Hamas Da Sauran Bangarorin Falasdinawa Sun yi Watsi Da Shirin Aikewa Da Dakarun Kasashen Waje A Yankin Gaza
Published: 17th, November 2025 GMT
Rahotanni sun bayyana cewa bangarorin falasdinawa sun yi watsi da kudurin da aka kaddamar ga kwamitin sulhu na majalsar dinkin duniya na shirin aikewa da sojojin ketare zuwa yankin Gaza sun yi kira ga kasar Aljeriya da sauran mambobin da ba na dindin ba a kwamitin sulhu da su kalubalance shi.
Daftarin kudurin an tsara za’a kada kuri’a akan shi a yau litinin na yiyuwar akewa da dakarun kasashen waje 20,000 domin kulawa da iyakokin Gaza, da kuma bada huro ga yan sandan falasdinu .
A Sanarwar hadin guiwar dukkan bangarorin falasdinawan sun yi tir da wannan shiri, inda suka bayyana shi a matsayin wani sabon salo na kara mamaye yankin dama alummarsa, domin bada halacci ga zaman dakarun kasashen waje a yankin.
Mai Magana da yawun kungiyar Hamas Hazem Qaseem ya jadda cewa amincewa da daftarin kudurin da Amurka ta gabatar ba zai kawo zaman lafiya da daidaito ba a yankin Gaza, don haka ya bukaci kwamitin tsaro da ya kare musu hakkokinsu da kuma hana afkuwar yaki a yankin
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Nukiliya : Iran zata sake duba huldarta da IAEA idan aka dauki wani sabon mataki kanta November 17, 2025 Kwamitin tsaro zai kada kuri’a kan daftarin kudirin Trump kan Gaza November 17, 2025 Ansarullah Ta Yi Allah Wadai Da Sabunta Takunkumin MDD Kan Yemen November 17, 2025 Afirka ta Kudu na Binciken shigar wasu ‘yan gudun hijirar Falasdinu 153 cikin kasar November 17, 2025 Najeriya ba za ta buga kofin duniya ba karo na biyu a jere November 17, 2025 DRC: An Kulla Yarjejeniyar Zaman Lafiya A Tsakanin Gwamnati Da Kungiyar M23 November 16, 2025 An Yi Kira A Bai Wa ‘Yan Hijira Saboda Sauyin Muhalli Kariya November 16, 2025 An Amince Da Sauye-sauye A Tsarin Mulkin Kasar Benin November 16, 2025 Isra’ila Ta Kai Wa Sojojin MDD Hari A Kasar Lebanon November 16, 2025 Makiya Sun Kulla Makirci kan Kasar Labanon Irin Wanda Suka Kulla Kan Siriya November 16, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Iran ta bukaci duniya ta gaggauta daukar mataki a Sudan
Iran ta bukaci kasashen duniya dasu gaggauta daukar mataki kan halin da ake ciki a Sudan musamman a yankin El Fasher don magance matsalar dake ta’azzara a arewacin Darfour.
Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya, Ali Bahraini, ne ya bayyanan hakan a jawabinsa yayin zaman musamman na 38 kan yanayin kare hakkin dan adam a yankin El Fasher da kewaye a yayin rikicin da ke ci gaba da faruwa a Sudan.
Mista Bahraini ya yi gargadi game da yunwa, yawan ‘yan gudun hijira da kuma tasirin tsoma bakin kasashen waje kan rikicin.
Wadanan matsalolin sun haifar da daya daga cikin rikicin jin kai mafi muni a duniya, wanda ke bukatar kulawa nan take daga kasashen duniya,” in ji jakadan.
Jami’in na Iran ya soki kasashen duniya kan “yin shiru” yayin da rikicin ke kara ta’azzara kuma ya nuna damuwa game da shigar kasashen waje cikin lamarin.
Shishigin kasashen waje, gami da samar da makamai da daukar sojojin haya, suna kara rura wutar ci gaba da rikice-rikicen da kuma karuwar ta’azarar rikicin jin kai,” in ji shi.
Bahrain ya yi kira ga dukkan kasashe da su dauki “matakai masu tsauri,” su kare fararen hula da kuma tallafawa kokarin da ake yi na samar da zaman lafiya da haɗin kai mai ɗorewa a Sudan.
Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce yakin ya yi sanadin mutuwar akalla mutane 40,000, kuma MDD ta ce wasu miliyan 12 sun rasa matsugunansu.
A zamansu na ranar Juma’a, manyan kungiyoyin kare hakkin bil’adama na MDD sun amince da wani kuduri da ya umarci tawagar bincike mai zaman kanta ta MDD kan Sudan da ta gaggauta binciki lamarin domin hukunci wadanda ke da laifi.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka EU ta bukaci Isra’ila ta dauki mataki don kawo karshen tashin hankali a Yammacin Kogin Jordan November 15, 2025 Amurka Ta Sanar Da Fara Kai Farmakin Soja Mai Sunan ” Mashin Kudu” Akan Yankin Latin November 14, 2025 Ana Samun Kwararar ‘Yan Hijira Daga Mali Zuwa Kasar Cote De Voire November 14, 2025 Unrwa: Fiye Da Gidaje 282,000 “Isra’ila” Ta Rusa A Gaza November 14, 2025 Limamin Juma’a Ya Bukaci Ganin An Kai Karar Donald Trump A Kotunan Duniya November 14, 2025 Iran ce ta farko wajen fitar da dabino a duniya November 14, 2025 Wasu kasashen duniya sun nuna damuwa game da tsarin mulkin bayan yakin Gaza November 14, 2025 Kwamitin Tsaro ya tsawaita wa’adin aikin tawagar MDD a Afrika ta Tsakiya November 14, 2025 Tehran da Ankara sun jaddada muhimmancin zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin November 14, 2025 Iran ta yi tir da G7 kan goyon bayan takunkuman Amurka November 14, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci