Nukiliya : Iran zata sake duba huldarta da IAEA idan aka dauki wani sabon mataki kanta
Published: 17th, November 2025 GMT
Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ta bayyana cewa za ta dauki mataki idan idan Kwamitin Gwamnonin Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) ya amince da wani sabon kuduri da bai dace da Iran ba.
Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Iran Kazem Gharibabadi, ne ya bayyana hakan, a gefen taron kasa da kasa mai taken ‘’yancin kasa da kasa na fuskantar barazana a martanin ga kungiyar tarayyar Turai a sahun gaba (Faransa, Burtaniya, da Jamus) da suka gabatar da wani sabon kuduri kan Iran a taron Kwamitin Gwamnonin IAEA na mako mai zuwa.
“Ina fatan Tarayyar Turai za ta yi aiki da hankali kuma ba za ta gabatar da kudurin a hukumance ba, amma idan ta yi, Iran za ta yi gyara na asali ga manufofinta,”.
Mista Gharibabadi ya kara da cewa kasashen Turan uku sun janye daga tattaunawa da duk wasu hanyoyin diflomasiyya da Iran ta hanyar kaddamar da tsarin nan na snapback, wanda ya sake dawo da takunkumin Majalisar Dinkin Duniya kan Iran bisa fakewa da shirin nukiliyarta na zaman lafiya.
Ya kuma soki wasu kasashe saboda shirunsu, ko ma goyon bayansu, game da ayyukan ta’addanci da Amurka da gwamnatin Isra’ila suka yi wa cibiyoyin nukiliyar Iran a watan Yuni.
“Duk da haka, Iran ta nuna kyakkyawan fata kuma ta ci gaba da hulda da IAEA game da cibiyoyin da ba a kai wa hari ba,” in ji shi.
Jami’in diflomasiyyar ya bayyana cewa bayan dawo da tsarin ne da ake kira snapback, Iran ta yi watsi da Yarjejeniyar Alkahira, wacce ta tanadi hulda da IAEA.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kwamitin tsaro zai kada kuri’a kan daftarin kudirin Trump kan Gaza November 17, 2025 Ansarullah Ta Yi Allah Wadai Da Sabunta Takunkumin MDD Kan Yemen November 17, 2025 Afirka ta Kudu na Binciken shigar wasu ‘yan gudun hijirar Falasdinu 153 cikin kasar November 17, 2025 Najeriya ba za ta buga kofin duniya ba karo na biyu a jere November 17, 2025 DRC: An Kulla Yarjejeniyar Zaman Lafiya A Tsakanin Gwamnati Da Kungiyar M23 November 16, 2025 An Yi Kira A Bai Wa ‘Yan Hijira Saboda Sauyin Muhalli Kariya November 16, 2025 An Amince Da Sauye-sauye A Tsarin Mulkin Kasar Benin November 16, 2025 Isra’ila Ta Kai Wa Sojojin MDD Hari A Kasar Lebanon November 16, 2025 Makiya Sun Kulla Makirci kan Kasar Labanon Irin Wanda Suka Kulla Kan Siriya November 16, 2025 Kasar Afghanistan Na Kokarin Karkata Akalar Kasuwancinta Zuwa Iran November 16, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Limamin Juma’a Ya Bukaci Ganin An Kai Karar Donald Trump A Kotunan Duniya
Wanda ya jagoranci sallar juma’a a Tehran Ayatullah Sayyid Ahmad Khatami ya yi kira ga jami’an diplomasiyyar kasar Iran da su kai karar shugaban kasar Amurka Donald Trump a kotunan kasa da kasa, bayan da ya yi furuci da cewa shi ne ya jagroanci harin da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta kawo wa Iran.
Ayatullah Sayyid Ahmad Khatami ya kuma kara da cewa, ya kamata a fitar da bayani na yin tir da wannan maganar sannan kuma a kai kara a cibiyoyin duniya.
Da ya koma yin Magana akan hijabi kuwa, limamin na Tehran ya bayyana cewa, sanya hijabi ga mata,hukunici ne da addini da kuma doka, sannan ya ambato wani marubuci dan Amurka da yake cewa: Idan har matan Iran su ka cire suturar hijibi to sun fada cikin tarkon makarkashiyar kungiyar leken asirin Amurka ( C.I.A) wacce ke nufin kifar da tsarin musulunci da rusa Iran.
Limamin ya kuma yi kira ga matan da su sake tunani akan kare addininu da kuma kasarsu, wadanda ba su sanya suturar hijabi su sauya tunani.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran ce ta farko wajen fitar da dabino a duniya November 14, 2025 Wasu kasashen duniya sun nuna damuwa game da tsarin mulkin bayan yakin Gaza November 14, 2025 Kwamitin Tsaro ya tsawaita wa’adin aikin tawagar MDD a Afrika ta Tsakiya November 14, 2025 Tehran da Ankara sun jaddada muhimmancin zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin November 14, 2025 Iran ta yi tir da G7 kan goyon bayan takunkuman Amurka November 14, 2025 Iran da China na bunkasa alakoki da hadin gwiwa a tsakaninsu November 14, 2025 Abdoulaye Diop: ‘Yan Tawaye Ba Za Su Iya Mamaye Dukkan Kasar Mali Ba November 14, 2025 Ramaphosa Ya Caccaki Trump Kan Kauracewa Taron G20 A Johannesburg November 14, 2025 MDD ta nuna damuwa game da rahotannin kisan gilla a El Fasher November 14, 2025 Rasha Ta yi Gargadin Mayar Da Martani Mai Tsanani Kan Amurka November 13, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci