce kawai gwamnatin dake ayyukan nukiliya ba bisa kaida ba a yammancin asiya, amma take sukar iran duk da cikakken hadinkai da take bayarwa ga dokokin hukumar nukiliya kuma wadda ke da tarihi mafi girma na binciken hukumar nukiliya ta duniya, Zarifi ya fadi haka ne a wajen taron international iranology da aka gudanar a birnin Tehran, kuma ya bayyana matsayin iran na dogon lokaci inda isra’ila take kokarin haifar da barazana a yankin domin kawar da kokarin deiplomasiya da ake yi na yarjejeniyar JCPOA. Har ila yau ya jaddada cewa batun danganta shirin iran da barazanar tsaro wani makirci ne da aka kulla domin...
Shugaban kasar venuzuwela Nicolas Maduro yayi suka game da atisayan soji da Trinidad an Tobago ke yi, kuma ya bayyana shi a matsayin abin da bai dace ba kuma yana barazana ga zaman lafiyar yankin Caribbean. Atisayan sojin yana kara tada hankali tsakanin kasar venuzuwela da daya daga cikin makwabciyarta ta kurkusa adaidai lokacin da ayyukan sojojin Amurka a yankin karebiya ya jefa yanki cikin zaman dar-dar. Kasar Trinidad and Tobago ta tsara fara gudanar da atisayin soji na hadin guiwa a cikin ruwan dake kusa da kasar venuzuwela daga ranar 17 zuwa 20 ga watan nuwamba, atisayan yazo daidai da ayyukan tsaro da Amurka ke jagoranta a yankin karebiya wandaAamurka tace ya shafi yaki da masu safarar miyagun kwayoyi...
Amfani da jami’an tsaro: Abu na farko dai dole ne kungiyoyi su yi aiki tare da yansanda, NSCDC, da jami’an tsaro na sirri wajen tsara tsare-tsaren tsaro a ranar da za su buga wasa, domin kuwa Bahaushe na cewa, “tun za a, ake shiri ba sai an dawo ba”, hakazalika yana da mahimmanci a tura isassun masu aikin kwantar da tarzoma (ba yansanda kawai ba) don sa ido kan magoya baya, lura da wuraren shiga/fita, da kuma taimakawa wajen rage turmutsitsi yayin wasa. Amfani da CCTV: Yawancin filayen wasa na gasar NPFL ba su da isasshen tsarin kyamarar CCTV, a cikin filayensu cewar bincike, samar da kyamarori masu sa ido na iya rage tashin hankali a cikin...
Ɓangaren Shari’a a Nijeriya, yana da alhakin bayyana dokoki, kare kundin tsarin mulki, da kuma tabbatar da adalci. An tsara tsarin shari’a a karkashin jagorancin Kotun Ƙoli inda Alƙalin Alƙalan Nijeriya (CJN) ke kula da ita, sannan Kotun Ɗaukaka Ƙara da Manyan Kotuna a matakin jiha da tarayya. Daga cikin manyan haƙƙoƙin da suka rataya akan ɓangaren Shari’a, akwai fassara kundin tsarin mulki da dokoki don amfani da su a shari’o’i. Sulhunta masu saɓani da kare haƙƙin ‘yan ƙasa da kuma tabbatar da cewa, sauran sassan gwamnati suna aiki a cikin iyakokin kundin tsarin mulki. Amma, mu tambayi kanmu, wai me ke faruwa a ɓangaren Shari’a, ake samun hukuncin Shari’a ɗaya masu karo da juna? An...
Dakarun kare juyin juya halin Musulinci na Iran, sun sanar da kwace wani jirgin ruwan dakon mai a gabar tekun kudancin Makran. A cikin wata sanarwa da ta fitar IRGC ta ce rundunarta ta gaggawa ta fara bin diddigin jirgin ruwan dake dauke da tutar Tsibirin Marshall a ranar Juma’a da safe, bayan umarnin kotu na kwace kayan da yake dauke da. A cewar sanarwar, jirgin yana dauke da tan 30,000 na sinadarai dangin mai dake kan hanyarsa ta zuwa Singapore. “Tankor ya saba wa ka’idoji na daukar kaya ba tare da izini ba,” in ji sanarwar IRGC. An gudanar da wannan aikin ne bisa doka da nufin kare muradun kasa da albarkatun Jamhuriyar Musulunci ta Iran. A ranar Juma’a,...
Iran ta yi gargadin cewa tsanantar ayyukan sojojin Amurka a yankin Caribbean da Latin Amurka na haifar da babbar barazana ga zaman lafiya da tsaro na duniya, kuma ta yi kira da a girmama hurumi da cikakken yancin Venezuela. A cikin wata sanarwa, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Iran, Esmail Baghai, ya ce barazanar Amurka na amfani da karfi kan zababiyar gwamnatin Venezuela ya saba wa dokokin kasa da kasa. Ya kuma bayyana cewa irin wadannan ayyuka tamkar keta ka’idojin Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya, musamman haramta amfani da karfi. A daya bangaren kuma, M. Baghai ya yi Allah wadai da hare-haren da Amurka ke kai wa jiragen kamun kifi na Venezuela a matsayin misalai na kisan gilla ba...
Gwamnatin Beirut ta ce za ta shigar da kara a kan Isra’ila gaban Majalisar Dinikin Duniya game da gida katangar siminti a kan iyakar Kudancin Lebanon. A cikin wata sanarwa data fitar fadar shugaban Lebanon ta sanar da cewa Beirut za ta shigar da kara a Majalisar Dinkin Duniya game da gina katangar. Shugaban Lebanon Joseph Aoun ya umarci Ministan Harkokin Wajen kasar Youssef Radji da ya umurci tawagar Lebanon ta Dindindin a Majalisar Dinkin Duniya da ta shigar da karar gaggawa a kwamitin Tsaro kan gwamnatin Isra’ila saboda gina katangar siminti a kan iyakar kudancin Lebanon, wadda ta wuce ‘’Layi Shuɗi’’ da aka zana bayan janyewar Isra’ila a shekarar 2000. Hukumomin Lebanon sun ce katangar simintin da sojojin Isra’ila...
Shugaban Kwamitin Tarayyar Afirka ya yi watsi da zargin da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi cewa ana wa Kiristoci kisan kare dangi a arewacin Najeriya. Da yake jawabi a wani taron Majalisar Dinkin Duniya a New York, ya ce irin wadannan kalamai kan iya gurbata matsalolin tsaro mai sarkakiya. Da yake magana tare da Sakataren Majalisar Dinkin Duniya António Guterres a ranar Alhamis, Mahmoud Ali Youssouf ya jaddada cewa Tarayyar Afirka ta riga ta fayyace matsayinta kuma ta yi kira da a yi taka tsantsan a cikin harshen da ake amfani da shi wajen bayyana rikice-rikicen da ke faruwa a nahiyar. “Babu kisan kare dangi a arewacin Najeriya,” in ji Youssouf. “Mun fitar da wata sanarwa a fili da...
A karon farko an yi wani wasan kwallon kafa na sada zumunci da ba a saba gani ba tsakanin ‘yan wasan Basque, da Falasdinu a Spain. Masu shirya wasan sun ce kimanin ‘yan kallo 50,000 ne suka samu tikitin shiga a filin wasa na San Mames, gidan Athletic Bilbao. Masoya da yawa sun daga tutocin Falasdinawa, da kuma tutocin yankin arewacin Basque Country. Duk da cewa an fitar da Falasdinu a zagaye na farko na gasar cin kofin duniya na 2026, wanda za a gudanar a watan Yuni da Yuli a Canada, Amurka, da Mexico, ana ganin murza leda da Falasdinun ta yi a Turai a matsayin mai matukar tasiri idan aka waiwaiyi yakin da Isra’ila ta kwashe tanayi a...
Kuri’un Jin Ra’ayi Na CGTN Sun Shaida Adawar Sassan Kasa da Kasa Da Burin Masu Tsattsauran Ra’ayi Na Japan Na Ruguza Odar Kasa Da Kasa Ta Bayan Yakin Duniya Na 2 Dangane Da Batun Taiwan
Kalaman tayar da husuma na firaministar Japan Sanae Takaichi, dangane da batun yankin Taiwan na kasar Sin, na ci gaba da shan suka da Allah wadai daga sassan kasa da kasa. Wani sakamakon kuri’un jin ra’ayin al’umma da kafar CGTN ta gabatar ya nuna yadda akasarin masu bayyana mahanga suka amince da cewa, matakin na Takaichi tsoma baki ne cikin harkokin cikin gidan kasar Sin, kuma akwai bukatar gaggauta sanya ido kan karuwar burikan wasu jagororin Japan masu tsattsauran ra’ayi, na ruguza odar kasa da kasa ta bayan yakin duniya na biyu. Kaso 91.1 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyin na ganin kamata ya yi Japan ta gyara tarihin ta’asar da ta aikata ta hanyar aiwatar da matakai na hakika,...
Kamar ‘yan wasa da masu horarwa, an hana jami’an wasa shiga ayyukan yin caca bisa ga ka’idojin TFF, da kuma na FIFA da hukumar gudanarwa ta Turai (Uefa), masu gabatar da kara na Turkiyya sun bayar da umarnin tsare mutane 21 ciki har da alkalai 17 da shugabannin kungiyoyin kwallon kafa biyu a wani bangare na babban bincike kan yin caca da kuma shirya yadda sakamakon wasa zai iya fitowa. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Wasanni Ina Son Kasancewa Cikin Koshin Lafiya Kafin Buga Gasar Kofin Duniya Na Shekarar 2026 – Messi November 15, 2025 Wasanni Shakirat Ta Tsallaka Mataki Na Ƙarshe Na Zama Gwarzuwar Ƴar Wasan Afrika November 15, 2025 Wasanni Kofin Duniya: Nijeriya Za Ta Fafata Da...
Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na Jihar Adamawa, ya yi watsi da hukuncin da Jam’iyyar PDP ta yanke na korar Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, daga jam’iyyar. Aminiya ta ruwaito yadda PDP ta kori Wike, Sanata Samuel Anyanwu da tsohon Gwamnan Ekiti, Ayodele Fayose, a yayin babban taron PDP da aka gudanar a Ibadan, Jihar Oyo. Cif Olabode George ne, ya gabatar da ƙudirin korarsu, kuma Shugaban PDP na Jihar Bauchi, Samaila Burga, ya mara masa baya. Sai dai bayan sanarwar, Gwamna Fintiri ya fitar da wata sanarwa, wadda ya nesanta kansa daga matakin da jam’iyyar ta ɗauka. Ya ce ba ya goyon bayan korar da aka yi wa Wike, domin hakan zai ƙara haifar da rikici a cikin jam’iyyar....
Mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Sun Lei, ya gabatar da tsokaci dangane da daftarin da Amurka ta gabatar, game da bukatar tsawaita ayyukan tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD a yankin Abyei na ko UNISFA a takaice. Sun, wanda ya yi tsokacin a jiya Juma’a, bayan jefa kuri’a a zaman kwamitin tsaron MDD kan daftarin, ya ce kasarsa ta damu game da yadda Amurka ta ingiza daftarin, wanda da ma ita ce ta gabatar da shi. Ya ce a matsayin kasar dake sahun gaba wajen tallafawa tawagar ta UNISFA, Sin ta shiga an dama da ita a shawarwarin da suka shafi daftarin, to sai dai kuma daftarin ya fitar da wasu ma’aunai masu alaka da yanayin...
Kyaftin din tawagar kwallon kafa ta kasar Argentina da Inter Miami, Lionel Messi, ya bayar da sharadin da zai sa ya buga wa Argentina wasa a gasar FIFA World Cup na shekarar 2026 da za a buga a kasashen Arewacin Amurka, za a buga gasar cin kofin Duniya na 2026 a manyan biranen kasar Kanada, Amurka da Medico a lokacin bazara, kuma ana sa ran gwarzon dan wasan na Argentina zai halarci gasar. Duk da haka, Messi ya ce zai shiga tawagar Argentina ne kawai idan yana cikin koshin lafiya, yana mai tabbatar da cewa ba ya son zama nauyi ga tawagar, Messi ya jagoranci Argentina zuwa ga nasara a gasar cin kofin duniya na shekarar 2022 inda suka doke...
A gobe Lahadi ne za a wallafa makalar babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping, game da ingiza gina sabbin ginshikan samar da ci gaban kasa masu inganci, daidai da yanayin da kasar ta Sin ke ciki. Za a wallafa makalar ta Xi Jinping, wanda shi ne shugaban kasar Sin, kuma shugaban hukumar zartarwar rundunar sojojin kasar ne a mujallar Qiushi fitowa ta 22 a bana, muhimmiyar mujallar kwamitin kolin JKS. (Saminu Alhassan) ADVERTISEMENT ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sin Ta Sha Alwashin Bunkasa Goyon Bayan Juna Tsakaninta Da Saliyo November 15, 2025 Daga Birnin Sin An Gabatar Da Sabuwar Hanyar Raya Hadin Gwiwar Tattalin Arziki Da Cinikayya A Tsakanin Sin Da Afirka November 15, 2025 ...
Tsohuwar Shugabar Mata ta Jam’iyyar PDP, Iyom Josephine Anenih, ta ce jam’iyyar za ta sake yin ƙarfi idan shugabanninta suka cire girman kai suka mayar da hankali kan yi wa jama’a hidima. Ta bayyana haka ne yayin babban taron PDP da aka gudanar a Ibadan a ranar Asabar. PDP ta kori Wike, Fayose, Anyanwu da wasu Sanusi II ne kaɗai halastaccen Sarki a Kano — Kwankwaso Ta ce har yanzu ’yan Najeriya da dama suna sa ran jam’iyyar za ta sake yin ƙarfi domin yi musu jagoranci. Anenih, ta yi gargaɗin cewa PDP na iya zama tarihi idan ba a gyara matsalolinta ba. “Idan ba mu fuskanci matsalolinmu ba, PDP za ta zama tarihi, labarin yadda sakaci da girman kai...
Jam’iyyar PDP ta kori Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, tsohon gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose da tsohon sakataren jam’iyyar na ƙasa, Samuel Anyanwu. PDP ta yanke wannan hukunci ne a babban taron jam’iyyar da ake gudanarwa a Ibadan, babban birnin Jihar Oyo. Gwamnati, UNICEF da ’yan jarida sun haɗa don yaƙar cututtukan da aka manta da su a Gombe Sanusi II ne kaɗai halastaccen Sarki a Kano — Kwankwaso Tsohon Mataimakin Shugaban Jam’iyyar na yankin Kudu, Cif Olabode George ne, ya gabatar da ƙudirin korarsu, sannan Samaila Burga, shugaban PDP na Jihar Bauchi, ya mara masa baya. A baya, tsagin jam’iyyar da ke goyon bayan Wike sun kai ƙara kotu don a hana gudanar da taron. Amma PDP ta...
An Gabatar Da Sabuwar Hanyar Raya Hadin Gwiwar Tattalin Arziki Da Cinikayya A Tsakanin Sin Da Afirka
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Yi Taka-tsantsan Da Batun Yankin Taiwan November 15, 2025 Daga Birnin Sin Jakadan Sin A Japan Ya Bayyana Matukar Adawa Da Kalaman Firaminista Takaichi Dangane Da Kasar Sin November 15, 2025 Daga Birnin Sin Bangaren Sauka Na Kumbon Shenzhou-21 Ya Iso Doron Duniya November 14, 2025
Dakin Gwaje-gwaje na “Sandia” dake karkashin ma’aikatar makamashin Amurka ya sanar da cewa; Jirgin sama samfurin “F-35” ya jefa bom din Nukiliya ba tare da yana dauke da abubuwan da suke fashewa a ciki ba. Majiyar ta kara da cewa an yi wannan gwajin ne dai a yankin Nivada na kasar ta Amurka a tsakanin 19 zuwa 21 ga watan Ogusta a karkashin sake duba lafiyar makamin Nukiliyar kasa da kuma kara bai wa matuka jiragen saman yaki horo. Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya jaddada niyyarsa ta ganin Amurka ta koma kan yin gwaje-gwajen makaman Nukiliya ba da jimawa ba. Sai dai shugaban na Amurka bai bayar da wani Karin bayani akan haka ba. Sai dai kuma wani labarin...
Jaridar “ma’ariv’ ta buga labarin dake cewa Fira minista Netanyahu yana rayuwa cikin zullumi da tsoro mai tsanani akan hukuncin da kotu za ta yanke masa. Jaridar ta ‘yan sahayoniya ta kuma ce yadda ake yin matsin lamba daga waje domin ganin an yafe wa Netanyahu,yana nuni ne da yadda Fira ministan yake cikin tsoro da razana akan hukuncin da kotun za ta yanke a kansa. Kwanaki kadan da su ka gabata ne dai shugaban kasar Amurka ya aike da wasika zuwa ga shugaban Haramtacciyar kasar Isra’ila Ishaq,,, yana bukatar ya yi wa Netanyahu afuwa.Ana tuhumar Netanyahu ne daaii da cin hanci da rashawa. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to...
Hukumar dake kula da ‘yan hijira ta MDD ta ce; Da akwai fiye da mutane 100,000 da su ka fice daga birnin Al-Fasher makwanni biyu kadai bayan da da kungiyar RSF ta shimfidaikonta a cikinsa. Mai magana da yawun hukumar ‘yan hijirar ta MDD, Yujing Biyun … ta kuma ce abu ne mai yiyuwa a halin yanzu adadin wadanda su k fice daga cikinbirnin sun fi haka,domin da akwai wadanda su ka makale akan hanya suna ci gaba da tafiya, wasu kuma suna cikin birnin suna son ficewa. Mutanen da suke ficewa suna son isa yankunan da suke da nisa sosai kamar kilo mita 50 daga gundumar Darfur. Wasu kuma suna tafiyar dubban kilo mita daga yankin baki daya. Sai...
Gwamnatin Tarayya, tare da haɗin gwiwar UNICEF da gwamnatin Jihar Gombe, sun shirya taron wayar da kai da ’yan jarida domin yaƙi da cututtukan da ba a cika kula da su ba. Ofishin UNICEF na Bauchi ya haɗa kai da ’yan jarida da JPHCDA da wakiliyar Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya, Hauwa Abubakar, domin tattaunawa kan yadda za a rage yaɗuwar cututtukan a jihar. Sanusi II ne kaɗai halastaccen Sarki a Kano — Kwankwaso Babu Janar ɗin da ISWAP ta kama a Borno — Sojoji A taron, ’yan jarida sun samu damar jin bayanai daga masana da kuma yadda aikace-aikacen yaƙi da cututtukan ke tasiri a cikin al’umma. Gwamnatin Jihar Gombe tana ware Naira miliyan 25 duk shekara domin yaƙi da...
Sunana Hassana Yahaya Iyayi (Maman Noor) daga Jihar Kano: Gaskiya ba abu ne mai kyau ba, ka nema ta hanyar halal din ma ya aka kare da kudin yanzu, bale kuma ta hanyar haram. Tsabar son abin duniya ne da rashin tsoron Allah, aji tsoron Allah a nemi halal, a nemi kudi ta tsabtatacciyar hanya. Sunana Abba Abubakar Yakubu, daga Jos, a Jihar Filato: Wannan maudu’i ne mai matukar muhimmanci, saboda talauci da son zuciya ya yi wa mutane yawa. Idanun mutane sun rufe, ba sa tunanin ya dace ko bai dace ba. Burinsu kawai shi ne a ina za su samu kudin da za su kashe wutar gabansu, ko kuma su cika burinsu na rayuwa. Lallai kuskure...
