Congo ta tsawaita haramcin fataucin ma’adinai a gabashin kasar
Published: 18th, November 2025 GMT
Ma’aikatar ma’adinai a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo ta sanar da tsawaita dokar hana fataucin ma’adinai na tsawon watanni shida daga wuraren hakar ma’adinai da dama a lardunan Kivu ta arewa da ta kudu da ke fama da rikici.
Sabunta haramcin zai kara kawo tsaiko da cikas wajen samar da wasu ma’adanai a duniya, musamman ma’adaanai irin su tin, tantalum, da tungsten, mahimman abubuwan da ake amfani da su wajen kera kayan lantarki, motoci, da wasu ayyuka na sararin samaniya.
Haramcin, wanda aka fara aiki da shi a watan Fabrairu, ya ci gaba da aiki na tsawon wannan lokaci, inda shaidun ke nuna cewa kayayyakin da ake amfani da su ba bisa ka’ida ba daga ma’adinan suna tallafawa kungiyoyin masu dauke da makamai a gabashin Congo, a cewar wani bayani mai kwanan wata 3 ga watan Nuwamba mai dauke da sa hannun ministan ma’adinai na kasar, Louis Watom Kampaba.
Bayanin ya kunshi shafuka 38 da ke nuni da cewa haramcin ya shafi abubuwa da dama daga ciki har da coltan, cassiterite, da wolframite, tin, tantalum, da tungsten.
Har ila yau kungiyar ‘yan tawayen M23 da sauran kungiyoyi masu dauke da makamai sun kwace filaye da dama a gabashin Kongo mai arzikin ma’adinai a cewar Ministan.
Matakin da ma’aikatar ma’adinai ta dauka ya haramta fitar da kayayyaki daga wuraren hakar ma’adinan da ake magana a kai, kuma ta ce za su iya fuskantar bincike mai zaman kansa daga ma’aikatar ko hukumomin kasa da kasa, ciki har da Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar hadin kan tattalin arziki da raya kasashen yankin gabashin nahiyar Afirka.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Rasha: An dakile wani yunkurin kisan gilla kan Sakataren Majalisar Tsaron kasa November 18, 2025 Aref: Iran Tana Da Kyakkyawar Alaka Da Mambobin Kungiyar Hadin Gwiwa Ta Shanghai {SCO} November 17, 2025 Na’ini: Jagora Ne Da Kansa Ya Jagoranci Lamurra A Lokacin Yakin Kwanaki 12 Da Aka Kaddamar Kan Iran November 17, 2025 Mahukuntan Gaza Sun Yi Gargadin Bullar Bala’in Jin Kai A Yankin Da Ba A Taba Ganin Irinsa Ba November 17, 2025 Sheikh Na’im: Gwamnatin Lebanon Zata Yi Babban Kuskure Matukar Tabi Hanyar Sassauci November 17, 2025 Rushewar Ramukan Hako Ma’adinai Ta Kashe Mutane 32 A Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango November 17, 2025 Alummar Kasar Ecodo Sun yi Watsi Da Batun Sake Dawo Da Sansanin Sojin Amurka A Kasar November 17, 2025 Sojojin HKi Sun Kashe Wasu Falasdinawa Guda 2 A Sansanin Yan Gudun Hijira November 17, 2025 Tawagar Wasan Wushu Ta Kasar Iran Ta Samu Lambobin Yabo 4 A Saudiya November 17, 2025 Shugaban Nukiliyar Iran Yace Amurka Da Israila Sun Shiga Sabon Mataki Mai Hadari November 17, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban kasar venuzuwela Yayi Tir Da Atisayan Soji Da Trinidad and Tobago Ke yi.
Shugaban kasar venuzuwela Nicolas Maduro yayi suka game da atisayan soji da Trinidad an Tobago ke yi, kuma ya bayyana shi a matsayin abin da bai dace ba kuma yana barazana ga zaman lafiyar yankin Caribbean.
Atisayan sojin yana kara tada hankali tsakanin kasar venuzuwela da daya daga cikin makwabciyarta ta kurkusa adaidai lokacin da ayyukan sojojin Amurka a yankin karebiya ya jefa yanki cikin zaman dar-dar.
Kasar Trinidad and Tobago ta tsara fara gudanar da atisayin soji na hadin guiwa a cikin ruwan dake kusa da kasar venuzuwela daga ranar 17 zuwa 20 ga watan nuwamba, atisayan yazo daidai da ayyukan tsaro da Amurka ke jagoranta a yankin karebiya wandaAamurka tace ya shafi yaki da masu safarar miyagun kwayoyi ne.
Sai dai maduro ya bayyana rashin amicewarsa da daukarsa a matsayin wasu dabarun ne na boye, na gurgunta gwamnatinsa.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka IRGC ta kama wani jirgin ruwan dakon mai a gabar tekun kudancin Makran November 16, 2025 Iran : sojojin Amurka a yankin Caribbean barazana ne ga zaman lafiya November 16, 2025 Lebanon za ta kai karar Isra’ila a MDD kan gina Katanga a iyakarta November 16, 2025 AU ta sake watsi da ikirarin Trump cewa ana kashe Kiristoci a Najeriya November 16, 2025 Falasdinu ta yi wasan sada zumunci a Spain November 16, 2025 Amurka Ta Yi Gwajin Makaman Nukiliya A Watan Ogusta November 15, 2025 Adadin Ma’adanin “Colbat” Da DRC Ta Bai Wa Duniya Ya Kai Ton 1,000 November 15, 2025 Ma’ariv: Netanyahu Yana Tsoron Hukuncin Da Kotu Za Ta Yanke Akansa November 15, 2025 An Bayyana Sunayen Kasashen Da Su Ka Fi Sayar Wa “Isra’ila” Man Fetur A Lokacin Yakin Gaza November 15, 2025 MDD: Mutane 100,000 Ne Su Ka Fice Daga Birnin Al-Fasher Na Kasar Sudan November 15, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci