HausaTv:
2025-11-16@19:52:36 GMT

 An Amince Da  Sauye-sauye A Tsarin Mulkin Kasar Benin

Published: 16th, November 2025 GMT

Kasar Benin ta amince da sabon tsarin Mulki da ya amince da  sabbin sauye-sauye a tsarin Mulki wanda ya kunshi kafa majalisar dattijai da kuma tsawaita wa’adin shugabancin kasa da na ‘yan majalisu.

Sabon wa’adin da ‘yan majalisar dokokin kasar su ka amince da shi, shi ne shekaru bakwai, bayan da ya kasance shekaru biyar.

Sai a shekara mai zuwa ta 2026 ne dai sabbin sauye-sauyen da aka yi za su fara aiki.

Sai dai shugaban kasar da yake ci a yanzu Patrice Talon ba zai ci moriyar wannan sauyin ba saboda watanni bakwai su ka rage masa wa’adinsa na biyu yak are.

 A karkashin sauye-sauyen da aka yi, an kirkiro majalisar dattijai da za ta kasance da mambobi 25 zuwa 30. Kuma wadanda za a zaba su zama wakilai a wannan majalisar ta dattijai su ne masu kwarewa a fagen siyasa, tsaro, tsofaffin shugabannin kasashe, tsoffin ‘yan majalisar dokoki, alkalai da kuma jami’an soja.

Daga cikin aikin da majalisar dattijan za ta yi da akwai karfafa hadin kan kasa, demokradiyya da zaman lafiya. Har ila yau Majalisar za ta rika yin bita ta biyu ta duk wata doka da majalisar dokoki za ta amince da ita,musamman wadanda su ka shafi harkokin kudi.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Isra’ila Ta Kai Wa Sojojin MDD Hari A Kasar Lebanon November 16, 2025 Makiya Sun Kulla Makirci kan Kasar Labanon Irin Wanda Suka Kulla Kan Siriya November 16, 2025  Kasar Afghanistan Na Kokarin Karkata Akalar Kasuwancinta Zuwa Iran November 16, 2025 Kanada Ta Tsare Tsohon Wakilin Majalisar Dinkin Duniya Mai Bincike Kan Laifukan Yakin Israila.   November 16, 2025  Zarfi: HKI Ce Kawai Take Ayyana Nukiliya Ba Bisa Kaida Ba A Yammacin Asiya. November 16, 2025 Shugaban kasar venuzuwela Yayi Tir Da Atisayan Soji Da Trinidad and Tobago Ke yi. November 16, 2025 IRGC ta kama wani jirgin ruwan dakon mai a gabar tekun kudancin Makran November 16, 2025 Iran : sojojin Amurka a yankin Caribbean barazana ne ga zaman lafiya  November 16, 2025 Lebanon za ta kai karar Isra’ila a MDD kan gina Katanga a iyakarta November 16, 2025 AU ta sake watsi da ikirarin Trump cewa ana kashe Kiristoci a Najeriya November 16, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

AU da MDD, sun karfafa dabarun tabbatar da zaman lafiya da tsaro

Kungiyar tarayyar Afrika da Majalisar Dinkin Duniya sun karfafa kawancensu kan dabarun tabbatar da zaman lafiya, tsaro da kuma ci gaba don magance kalubalen duniya da na yanki yanki.

“Hadin gwiwa tsakanin kungiyoyinmu bai taba kasancewa mafi karfi da muhimmanci fiye da yadda yake a yau ba,” in ji Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya António Guterres.

Wannan sanarwar ta zo ne a karshen taron hadin gwiwa na shekara-shekara na 9 na Tarayyar Afirka da Majalisar Dinkin Duniya, wanda aka gudanar a hedkwatar Majalisar Dinkin Duniya da ke New York a ranar Alhamis, wanda Shugaban Hukumar Tarayyar Afirka, Mahamoud Ali Youssouf, da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya António Guterres suka jagoranta.

Guterres ya jaddada cewa duniya a halin yanzu tana fuskantar “rikici, tashin hankali, karuwar rashin daidaito, wadannan tasirinsu ake ganinshu sosai a nahiyar Afirka.”

Jami’an biyu sun jaddada cewa hadin gwiwa tsakanin AU da Majalisar Dinkin Duniya muhimmin ginshiki ne na kokarin kasa da kasa na inganta zaman lafiya da kare hakkin dan adam.

Sun nuna damuwa game da yaduwar rikice-rikicen jin kai da ke shafar yankuna da dama.

Babban Sakataren ya bayyana “damuwarsa mai zurfi” game da rahotannin baya-bayan nan na “kisan kiyashi da keta hakkokin dan adam” a Al-Fashir da kuma karuwar tashin hankali a yankin Kordofan na Sudan, tare da gargadi game da karuwar rashin tsaro a yankin Sahel ciki har da Mali, Sudan ta Kudu, Somaliya, Libya, da Jamhuriyar Demokraɗiyyar Kongo.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran ta bukaci duniya ta gaggauta daukar mataki a Sudan November 15, 2025 EU ta bukaci Isra’ila ta dauki mataki don kawo karshen tashin hankali a Yammacin Kogin Jordan November 15, 2025  Amurka Ta Sanar Da Fara Kai Farmakin Soja Mai Sunan ” Mashin Kudu” Akan Yankin Latin November 14, 2025 Ana Samun Kwararar ‘Yan Hijira Daga Mali Zuwa Kasar Cote De Voire November 14, 2025  Unrwa: Fiye Da Gidaje 282,000 “Isra’ila” Ta Rusa A Gaza November 14, 2025 Limamin Juma’a Ya Bukaci Ganin An Kai Karar Donald Trump A Kotunan Duniya November 14, 2025 Iran ce ta farko wajen fitar da dabino a duniya November 14, 2025 Wasu kasashen duniya sun nuna damuwa game da tsarin mulkin bayan yakin Gaza November 14, 2025 Kwamitin Tsaro ya tsawaita wa’adin aikin tawagar MDD a Afrika ta Tsakiya November 14, 2025 Tehran da Ankara sun jaddada muhimmancin zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin November 14, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Makiya Sun Kulla Makirci kan Kasar Labanon Irin Wanda Suka Kulla Kan Siriya
  •  Kasar Afghanistan Na Kokarin Karkata Akalar Kasuwancinta Zuwa Iran
  • Kanada Ta Tsare Tsohon Wakilin Majalisar Dinkin Duniya Mai Bincike Kan Laifukan Yakin Israila.  
  • Shugaban kasar venuzuwela Yayi Tir Da Atisayan Soji Da Trinidad and Tobago Ke yi.
  • Jakadan Iran A Majalisar Dinkin Duniya Yace Iran Ba za Ta Taba Mika Wuya Ga Duk Wata Barazana Ba
  • AU da MDD, sun karfafa dabarun tabbatar da zaman lafiya da tsaro
  • Ana Samun Kwararar ‘Yan Hijira Daga Mali Zuwa Kasar Cote De Voire
  • Wasu kasashen duniya sun nuna damuwa game da tsarin mulkin bayan yakin Gaza
  • Majalisar Wakilai ta dage lokacin fara yin jarabawar WAEC a kwamfuta zuwa 2030