Jakadan kasar Sin a Japan Wu Jianghao, ya gana da mataimakin ministan harkokin wajen Japan Takehiro Funakoshi a jiya Juma’a, inda ya bayyana matukar adawar kasarsa, da korafi a hukumance, dangane da kalamai marasa dacewa da firaministar Japan Sanea Takaichi ta furta dangane da kasar Sin. Jakada Wu, ya ce munanan kalamai masu tayar da husuma na Takaichi, dangane da yankin Taiwan na Sin, wadanda aka jiyota tana yi kwanan baya, a majalissar dokokin kasarta sun sabawa hankali, sun tsallaka jan-layin kasar Sin, kana barazanar nuna karfi ne da neman takalar yaki. Kazalika, firaministar ta Japan ta ki amincewa da kuskurenta, ta ki janye kalaman, ko sassauta mummunan tasirinsu. Don haka matakin nata ya shaida matukar kaucewa gaskiya, da fankamar...
Sarki Sanusi II, ya yaba da ci gaban da jami’ar ke samu tare da farin ciki kan yawan mata da suka kammala karatu, yana fatan hakan zai ƙara yawan rawar da mata ke takawa a mulki da sauran ɓangarorin rayuwa. Tun da farko, Shugaban Jami’ar, Farfesa Ajith Kumar, ya bayyana cewa cikin ɗalibai 180 da suka kammala karatun 24 sun samu sakamako daraja ta ɗaya (First Class), tare da bayyana cewa wannan bikin yaye ɗaliban shi ne karo na farko da jami’ar ta raba digiri na biyu tun bayan amincewar Hukumar Kula da Jami’o’i ta Ƙasa (NUC), da ta samu. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai NAF Ta Ragargaza Mafakar Ƴan Ta’adda A Zamfara, Ta Halaka Da Dama November 15,...
Kifi mai nama ko naman rago, Ataruhu da tattasai, Barkono ja, Albasa, Daddawa, Gauta (baobab leabes),Yaji, gishiri da maggi, Manja ko man gyada. Yadda ake hada miyar: A wanke kifi ko naman da kyau, a nika attaruhu, tattasai, barkono ja da albasa a hade. A zuba kifi ko naman a tukunya tare da dan ruwa, gishiri da maggi. A bar shi ya tafasa har ya fara laushi. Sannan a zuba nikakken kayan miya a cikin tukunyar. A bar su su dahu har su gauraya da naman ko kifin. Sannan sai a zuba daddawa a cikin miya. A juya sosai sannan a bar shi ya tafasa na ‘yan mintuna. Sai a wanke gauta sosai kafin a zuba a cikin miya....
Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya sake jaddada cewar Muhammadu Sanusi II ne, halastaccen Sarki a hukumance Ya bayyana haka ne a ranar Asabar, a lokacin bikin yaye ɗalibai karo na huɗu a Jami’ar Skyline University of Nigeria (SUN) da ke Kano. Babu Janar ɗin da ISWAP ta kama a Borno — Sojoji Sojoji sun kashe ’yan ta’adda, sun kama mutum 94 “Muhammadu Sanusi II shi kaɗai ne Sarkin Kano a wajen mutane da gwamnatin jiha. Duk wani da aka naɗa daga wajen jihar ba shi da inganci a idon al’ummar Kano.” A cewarsa, duk wanda wasu suka naɗa a matsayin Sarki ba shi da ƙima a idon al’ummar Kano da gwamnatin jihar. Kwankwaso, wanda ya yi...
Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya sake jaddada cewar Muhammadu Sanusi II ne, halastaccen Sarki a hukumance Ya bayyana haka ne a ranar Asabar, a lokacin bikin yaye ɗalibai karo na huɗu a Jami’ar Skyline University of Nigeria (SUN) da ke Kano. Babu Janar ɗin da ISWAP ta kama a Borno — Sojoji Sojoji sun kashe ’yan ta’adda, sun kama mutum 94 “Muhammadu Sanusi II shi kaɗai ne Sarkin Kano a wajen mutane da gwamnatin jiha. Duk wani da aka naɗa daga wajen jihar ba shi da inganci a idon al’ummar Kano.” A cewarsa, duk wanda wasu suka naɗa a matsayin Sarki ba shi da ƙima a idon al’ummar Kano da gwamnatin jihar. Kwankwaso, wanda ya yi...
Rundunar Soji ta ƙaryata rahotannin da ke cewa an yi garkuwa da kwamandan Bitget ta 25 da ke Jihar Borno a wani harin kwanton ɓaunan mayaƙan ƙungiyar ISWAP. Ta buƙaci jama’a su yi watsi da wannan labarin ƙarya, tare da yin addu’ar samun nasarar sojojin Najeriya da ke bakin daga. Rundunar ta ce sojojin sun murƙushe wani harin kwanton ɓauna da ISWAP ta kai musu a yayin da suke sintiri domin kare al’ummomin da ke kewaye da Wajiroko a yankin Azir Multe a Ƙaramar Hukumar Damboa da ke Jihar Borno. Ta ce sojojin sun gamu da kwanton ɓauna ne daga ’yan ta’adda yayin da suke dawowa daga aikin sintiri a gefen Dajin Sambisa. Mayaƙan ISWAP sun sace Janar sun kashe...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Wasu Mahara Sun Kashe Mata 2, Tare Da da Ƙona Gidansu A Tudun Yola November 15, 2025 Manyan Labarai Shugaban APC Na Kano Ya Nemi Afuwa Daga Al’ummar Fagge Kan Kalamansa November 15, 2025 Da ɗumi-ɗuminsa Tsohon Gwamnan Anambra, Willie Obiano, Ya Rasu Yana Da Shekaru 70 November 14, 2025
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Wasu Mahara Sun Kashe Mata 2, Tare Da da Ƙona Gidansu A Tudun Yola November 15, 2025 Manyan Labarai Shugaban APC Na Kano Ya Nemi Afuwa Daga Al’ummar Fagge Kan Kalamansa November 15, 2025 Da ɗumi-ɗuminsa Tsohon Gwamnan Anambra, Willie Obiano, Ya Rasu Yana Da Shekaru 70 November 14, 2025
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Wasu Mahara Sun Kashe Mata 2, Tare Da da Ƙona Gidansu A Tudun Yola November 15, 2025 Manyan Labarai Shugaban APC Na Kano Ya Nemi Afuwa Daga Al’ummar Fagge Kan Kalamansa November 15, 2025 Da ɗumi-ɗuminsa Tsohon Gwamnan Anambra, Willie Obiano, Ya Rasu Yana Da Shekaru 70 November 14, 2025
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Wasu Mahara Sun Kashe Mata 2, Tare Da da Ƙona Gidansu A Tudun Yola November 15, 2025 Manyan Labarai Shugaban APC Na Kano Ya Nemi Afuwa Daga Al’ummar Fagge Kan Kalamansa November 15, 2025 Da ɗumi-ɗuminsa Tsohon Gwamnan Anambra, Willie Obiano, Ya Rasu Yana Da Shekaru 70 November 14, 2025
Haka zalika, a 2025, an samu kararraki 28 na ‘yan Nijeriya da suka kashe kansu. Shari’ar ta shafi mutane daga kowane jinsi da kuma masu matsayi daban-daban, ciki har da dalibai da kuma ‘yan kasuwa. Da yake zantawa wani dan jarida, masanin ilimin halayyar Dan’adam, kuma kwararre a kan lafiyar kwakwalwa, Dakta Shuab Waidi ya ce; batun kisan kai a halin yanzu, na bukatar da kulawar gaggawa ga mahukuntan kasa. Ya ce, “Kididdigar na nuna cewa, a kowane minti 33; ana asarar rai a Nijeriya sakamakon kashe kai, don haka, akwai bukatar cikin gaggawa a bude tattaunawa game da kashe kai ta hanyar gwajin lafiyar kwakwalwa. “Cutar tabin hankali, wani bangare ne na kisan kai da kai, amma kashe kai...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Siyasa Injiniya Sagir Ibrahim Ƙoƙi Ya Fice Daga Jam’iyyar NNPP November 12, 2025 Labarai Majalisar Wakilai Ta Yi Tir Da Harin Da Aka Kai Wa Tawagar Ɗan Majalisar Neja November 7, 2025 Siyasa Dalilin Da Ya Sa Sanatoci Ba Su Goyi Bayana Ba Lokacin Da Aka Dakatar Da Ni – Natasha November 4, 2025
Rahotanni sun bayyana cewa jakadan iran a majalisar dinkin duniya Amir Saeid Iravani yayi gargadin cewa Tehran ba za ta taba mika wuya ga matsalin lmbar soji ba, ko ta siyasa ko kuma takunkumin tattalin Arziki, kuma ta yi tir da Amurka da Isra’ila game da harin da ta kai kan tashoshin nukiliyarta da ya sabama doka, da kuma yin fuska biyu a matakenta na kasa da kasa Wannan bayani na Iravani yana zuwa ne adaidai lokacin da zaman tankiya ke kara Kamari bayan hari da Amurka da isra’ila suka kai a watan yuni shekara ta 2025 da muke ciki, wanda iran tace wurare ne dake karkashin kulawar hukumar nukiliya ta Duniya IAEA. Kamalan nasa sun nuna cewa bisa mahangar...
Kasashen Latin Amurka Sun Shirya Tsaf Don Mayar Da Martani Kan Wuce Gona Da Irin Amurka Kan Venuzuwela
Rahotanni sun nuna cewa kasashen latin Amurka sun gudanar da tattaunawa na shirya fitar da sanarwa ta hadin guiwa na shirya mayar da martani kan duk wani hari da kasar Amurka za ta kai a kan kasar Venuzuela, Wakilan diplomasiya na kasashen daban daban sun shirya tuntubar juna domin shirya ma duk wani shirin Amurka na kaddamar da hare-hare, yace idan ba haka ba fadar white hause za ta ji wani karfi ne wajen ci gaban da amfani da karfi wajen cimma manufofinta a yankin. Kasashen brazil, Columbiya, da kuma Maxico za su zama su ne kasahen farko da za su yi tir da duk wani wuce gona da irin Washington , domin Amurka tana zargin karya kan venezuwela cewa...
Rasha Tace Bata Da Shirin Kai wa Kungiyar Nato Hari Amma Za ta Mayar Da Martani Kan Duk Wata Barazana
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha mariya zakhrova ta bayyana cewa Mosko ba ta da wani shirin na kai hari kan wata mamba a kungiyar tsaro ta Nato amma ta shirya mayar da martani kan duk wanda ya kai mata hari daga mambobin kungiyar. Da take taron manenma labarai mariya ta zayyana cewa tana kara maimaitawa babu wani shiri na kai hari kan wata kasa dake mamba a kungiyar tsaro ta nato , sai dai kasar rasha ta riga ta dauki mataken da suka dace na ganin ta samar da tsaronta, adaidai lokacin da abokan hamayya suke gina sansanin soja kusa da iyakar kasarta A cewa Jami’in diplomasiya, bayanan da wasu jami’an kungiyar tsaro ta nato suka fitar bangare ne...
Shugaban kasar iran Msud pezeshkiyan ya kira prime ministan Iraqi mohammad shia al-sudani ta wayar tarho domin taya shi murnar kammala zaben yan majalisar dokoki da aka yi a kasar cikin gagarumar nasara da kuma kwanciyar hankali da tsaro. Kasashen iran da Iraqi kasashe ne masu makwabtaka da juna kuma sakamakon da aka fitar na zaben yan majalisa da aka gudanar zai taka muhimmiyar rawa wajen kara bunkasa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, Ana sa bangaren Al-sudani ya jaddada cewa zaben ya nuna irin yadda alummar iraki suka yi riko da demukuradiya, kuma sakamakon zaben zai taimakawa kasar wajen gudanar da ayyukan ci gaba da gina kasar da gwamnatin tasa a gaba, Shi ma shugaban iran pezeshkiyan ya jinjina game...
M D D Ta yi Tir Da Harin Da Yahudawa Yan Share Wuri Zauna Suka Kai A Masallaci A Yammacin kogin Jodan
Babban sakatare janar din majalisar dinkin duniya Antonio Guterre yayi kakkausar suka game da harin da yahudawa yan share wuri zauna suka kai kan wani masallaci da ya kai ga konewa a Dair Istiya dake yankin da isra’ila ta mamaye a gabar yamamcin kogin jodan, Matakin na majalsiar dinkin duniya na yi tir da kai harin ya nuna irin yadda duniya ta damu matuka game da fitinar da yahudawa yan share wuri zauna suke tayarwa da rawar da suke takawa wajen karuwa rashin zaman lafiya, tsaro a yankunan da aka mamaye. Hare-hare da sojojin isra’ila da yahudawan yan share wuri zaune ke kai wa ya karu sosai a gabar yammacin kogin jodan tun bayan harin oktoba 2023 inda akalla falasdinawa1070...
Rahotanni na nuni da cewa mayaƙan ƙungiyar ISWAP sun yi garkuwa da wani Janar ɗin sojan Najeriya tare da kashe sojoji da dama a wata Arangama a Jihar Borno. Ayaraijn motocin sojojin ya faɗa a harin kwanton ɓaunan mayaƙan ISWAP ne a daren Juma’a a Jihar Borno. Rahotanni na nuna cewa mayaƙan sun yi garkuwa da Janar ɗin tare da hallaka sojoji da dama da ke tare da shi, ciki har da mambobin CJTF. Rahoton kafar HumAngle — cibiyar da ke mayar da hankali kan rikice-rikice da batutuwan jin ƙai — wanda PremiumTimes ta ruwaito, ya ce Janar ɗin da aka yi garkuwa da shi shi ne kwamandan wani bitget ɗin soji, kuma shi ne yake jagorantar dakarun a lokacin....
’Yan banga 16 sun kwanta dama a yayin da ’yan bindiga suka yi garkuwa da mutane 42 a wani hari na daban a Ƙaramar Hukumar Mashegu da ke Jihar Neja. Aminiya ta samu rahoton cewa ’yan bindiga sun kai hare-haren ne daga ranar Alhamis zuwa Asabar, lamarin da ya sa mutane da dama yin ƙaura daga ƙauyuka Wani mazaunin yankin ya shaida wa wakilinmu cewa maharan sun fara kai farmaki ne a ƙauyen Dutsen Magaji, inda suka yunwa mutane 22 kisan gilla. “Da suka kawo hari, ’yan banga sun bi su, ɓangarorin suka yi musayar wuta, amma suka kashe ’yan Banda biyar, wasu uku na karɓar magani a Asibiti.” Gwamnati na jefa makomar ilimi cikin hatsari — ASUU Mutum ɗaya...
’Yan banga 16 sun kwanta dama a yayin da ’yan bindiga suka yi garkuwa da mutane 42 a wani hari na daban a Ƙaramar Hukumar Mashegu da ke Jihar Neja. Aminiya ta samu rahoton cewa ’yan bindiga sun kai hare-haren ne daga ranar Alhamis zuwa Asabar, lamarin da ya sa mutane da dama yin ƙaura daga ƙauyuka Wani mazaunin yankin ya shaida wa wakilinmu cewa maharan sun fara kai farmaki ne a ƙauyen Dutsen Magaji, inda suka yunwa mutane 22 kisan gilla. “Da suka kawo hari, ’yan banga sun bi su, ɓangarorin suka yi musayar wuta, amma suka kashe ’yan Banda biyar, wasu uku na karɓar magani a Asibiti.” Gwamnati na jefa makomar ilimi cikin hatsari — ASUU Mutum ɗaya...
Kyaftin ɗin tawagar ƴan wasa matan Nijeriya ƴan ƙasa da shekara 17 (Flamingos), Shakirat Moshood, na cikin jerin ƴan wasa uku da suka kai matakin ƙarshe domin lashe ƙyautar Matashiyar Ƴar Wasan CAF ta 2025. Sauran ƴan wasan da ke fafatawa da ita su ne Moha El Madani daga Morocco da Adji Ndiye ta Senegal. Moshood ta yi fice a manyan wasanninta a gasar cin kofin Duniya na mata ƴan ƙasa da shekara 17 ta FIFA a 2025, ko da yake tawagar da Bankole Olowookere ke jagoranta ta tsaya a zagaye na 16. A duk tsawon gasar, ta kasance ɗaya daga cikin fitattun ƴan wasan da suka yi ƙwazo a tawagar da kyakkyawan salon wasa. Wasu Mahara Sun Kashe Mata...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Shugaban APC Na Kano Ya Nemi Afuwa Daga Al’ummar Fagge Kan Kalamansa November 15, 2025 Da ɗumi-ɗuminsa Tsohon Gwamnan Anambra, Willie Obiano, Ya Rasu Yana Da Shekaru 70 November 14, 2025 Manyan Labarai Musulmin da Aka Kashe A Zamfara, Katsina Da Sokoto Sun Ninka Na Kiristoci A Tsakiyar Najeriya: MACBAN November 14, 2025
Babi na 25 na sabuwar doka ya shafi batun aure ga jami’ai da sojojin rundunar tsaro. Musamman, Sashe na 5 na wannan takarda ya bayyana cewa “ba a yarda wani jami’i ya auri bakuwa ko kuma dan Nijeriya da aka ba takardar zama ba.” Za A Sake Duba Daftarin HTACOS Bayan Shekara Biyar Sabon Daftarin HTACOS na shekarar 2024, wanda Majalisar Rundunar Sojoji ta amince da shi, ya fara aiki ne a ranar 6 ga Disamba, 2024, lokacin da Shugaban Kasa ya sanya wa takardar hannu. A cewar Babi na 25, Sashe na 1, dan karamin jami’i mai mukamin Second Lieutenant, Midshipman ko Pilot Officer (2Lt/Mid/Plt Offr) yana cikin lokacin gwaji ne, kuma ana tsammanin zai zauna a gidan...
Fashi Da Makami: An Yanke Wa ’Yan Nijeriya Hudu Mazauna Birtaniya Hukuncin Daurin Shekara 55 A Gidan Yari
Ta ce, “Kungiyar ta fi kai hare-hare a shagunan EE, inda suke amfani da barazana da tashin hankali wajen tilasta ma’aikata su bude dakunan ajiya na sirri kafin su gudu da wayoyi masu tsada da sauran na’urori.” A jimlace, sun sace kayayyaki da darajarsu ta kai fam miliyan £240,000. Jami’an tsaro sun gano masu laifin ta hanyar shaidar DNA, da kuma bayanan kira da rikodin motocin da suka yi amfani da su. An ce sun ci gaba da bibiyar kungiyar yayin da take shirin sake kai wani hari, inda a ranar 19 ga Nuwamba, 2024, jami’ai suka yi musu kwanton bauna suka kama mutane hudu daga cikinsu a lokacin da suke kokarin yin fashi a wani shagon EE da ke...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Da ɗumi-ɗuminsa Tsohon Gwamnan Anambra, Willie Obiano, Ya Rasu Yana Da Shekaru 70 November 14, 2025 Manyan Labarai Musulmin da Aka Kashe A Zamfara, Katsina Da Sokoto Sun Ninka Na Kiristoci A Tsakiyar Najeriya: MACBAN November 14, 2025 Manyan Labarai Kotu Ta Yanke Wa Mutum 4 Hukuncin Kisa Kan Kashe Wani Makanike A Kano November 14, 2025
Hukumomin Mali sun dakatar da watsa shirye-shiryen tashoshin gidajen talabijin na kasar Faransa TF1 da LCI a fadin kasar. Hukumar Sadarwa ta Mali ta bayar da dalilan dakatar da wadanan tashohin bisa wani shiri da tashar LCI ta yi kan halin da ake ciki sakamakon matsalolin tsaro masu nasaba da kungiyoyin dake ikirari da sunan jihadi. Shirin mai suna “Grands Dossiers” da aka watsa a LCI a ranar Lahadi, 9 ga Nuwamba, wanda aka raba zuwa sassa biyu ya kunshi kanun labarai kamar haka ” Masu ikirarin Jihadi a Kofofin Bamako” da kuma “Mali, Karkashin kungiyar Al-Qaeda.” A sashen guda, wanda aka dora a shafin yanar gizon tashar TF1+, rahoton yi ikirarin cewa gwamnatin mulkin soja ta haramta sayar da...
