Tsaro: Na kan yi kuka duk lokacin da na ji an kashe wani — Akpabio
Published: 16th, November 2025 GMT
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya ce gwamnati ce ke da alhakin samar da tsaro da haɗin kai a Jihar Filato da kuma Najeriya baki ɗaya.
Ya ce babu wata ƙasa da za ta shigo don kawo zaman lafiya na dindindin a Najeriya, face ’yan ƙasa sun haɗa kai.
’Yan Bindiga A Kano: Sanusi II ya ziyarci Faruruwa, ya buƙaci a tsaurara tsaro Ba da yawuna PDP ta kori Wike ba — MuftwangAkpabio, ya yi wannan magana ne a filin Polo na Jos a ranar Asabar yayin taron tarbar sabbin mambobin da suka sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC a Jihar Filato.
Ya kira jama’a da su goyi bayan ƙoƙarin samar da zaman lafiya tare da yin aiki don ƙarshen rikice-rikece.
Ya ce Shugaba Bola Tinubu yana ƙoƙarin kawo ƙarshen kashe-kashe da tabbatar da zaman lafiya a Filato da sauran sassan ƙasar nan.
“Muna roƙon Allah Ya taimaka mana mu samu zaman lafiya a Filato. Duk wanda zai mulki Filato dole ne ya zama mutum mai kishin zaman lafiya. Wannan ita ce jam’iyyar da ta ke kula da ku,” in ji shi.
Akpabio, ya ƙara da cewa: “Na zo a madadin Shugaban Ƙasa domin tabbatar muku cewa za mu yi duk abin da ya kamata domin ku samu zaman lafiya.
“Babu wasu mutane daga waje da za su zo su kawo muku zaman lafiya. Dole mu ne za mu samar da shi. Dole mu zauna lafiya da juna. Najeriya na buƙatar zaman lafiya domin samun ci gaba.”
Ya tabbatar wa al’ummar Jihar Filato cewa gwamnati za ta magance matsalolin da suke fuskanta.
“Ina kuka a duk lokacin da na ji an kashe wani mutum; yaro ko babba. Matsalar da muke fuskanta ba yau ta samo asali ba.
“Mutane da dama sun mutu a Filato. An zubar da jini mai yawa, kuma ba mu farin ciki da haka. Shugaban Ƙasa ma ba ya farin ciki,” in ji shi.
Akpabio ya amince cewa da cewar ana kashe-kashe, tashe-tashen hankula a ƙasar nan, amma ya yi alƙawarin cewa nan da wani lokaci lamarin zai zama tarihi.
Ya roƙi al’ummar Filato da su goyi bayan Shugaba Tinubu da jam’iyyar APC, inda ya jaddada cewar za su samar da ci gaba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Tsaro zaman lafiya
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban APC Na Kano Ya Nemi Afuwa Daga Al’ummar Fagge Kan Kalamansa
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Da ɗumi-ɗuminsa Tsohon Gwamnan Anambra, Willie Obiano, Ya Rasu Yana Da Shekaru 70 November 14, 2025
Manyan Labarai Musulmin da Aka Kashe A Zamfara, Katsina Da Sokoto Sun Ninka Na Kiristoci A Tsakiyar Najeriya: MACBAN November 14, 2025
Manyan Labarai Kotu Ta Yanke Wa Mutum 4 Hukuncin Kisa Kan Kashe Wani Makanike A Kano November 14, 2025