Amurka na matsin lamba ga kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya don amincewa da shirin zaman lafiya na shugaba Donald Trump. Amurkar da wasu abokan huldarta na kasashen Larabawa sun yi kira ga Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya da ya “yi sauri” ya amince da daftarin kudurin Amurka wanda ya amince da shirin zaman lafiya na Donald Trump kan Gaza, yayin da Rasha ta gabatar da wani daftarin kuduri na daban kan Gaza. “Amurka, Qatar, Masar, Hadaddiyar Daular Larabawa, Masar, Indonesia, Pakistan, Jordan, da Turkiyya sun bayyana goyon bayansu ga daftarin kudurin na Amurka wanda ya tanadi kafa kwamiti da zai kula da gwamnatin rikon kwarya a Gaza da rundunar kasa da kasa a yankin Falasdinu, da kuma fatan amincewa...
“Da zarar wanda ake zargin ya hango jami’an, ya yi amfani da wuka ya yanki daya daga cikin ’yan sa kai a kugu da hannu, wanda hakan ya jikkata shi sosai,” in ji mai magana da yawun ’yansandan. Ya kara da cewa an garzaya da dan sa kai da ya ji rauni zuwa cibiyar lafiya mafi kusa, inda yake karbar magani a halin yanzu. Bayan binciken jiki da aka yi wa wanda ake zargi, jami’an sun samu bindiga daya ta gida, bindiga daya, da kuma harsasai guda hudu a hannunsa. A cikin martaninsa, kwamishinan ’yansandan jihar, CP Bello Sani, ya yaba da kwararrun ayyuka da dabarun binciken bayanan sirri da kuma hadin kai tsakanin DPO na Illo da tawagarsa tare...
Kungiyar tarayyar Afrika da Majalisar Dinkin Duniya sun karfafa kawancensu kan dabarun tabbatar da zaman lafiya, tsaro da kuma ci gaba don magance kalubalen duniya da na yanki yanki. “Hadin gwiwa tsakanin kungiyoyinmu bai taba kasancewa mafi karfi da muhimmanci fiye da yadda yake a yau ba,” in ji Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya António Guterres. Wannan sanarwar ta zo ne a karshen taron hadin gwiwa na shekara-shekara na 9 na Tarayyar Afirka da Majalisar Dinkin Duniya, wanda aka gudanar a hedkwatar Majalisar Dinkin Duniya da ke New York a ranar Alhamis, wanda Shugaban Hukumar Tarayyar Afirka, Mahamoud Ali Youssouf, da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya António Guterres suka jagoranta. Guterres ya jaddada cewa duniya a halin yanzu...
Iran ta bukaci kasashen duniya dasu gaggauta daukar mataki kan halin da ake ciki a Sudan musamman a yankin El Fasher don magance matsalar dake ta’azzara a arewacin Darfour. Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya, Ali Bahraini, ne ya bayyanan hakan a jawabinsa yayin zaman musamman na 38 kan yanayin kare hakkin dan adam a yankin El Fasher da kewaye a yayin rikicin da ke ci gaba da faruwa a Sudan. Mista Bahraini ya yi gargadi game da yunwa, yawan ‘yan gudun hijira da kuma tasirin tsoma bakin kasashen waje kan rikicin. Wadanan matsalolin sun haifar da daya daga cikin rikicin jin kai mafi muni a duniya, wanda ke bukatar kulawa nan take daga kasashen duniya,” in ji jakadan. Jami’in...
Tarayyar Turai ta yi kira ga Isra’ila da ta dauki mataki nan take don kawo karshen tashin hankali a Yammacin Kogin Jordan. Mai magana da yawun Hukumar Kula da Harkokin Waje ta Tarayyar Turai, na mayar da martani ne kan karuwar tashin hankalin dake da nasaba da yahudawa ‘yan kama wuri zamna da ke yi wa Falasdinawa a Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye. Jami’in ya yi kira ga hukumomin Isra’ila su dauki matakin gaggawa don hana kara tabarbarewar lamarin da kuma gurfanar da wadanda ke da alhakin wannan tashin hankalin. Anwar Al-Aouni, mai magana da yawun Tarayyar Turai, da ke magana a taron manema labarai ranar Juma’a, ya nuna karuwar hare-haren da ‘yan kama wuri zamna na Isra’ila ke...
Bangaren sauka na kumbon Shenzhou-21, dauke da ‘yan sama jannatin na kumbon Shenzhou-20 wato Chen Dong, da Chen Zhongrui, da Wang Jie ya sauka doron duniya cikin nasara. Sundukin ya sauka ne a yau Jumma’a a yankin Dongfeng na jihar Mongolia ta gida mai cin gashin kai, dake arewacin kasar Sin, kamar dai yadda aka tsara. Rahotanni na cewa, dukkanin ‘yan sama jannatin suna cikin koshin lafiya. Kafin dawowarsu doron duniya sun shafe kwanaki 204 a sararin samaniya, lokaci mafi tsayi da ‘yan sama jannatin kasar Sin suka taba shafewa a samaniya, kamar dai yadda hukumar kula da zirga-zirgar kumbuna masu dauke da ‘yan sama jannati ta Sin ko CMSA ta sanar. ADVERTISEMENT Kwamandan ‘yan sama jannatin Chen Dong, shi...
A nasa jawabin, Kwamishinan PPMF, Prince Aliyu Abdulrazaq, ya shawarci kwamitin da su gudanar da aikinsu da amana, gaskiya, da ƙwarewa, yana mai cewa dole ne amincewar da Hukumar ta yi musu ta bayyana a sakamakon aikinsu. Da yake magana a madadin kwamitin, Jagoran Kwamitin, Dr. Haruna Danbaba, ya tabbatar wa Hukumar cewa za su bi dukkann ka’idojin da Ƙasar Saudiyya ta shimfiɗa, tare da tabbatar da cewa ba’a samu jinkirin wajen gudanar da aikin kwamitin ba. Ƙaddamar da kwamitin na daga cikin manyan matakai na farkon shirin NAHCON domin Hajjin 2026, kuma ana sa ran fara aiwatar da muhimman ayyuka nan take. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Kotu Da Ɗansanda NSCDC Ta Cafke Mutum Biyu Bisa Zargin Satar NAPEP Da...
Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU), reshen Nsukka ta ce Gwamnatin Tarayya na lalata makomar ƙasar nan saboda rashin cika yarjejeniyar 2009. A taron manema labarai da ta gudanar a Jami’ar Jihar Benuwe da ke Makurdi, Kodinatan yankin, Kwamared Christian Opata, ya ce gwamnati ba ta jajirce wajen magance matsalolin da suka shafi ɓangaren ilimi. Ya yi magana ne a madadin jami’o’i takwas da ke yankin. Opata, ya ce an tattauna tare da ƙumla yarjejeniyoyi da dama tsakanin ASUU da gwamnati tsawon shekaru, amma babu wani ci gaba da aka samu. Ya zargi jami’an gwamnati da yin lƙawarin ƙarya da gangan. Ya ce ASUU ta dakatar da yajin gargaɗin da ta yi kwanan nan saboda ɗalibai, iyaye, da ƙungiyoyin ƙwadago,...
Ya kara da cewa yayin gudanar da aikin, jami’an hukumar sun gano babura hudu daga hannun wanda ake zargi babura uku na Jincheng da daya na Lifan Kumata, inda ya ce ana ci gaba da neman sauran abokan aikinsa biyu da suka tsere. Haka kuma, ya bayyana cewa an kama mai safarar miyagun kwayoyi mai suna Salisu Abdullahi, dan shekara 28, mazaunin Semegu a Karamar Hukumar Kumbotso, a yankin Sabon Titin Dorayi, tare da tarin miyagun kwayoyi da ake zargin yana sayarwa don amfani na haram. Kwayoyin da aka samo daga hannunsa sun hada da kwayoyi 100 na Padol 5mg, kwayoyi 30 na Pregabalin 300mg, kwayoyi 170 na Diazepam 10mg, da kuma kwaya guda daya ta karin karfin maza. Sanarwar...
Da yake ƙarin haske kan muhimman sassan da aka fi bai wa fifiko, Gwamnan ya bayyana cewa, ɓangaren tattalin arziƙi da ci gaban al’umma ne suka samu kaso mafi tsoka na kasafin kuɗin, inda aka ware sama da Naira biliyan 269 don sanya hannun jari a muhimman fannoni. Fannin ayyuka, gidaje da sufuri ne ke kan gaba da Naira Biliyan 135.9, sai ruwa, muhalli da gandun daji da aka warewa Naira Biliyan 88.4, yayin da noma, kiwo da ƙungiyoyin gama ya samu Naira biliyan 20.57. A fannin harkokin zamantakewa, an ware Naira biliyan 80 don samar da ayyukan ci gaba da gina jama’a, inda ilimi ya samu Naira biliyan 31.9, yayinda ilimi mai zurfi ya samu Naira biliyan 17.5. Ɓangaren...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Saman Yaki Na Sichuan Ya Fara Gwajin Sufuri A Karon Farko November 14, 2025 Daga Birnin Sin Xi Jinping Ya Gana Da Sarkin Thailand November 14, 2025 Daga Birnin Sin Babban Taron Kawancen Sin Da Afirka Ya Nuna Hadin Gwiwa Kan Gudanar Da Tsarin Shugabancin Duniya Na Bai-Daya November 14, 2025
Da misalin karfe 9:00 na safiyar yau Juma’a ne farkon matsakaicin jirgin ruwan yaki dankon jirage masu saukar ungulu na yaki samfurin 076 na kasar Sin, wato jirgin ruwa na Sichuan, ya tashi daga tashar jirgin ruwa ta kamfanin kera jiragen ruwa na Hudong-Zhonghua a Shanghai, zuwa wani yankin teku don gudanar da gwajin sufuri a karon farko. Gwajin sufurin a kan teku, zai mayar da hankali ne kan tabbatar da ingancin tsarin motsi, da sarrafa wutar lantarkin jirgin ruwan na Sichuan. An bayyana cewa, tun lokacin da aka sanya jirgin cikin ruwa a watan Disamban shekarar 2024, an ci gaba da ginin jirgin ruwan na Sichuan bisa tsari, an kuma kammala gwajin tsayawa, da kuma daidaita kayan aiki, wanda...
An kashe wani da ake zargin ɗan bindiga ne, yayin wani artabu da ’yan sanda da ’yan sa-kai suka yi da wasu mahara a Jihar Kwara. Lamarin ya faru ne a ƙauyen Adekanbi, kusa da garin Bode Saadu. Kotu ta sake hana PDP gudanar da babban taronta na ƙasa Mutfwang ya musanta raɗe-raɗin sauya sheƙa zuwa YPP Rahotanni sun nuna cewa ’yan bindigar sun yada zango a saman wani dutse da ke kallon ƙauyen. Suna hangar jami’an tsaro sai suka fara harbi ba ƙaƙƙautawa. ’Yan sanda da jami’an sa-kai sun yi artabu tare da tarwatsa maharan, inda wasu daga cikinsu suka tsere da raunin harbin bindiga. Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Adetoun Ejire Adeyemi, ta tabbatar da faruwar lamarin...
An yi hadaka tsakanin asusun da ke tallafa wa bunkasa aikin noma na kasa (NADF) da kuma Gwamnatin Jihar Jigawa, inda suka kaddamar da shiri na farko na bai wa manoma bashin noma. A cikin sanawar da asusun ya fitar, shirin zai bayar da dama ga masu zaman kansu, musamman kananan manoma wajen ba su bashin kudin noma tare kuma da kara samar musu da wadataccen abinci. Neman Gurbin Kofin Duniya: Nijeriya Ta Lallasa Gabon Da Ci 4 Sanarwar Taron Ministocin Harkokin Waje Na Kungiyar G7 Ba Ta Da Tushe Babban Sakataren Asusun, Mohammed Ibrahim ya bayyana cewa; shirin zai magance gibin da kananan manoma ke fuskanta wajen samun rance kudaden noma. ADVERTISEMENT Shi kuwa, Darakta Janar na Hukumar Bunkasa...
Da safiyar yau Juma’a 14 ga watan Nuwamba, a nan birnin Beijing, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da sarkin Thailand Maha Vajiralongkorn wanda yake ziyarar aiki a nan kasar Sin. Yayin ganawar tasu shugaba Xi ya ce, sarkin ya sanya kasar Sin a matsayin babbar kasa ta farko da ya kai ziyara. Hakan ya tabbatar da kasancewarsa sarkin Thailand na farko da ya taba ziyartar kasar Sin, tun bayan kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Thailand, wanda hakan ya shaida muhimmancin dangantaka tsakanin kasashen biyu, da kuma dankon zumuncin dake akwai tsakanin Sin da Thailand. A nasa tsokacin kuwa, sarkin ya ce Thailand na fatan koyon darussa daga kwarewar ci gaban Sin, da fadada hadin gwiwa a fannoni...
An fara koyar da aikin jarida a Nijeriya tun farkon bayan samun ‘yancin kai, kuma BUK ta kasance cikin jami’o’in farko da suka kafa sashen Koyar da Aikin Jarida (Mass Communication). A tsawon shekaru, jami’ar ta samar da fitattun ‘yan jarida, malamai, da ƙwararrun ma’aikatan kafofin watsa labarai da ke taka rawa a fadin ƙasar. An gina ra’ayin kafa wannan cibiyar ne a ƙarƙashin jagorancin Farfesa Umaru A. Pate, shahararren masani a fannin jarida kuma jajirtaccen mai fafutukar gyaran tsarin kafafen yaɗa labarai a ƙasa. Hangen nesa da shawarwarinsa sun taka muhimmiyar rawa wajen zurfafa madogarar bincike da ci gaban ilimin jarida a BUK. Da zarar an kammala cikakken kafuwar cibiyar, ana sa ran za ta ƙara ɗaukaka sunan Jami’ar...
Babban Taron Kawancen Sin Da Afirka Ya Nuna Hadin Gwiwa Kan Gudanar Da Tsarin Shugabancin Duniya Na Bai-Daya
Babban taron dandalin kafafen yada labarai na kasashe masu tasowa da kwararru na kawancen Sin da Afirka da aka bude a jiya Alhamis a birnin Johannesburg da ke kasar Afirka ta Kudu, zai lalubo hanyoyin karfafa hadin gwiwa, da fadada yin magana da murya daya a tsakanin kasashe masu tasowa da kuma habaka gudanar da tsarin shugabancin duniya na bai-daya. Wanda kamfanin dillancin labarai na Xinhua, da Tarayyar Afirka (AU) da kamfanin Independent Media na kasar Afirka ta Kudu da sauran abokan hulda suka shirya, taron na kwanaki biyu ya samu halartar wakilai sama da 200 daga kafofin watsa labarai fiye da 160, da kungiyoyin kwararru, da hukumomin gwamnati da sauran cibiyoyi daga kasar Sin da kasashen Afirka 41, da...
Ministan yakin Amurka Pete Hegseth ya bayyana cewa kasar tasa ta fara kai farmakin da ta kira ” Mashin Kudu” akan dillalan muggan kwayoyi. Ministan yakin na Amurka ya rubuta a Shafin X cewa; manufar wannan farmakin shi ne kare kasarmu, da kawo karshen masu dillancin muggan makamai ‘yan ta’adda, da kare kasarmu daga muggan kwayoyin da suke kashe mana ‘yan kasa.” Gwamnatin Donald Trump dai ta bude kai hare-hare akan jiragen ruwan a doron ruwan Carrebia da tekun Pacific bisa abinda take riya cewa masu fataucin muggan kwayoyi ne. Sai dai har yanzu babu wani dalili guda daya da Amurkan ta gabatar da shi wanda yake nuni da cewa wadannan jiraegen ruwa da take kai wa harin suna dauke...
Kasar Cote De Voire ta sanar da tsaurara harkokin tsaro akan iyakokinta na Arewa domin fuskantar ‘yan hijira da suke kwararowa daga kasar Mali da take fama da rikicin masu dauke da makamai. Majalisar tsaron kasar “Cote De Voire” ce ta bai wa sojojin kasar umarni da su tabbatar da tsaro a kan iyakoki, kamar yadda gwamanti ta bayyana. A can cikin kasar Mali mai makwabtaka da “Cote De Voire” ana samun karuwar hare-haren masu dauke da makamai akan fararen hula da hakan yake kara yawan kwararan ‘yan hijira. Mali wacce ba ta da iyaka ta ruwa tana fama da rikickin masu dauke da makamai dake da alaka da kungiyar alka’ida da su ka tsananta kai hare-hare daga watan Satumbar...
Jamhuiryar Demokradiyyar Congo ta fitar da ma’adanin ‘Colbat’ da ya kai ton 1,000 a karon farko. Shi dai wannan ma’adanin ne ake amfani da shi wajen yin batirin “Lithium-ion” masu cajin motoci mai amfani da wutar lantarki, wayoyin hannu, kwamfuta da suaransu. Bugu da kari wannan ma’adanin yana taka rawa wajen kauracewa amfani da makamashin da da yake gurbata muhalli. A cikin kasar DRC kadai ne ake samun kaso 72 % na dukkanin wannan ma’adanin da ake da shi a duniya. Da akwai mutanen da sun kai miliyan 1.5 da suke aiki a wuraren hako wannan ma’adanin a cikin kasar ta Jamhuriyar Demokradiyyar Congo. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to...
Wanda ya jagoranci sallar juma’a a Tehran Ayatullah Sayyid Ahmad Khatami ya yi kira ga jami’an diplomasiyyar kasar Iran da su kai karar shugaban kasar Amurka Donald Trump a kotunan kasa da kasa, bayan da ya yi furuci da cewa shi ne ya jagroanci harin da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta kawo wa Iran. Ayatullah Sayyid Ahmad Khatami ya kuma kara da cewa, ya kamata a fitar da bayani na yin tir da wannan maganar sannan kuma a kai kara a cibiyoyin duniya. Da ya koma yin Magana akan hijabi kuwa, limamin na Tehran ya bayyana cewa, sanya hijabi ga mata,hukunici ne da addini da kuma doka, sannan ya ambato wani marubuci dan Amurka da yake cewa: Idan har matan Iran...
Mataimakin ministan harkokin waje na kasar Sin Sun Weidong ya gana da jakadan Japan a Sin Kishi Nobuo bisa umurnin gwamnatin kasar a jiya Alhamis, inda ya yi tsokaci a hukumance kan kalaman da firaministar Japan Takaichi Sanae ta yi game da kasar Sin. Sun ya ce, batun Taiwan na da matukar muhimmanci cikin muradun Sin, kuma ba za a iya tauye shi ba. Taiwan yanki ne na Sin, kuma harkokin Taiwan batu ne na cikin gidan Sin. Tsara yadda za a warware matsalar Taiwan aiki ne na kasar Sin, kuma ba za a yi katsalandan a kai ba. Bana ta cika shekaru 80 da samun nasarar yakin da Sin ta yi da mamayar dakarun Japan da kuma yakin duniya...
An sanya ranar 25 ga watan Nuwamba a matsayin ranar da za a fara shari’arsa kan zargin karkatar da biliyoyin kuɗi da EFCC ta gabatar. Obiano ya yi gwamna a Jihar Anambra daga 2014 zuwa 2022. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Musulmin da Aka Kashe A Zamfara, Katsina Da Sokoto Sun Ninka Na Kiristoci A Tsakiyar Najeriya: MACBAN November 14, 2025 Manyan Labarai Kotu Ta Yanke Wa Mutum 4 Hukuncin Kisa Kan Kashe Wani Makanike A Kano November 14, 2025 Manyan Labarai Bayan Barazanar Amurka: Sultan Ya Nemi Hadin Kan ‘Yan Nijeriya Wajen Yaki Da Ta’addanci November 14, 2025
El-Rufa’i ya kara da cewa mutane amintattu za a ba su mukamai idan ADC ta samu nasarar kwace mulki a hannun APC a 2027, yana mai cewa cewa kashi 40 cikin dari na mukamai za su je ga matasa. Ya yi kira ga magoya bayansa da su kiyaye masu yaudara da ke kokarin raba kan jam’iyyar, yana cewa, “APC ba za ta bar ku ku tafi cikin sauki ba, ku yi hankali.” Haka kuma, ADC ta gudanar da taron masu ruwa da tsaki a Jihar Zamfara, wanda mataimakin sakataren gudanarwa na kasa na jam’iyya ya shirya, don karfafa hadin kai tsakanin ‘yan jam’iyya da kuma karfafa musu gwiwar yin rajista da samun katin zabe. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Tambarin Dimokuradiyya Rikicin...
Bayan hukunci, kwamitin gudanarwa karkashin shugabancin Damagum ta dakatar da sakataren jam’iyyar na kasa, Sanata Samuel Anyanwu da mashawarcin shari’a na kasa, Kamaldeen Ajibade da sakataren shirye-shirye na kasa, Umar Bature na tsawon wata guda saboda zargin ayyukan da ke goyon bayan abin da ya saba wa jam’iyya. Bayan awanni 24, Anyanwu da magoya bayansa sun hadu a Abuja suka sanar da dakatar da Damagum da dukkan mambobin kwamitin gudanarwa na jam’iyyar. Sun kuma bayyana sunan mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na Arewa ta tsakiya, Abdulrahman Mohammed, a matsayin sabon mukaddashin shugaban jam’iyya kasa. Yayin da bangarorin biyu suke kalubalantar junansu, bangaren da Damagum ke jagoranta ya samu umurnin alkalin babban kotun Jihar Oyo, Ladiran Akintola, wanda ya umartar PDP da...
Kasar Sin ta kara azamar kirkiro da fasahar sadarwa mai karfin 6G a cikin ’yan shekarun nan, inda ta samu ci gaba a bangaren binciken fasalin tsarin fasahar ta 6G da kuma zayyanar hanyar sadarwarta, kamar yadda ma’aikatar masana’antu da fasahar sadarwa ta zamani ta kasar ta bayyana a jiya Alhamis. A yayin gudanar da taron bunkasa fasahar 6G na shekarar 2025, mataimakin ministan masana’antu da fasahar sadarwa ta zamani na kasar Sin Zhang Yunming ya bayyana cewa, yanzu haka kasar tana da muhimman fasahohi na kirkiro da fasahar sadarwar 6G sama da 300. Zhang ya kara da cewa, kasar ta hada kan kamfanoni sama da 100 na cikin gida da na waje a fannin tsarin masana’antu, kuma ta gayyaci...
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta sake hana jam’iyyar PDP gudanar da babban taronta na ƙasa da ta ke shirin yi. Alƙalin kotun, Mai Shari’a Peter Odo Lifu, ya yanke hukuncin ne a ranar Juma’a. Mutfwang ya musanta raɗe-raɗin sauya sheƙa zuwa YPP Mutfwang ya musanta raɗe-raɗin sauya sheƙa zuwa YPP Ya ce taron da aka tsara yi a Ibadan a ranar 15 da 16 ga watan Nuwamba ba za a gudanar ba sai an bai wa tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, damar sayen fom ɗin takarar kujerar shugaban jam’iyyar na ƙasa. Alƙalin ya kuma umarci INEC da kada ta sanya baki ko ido a kan taron har sai an bai wa Lamido damar sayen fom. Lifu, ya...
Kwanan baya, firayim ministan Japan Takaichi Sanae ta yi ikirari a fili cewa, “lamarin Taiwan lamari ne na Japan”, kuma tana da alaka da aiwatar da ikon kare kai na gama kai, inda a karon farko hakan ya nuna tsoma baki cikin batun Taiwan ta hanyar amfani da makamai, kuma a karon farko ya yi barazanar yin amfani da karfin tuwo kan kasar Sin. Kalaman Takaichi game da Taiwan sun tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasar Sin, kuma sun saba wa dokokin kasa da kasa da ka’idojin asali na dangantakar kasa da kasa, da lalata tsarin kasa da kasa bayan yakin duniya na biyu, kana sun saba wa ka’idar “kasar Sin daya tak a duniya” da ruhin takardu hudu...
Ɗalibar Aji uku a Sashen Nazarin Harkar Noma na Jami’ar Bayero ta Kano, Ramatu Yakubu, ta samu kyautar mota wadda kuɗinta ya kai Naira miliyan 35 a gasar da kamfanin MTN ya shirya a jami’ar. Gasar wadda aka shafe kwanaki uku ana yi mai taken MTN “GoMAD on Campus,” wadda aka tsara domin tallafawa da nishaɗantar da ɗalibai ta hanyar wasanni, fasahar zamani da sauransu. Cin ganda na sa Najeriya tafka asarar $5bn — Gwamnatin Tarayya Majalisar Wakilai ta dage lokacin fara yin jarabawar WAEC a kwamfuta zuwa 2030 Ramatu ta lashe manyan kyaututtuka bayan shiga gasa daban-daban, inda sauran ɗalibai ma suka samu kyautar kwamfuta, wayoyi da kuɗi. Manajan Sashen Matasa na MTN a Najeriya, Femi Adesina, ya ce...
Ɗalibar Aji uku a Sashen Nazarin Harkar Noma na Jami’ar Bayero ta Kano, Ramatu Yakubu, ta samu kyautar mota wadda kuɗinta ya kai Naira miliyan 35 a gasar da kamfanin MTN ya shirya a jami’ar. Gasar wadda aka shafe kwanaki uku ana yi mai taken MTN “GoMAD on Campus,” wadda aka tsara domin tallafawa da nishaɗantar da ɗalibai ta hanyar wasanni, fasahar zamani da sauransu. Cin ganda na sa Najeriya tafka asarar $5bn — Gwamnatin Tarayya Majalisar Wakilai ta dage lokacin fara yin jarabawar WAEC a kwamfuta zuwa 2030 Ramatu ta lashe manyan kyaututtuka bayan shiga gasa daban-daban, inda sauran ɗalibai ma suka samu kyautar kwamfuta, wayoyi da kuɗi. Manajan Sashen Matasa na MTN a Najeriya, Femi Adesina, ya ce...
Ɗalibar Aji uku a Sashen Nazarin Harkar Noma na Jami’ar Bayero ta Kano, Ramatu Yakubu, ta samu kyautar mota wadda kuɗinta ya kai Naira miliyan 35 a gasar da kamfanin MTN ya shirya a jami’ar. Gasar wadda aka shafe kwanaki uku ana yi mai taken MTN “GoMAD on Campus,” wadda aka tsara domin tallafawa da nishaɗantar da ɗalibai ta hanyar wasanni, fasahar zamani da sauransu. Cin ganda na sa Najeriya tafka asarar $5bn — Gwamnatin Tarayya Majalisar Wakilai ta dage lokacin fara yin jarabawar WAEC a kwamfuta zuwa 2030 Ramatu ta lashe manyan kyaututtuka bayan shiga gasa daban-daban, inda sauran ɗalibai ma suka samu kyautar kwamfuta, wayoyi da kuɗi. Manajan Sashen Matasa na MTN a Najeriya, Femi Adesina, ya ce...
Haka zalika, ya kafa hujjojinsa a kan “Rashin biyan ‘yan fansho a kan lokaci”, “Jigata’Yan-fansho Da Sunan Tantancewa”, “Jefa Razani A Zukatan Maikata”, da ”Salwantar Da Kudaden ‘Yan-fanshon”. Wadannan bayanai na Anwar, sun tabbatar da ko dai bai san abin da ya faru a Hukumar Fansho a lokutan da Kwankwaso ya yi Gwamnan Kano ba, ko kuma shi dan kanzagin wani dan siyasa ne da yake so ya kambama, duk da tauraruwarsa ta disashe. Duk wanda ya san yadda mulkin Kwankwaso ya inganta rayuwar ‘yan fansho a Jihar Kano, ya san cewa; duk abubuwan da Anwar ya fada ba gaskiya ba ne. A tarihin biyan fansho da garatuti a Jihar Kano, babu lokacin da ‘yan fansho suka ji dadi; irin...
Tawagar Super Eagles ta Nijeriya za ta gwabza da Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo a wasan ƙarshe na tantance wakilin Afrika a share fagen Gasar Cin Kofin Duniya na 2026. Wasan zai ɗauki hankali zai gudana ne a ranar Lahadi a sabon filin Prince Moulay Abdellah da ke Rabat, Morocco, inda za a tantance ƙasa ta ƙarshe daga Afrika da za ta shiga matakin share fagen gasar Kofin Duniya. Nijeriya ta samu gurbin wasan ƙarshe bayan da ta lallasa Gabon da ci 4-1 a ranar Alhamis, sakamakon da ya ƙarfafa matsayin tawagar wajen sake samun martabarta a nahiyar. A ɗaya ɓangaren, DR Congo ta samu nasarar da ta ba ta gurbin wasan ƙarshe ne bayan da ta doke Kamaru da ci 1-0,...
A cewarsa, damar kauwancin da ake samu daga fannin an same ta ne, saboda yadda Matatar ta Dangote, ke sarrafa danyen Mai wanda kuma ‘ya’yan kungiyar, ke son ganin sun amafana da hakan daga Matatar ta Dangote. Madugu ya ci gaba da cewa, wasu daga cikin bangarorin da kungiyar za ta amfana daga Matatar ya ce, sun hada da, Man da ake sarrafawa daga danye Mai, Man Dizil, Kalanzir, Man Jirgin Sama da kuma Iskar Gas, samfarin LPG. Sauran ya ce, sun ne, sanadaran naphtha, bitumen, ethylene, propylene da sauransu. Kazalika, ya kuma jinjinawa Shugaban rukunin Matatar Man ta Dangote, Aliko Dangote, bisa namijin kokarin da ya yi, na kafa Matatar Man a kasar nan. Tawagar ta kungiyar MAN, ta...
Cibiyar dake kula da noman dabino ta kasa a Iran, ta ce kasar ta zamo ta farko wajen fitar da dabino a duniya, inda take samar da tan miliyan 1.5 a kowace shekara. Bayannin ya zayyana Kasashe goma mafiya samar da dabino a duniya wadanda su ne Masar, Saudiyya, Iran, Aljeriya, Pakistan, Iraki, Sudan, Hadaddiyar Daular Larabawa, Oman, da Tunisiya, wanda ya nuna Iran na cikin kasashe na uku na farko. Kuma a yadda Iran ke fitar da tan 430,000 na dabino a kowace shekara, hakan ya sa ta kasance ta farko wajen fitar da dabino a duniya, sai Saudiyya da tan 390,000 sai kuma Hadaddiyar Daular Larabawa da tan 330,000. Fitar da dabino daga Iran an kiyasta yana samar...
Rasha, China, da wasu kasashen Larabawa da dama sun nuna damuwa game da tsarin mulkin bayan yaki da kuma rashin wani muhimmin matsayi ga Hukumar Falasdinu bayan yakin Gaza da aka gabatar a daftarin kudirin shirin tsagaita wuta na Shugaba Donald Trump na Amurka. Duk da cewa jami’an diflomasiyyar kasashen sun yarda cewa tattaunawa ta kai ga cimma yarjejeniyar, amma rarrabuwar kawuna tsakanin Washington da wasu membobin kwamitin tsaron na Majalisar Dinkin Duniya, bayan fiye da shekaru biyu na kisan kare dangi. Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio ya ce ya kamata a amince da kudurin nan take, yana mai jaddada bukatar gaggauta amincewa da shirin. Daftarin farko na Amurka, wanda aka rarraba a makon da ya gabata, ya yi...
Kwamatin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya tsawaita da shekara guda wa’adin aikin tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya. Duk da shakkun da Amurka ta yi, Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, ya tsawaita wa’adin aikin tawagar ta MINUSCA, a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya har zuwa ranar 15 ga Nuwamba, 2026. Duk da haka, Majalisar ta nuna yiwuwar rage wa’adin saboda shiryen shiryen zaben da ake yi a shekarar 2026. An amince da kudurin da kuri’u 14 sai kuma kin amincewa daga Amurka. An samar da tawagar ta MINUSCA a watan Afrilun 2014 don kokarin kawo karshen yakin basasar da ya biyo bayan juyin mulkin da aka yi a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya kan...
Kasashen Iran da Turkiyye sun jaddada mahimmancin karfafa zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin. Wannan bayyanin ya fito ne bayan tattaunawar wayar tarho data wakana tsakanin ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi, da takwaransu na Turkiyye Hakan Fidan, game da dangantakar dake a tsakanin kasashen biyu da kuma halin da ake ciki a yankin da ma duniya. A yayin tattaunawar ta wayar tarho, Ministocin Harkokin Wajen Iran da Turkiyya sun yi nazari kan dangantakar kasashen biyu kuma sun jaddada muhimmancin karfafawa da bunkasa dangantaka a dukkan fannoni masu amfani. Yayin da yake yaba wa kokarin rage tashin hankali tsakanin Pakistan da Afghanistan, Ministan Harkokin Wajen Iran ya jaddada muhimmancin karfafa shawarwari don kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a...
Tehran ta yi Allah wadai da sanarwar da kasashen gungun G7 suka fitar kwanan nan, wadda ta amince da matakan da Amurka da Tarayyar Turai suka dauka na mayar da takunkumin Majalisar Dinkin Duniya kan shirin nukiliya na zaman lafiya na Iran. Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Esmail Baghai ya bayyana zarge-zargen kin jinin Iran dake kunshe a cikin sanarwar karshe ta gungun kasashen da suka hada da (Faransa, Amurka, Kanada, Japan, Burtaniya, Italiya, da Jamus), a matsayin “marar tushe, kana mai cike da karairayi.” Baghhai ya yi ikirarin cewa yunkurin Amurka da Tarayyar Turai na mayar da takunkumin kai tsaye daidai yake da amincewa da wani laifi na kasa da kasa. Da yake sukar kasashen kungiyar...
Portugal ta shiga wasan ne da kwarin gwiwar cewa nasara za ta tabbatar mata da gurbin zuwa gasar cin kofin duniya da za a yi a Amurka, Kanada da Mexico. Sai dai kwallaye biyu na Troy Parrott suka tarwatsa burinsu a Dublin. Duk da haka, Portugal har yanzu tana saman rukunin F da maki biyu a gaban Hungary, kuma za ta iya kammala tikitin shiga gasar idan ta doke Armenia a ranar Lahadi. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Neman Gurbin Kofin Duniya: Nijeriya Ta Lallasa Gabon Da Ci 4 November 13, 2025 Wasanni Dalilai 5 Da Suka Jefa Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa Ta Kano Pillars Cikin Matsaloli A Kakar Wasa Ta 2024/25 November 13, 2025 Wasanni Nijeriya Za...
Kungiyar Editocin Nijeriya (NGE) ta yi gargadi cewa yanayin da tattalin arzikin da kasar nan ke ciki ya jefa kafofin yada labarai cikin wani mawuyacin hali. Kungiyar ta kuma yi kira da a soke dokokin da ke takura ‘yancin ‘yan jarida. Shugaban NGE, Mista Eze Anaba, ya bayyana haka ne a jawabin maraba da ya yi a Taron Editocin Nijeriya Gabadaya (ANEC) mai taken “Dimokuradiyya, Gudanarwa da Hadin Kan Kasa: Rawar da Editoci ke Takawa,” wanda aka gudanar a dakin taro na Tarayya, Abuja. Ya yi nanata cewa halin tattalin arziki a kasar ya tilasta wasu gidajen jarida rufewa, yayin da wasu da ke kokarin ci gaba da aiki ba sa iya biyan albashin ma’aikata. A cewarsa, wannan lamari ne...
Shugaba Kasa Bola Ahmed Tinubu ya sake nada Birgediya-Janar Mohammed Buba Marwa (mai ritaya) a matsayin Shugaban Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) na tsawon shekaru biyar masu zuwa. Bayo Onanuga, Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Yaɗa Labaru, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranar Juma’a. An kama ’yan Najeriya 3 a Kenya kan zargin aikata damfara Majalisar Wakilai ta dage lokacin fara yin jarabawar WAEC a kwamfuta zuwa 2030 An fara nada Marwa a watan Janairu 2021 ta hannun Marigayi Shugaba Muhammadu Buhari ne ya fara naɗa Buba Marwa a muƙamin a watan Janairun 2021, bayan ya jagoranci Kwamitin Shugaban Kasa na Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi daga shekarar 2018...
Hukumar Shari’a ta Jihar Kano ta bayyana jin daɗinta da wannan hukunci, inda Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Maude Kabir, ta bakin mai taimaka masa a fannin yaɗa labarai, Abubakar Tijjani Ibrahim, ya ce hukuncin ya tabbata ne don tabbatar da adalci kamar yadda doka ta tanada. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Bayan Barazanar Amurka: Sultan Ya Nemi Hadin Kan ‘Yan Nijeriya Wajen Yaki Da Ta’addanci November 14, 2025 Manyan Labarai Jan Aikin Da Ke Gaban Manyan Hafsoshin Tsaron Nijeriya November 14, 2025 Manyan Labarai Neman Gurbin Kofin Duniya: Nijeriya Ta Lallasa Gabon Da Ci 4 November 13, 2025
Kazalika, ta amince da kulla wannan yarjejeniyar ce a shekarar 2023. A na sa jawabin a wajen kulla yarjejeniyar Babban Shugaban Tashar ta Snake Island Maher Jarmakani ya bayyana wannan hadakar a tsakanin Gwamnatin Tarayya da da Nigerdock mai matukar mahimmanci. Ya sanar da cewa, yarjejeniyar ta kai ta akalla dala biliyan daya wacce kuma za ta bayar da damar zuba hannun jari daga ketare na kai tsaye, inda hakan zai kuma kara daga matsayin Nijeriya wajen gudanar da hada-hadar kasuwanci a duniy. “Mun bi duk matakan da suka kamata domin mu tabatar da cewa, an bi ka’ida bayan amincewa da Tashar ta Snake Island da Gwamnatin Tarayyata yi, “A cewarsa. Jarmakani ya ci gaba da cewa, wannan jarjejeniyar za...
An kama ’yan Najeriya uku a rukunin gidaje na Mwaliko da ke garin Mwea a ƙasar Kenya, bisa zargin su da damfara ta intanet. Rahoton da wata kafar labarai a Kenya mai suna Tuko News ta fitar ya ce Hukumar Binciken Laifuka ta ƙasar (DCI) ce ta kama waɗanda ake zargin a ranar Laraba. Majalisar Wakilai ta dage lokacin fara yin jarabawar WAEC a kwamfuta zuwa 2030 Yahudawa sun banka wa masallaci wuta a Yammacin Kogin Jodan Waɗanda aka kama sun haɗa da Peter Chukwujekwu, Alazor Chukulute Sunday, da Nnalue Chiagozie Samwe. A cewar rahoton da aka fitar a ranar Alhamis, an kama su a gidansu bayan jama’a sun kai ƙorafi kan take-takensu musamman da daddare a cikin ginin. DCI...
Shugaban ya bayyana cewa, taron ya kuma mayar da hankali wajen wanzar da tsare-tsare, inda hakan ne, itama Hukumar ta NPA, ta mayar da hankali a kai. “Tekunan da suke a tsakanin kasasehn sun kasance wani babban nauyi a kan mu na tabbatar da cewa, kasashen da ke a cikin kungiyar, sun amfana da su,” A cewar Shugaban. Shugaban ya kuma bukaci mahalarta taron da su dauki kansu a matsayin jakadun bunkasa makomar fannin tattalin arzikin Afrika. Ya kara da cewa, kara ingnata kayan aiki da ke a Tashoshin Jiragen Ruwa da kara bunkasa tsaro da tabbatar da ana bin ka’ida. Shugaban ya kuma yabawa Gwamnatin kasar ta Jamhuriyar Kngo da kuma alummar kasar, bisa karbar bakuncin taron kungiyar a...