GGCSS Maga: Halin da iyaye ke ciki bayan sace ’ya’yansu
Published: 18th, November 2025 GMT
Iyayen ɗalibai ’yan mata 25 ’yan bindiga sace ɗakunan kwanansu a Jihar Kebbi sun bayyana irin tashin hankali da suka shiga bayan abin da ya faru.
“Ita kaɗai gare ni,” in ji Malam Muhammad Maga, mahaifin Nafisa, wadda ita kadai ya haifa, kuma take cikin ɗaliban da ’yan bindiga suka sace a makarantar.
Malam Muhammad wanda idanunsa ke cike da ƙwalla ya ce, “Roƙona Allah Ya sa a dawo min da ita lafiya, ita kaɗai gare ni.
Shi ma Malam Aliyu Yakubu, ɗaya daga cikin iyayen ɗaliban da aka sace, ya ce, “’Yata na cikin ɗaliban da aka sace daga ɗakin kwanansu a safiyar Litinin, gaskiya ni da sauran iyaye muna cikin tashin hankali.
Za mu ceto ’Yan Matan GGCSS Maga cikin ƙoshin lafiya — Gwamnan Kebbi Sace Ɗalibai: Gwamnatin Tinubu ba ta shirya kawo ƙarshen ta’addancin ’yan bindiga ba — Amnesty Mayaƙan ISWAP sun kashe kwamandan soji a Borno“Babban abin da nake tsoro shi ne kada abin ya zama irin na Makarantar ’Yan Mata ta Gwamantin Tarayya ta Birnin Yauri, inda yaran da aka sace suka shafe sama da shekara biyu a hannun ’yan bindiga
Muna rokon Gwamnatin Jihar Kebbi da Gwamnatin Tarayya su yi duk mai yiwuwa su ceto mana ’ya’yan mu”
Aminiya ta ruwaito cewar da asubahin ranar Litinin ne ’yan bindiga suka yi ta harbe-harbe a iska sa’annan suka kutsa cikin Makarantar sakandaren ’Yan Matan Gwamnati ta Musamman (GGCSS) da ke garin Maga a Ƙaramar Hukumar Danko Wasagu a Jihar Kebbi, suka yi abin gaba da ɗalibai 25.
’Yan bindigar sun ci karensu babu babbaka, ba tare da wani ƙalubale ba, in banda Mataimakin Shugaban Makarantar, Malam Hassan Yakubu Makuku, wanda ya yi ƙoƙarin hana su tafiya da ɗaliban, amma suka harba shi har lahira, suka yi abin gaba da yaran.
Makarantar GGCSS Maga ta kasance a rufe na kimanin shekaru biyar saboda tsaron irin garin GGSS Birnin Tauri a zamanin gwamnatin da ta gabata ta Abubakar Atiku Bagusu, sai ’yan shekarun baya aka buɗe ta, inda aka girke jami’an tsaro.
Wani mahaifi da ’yarsa A’isha take cikin ɗaliban da aka sace, ya ce, wani mazaunin garin ne ya fara sanar da shi cewa A’isha tana cikin yaran da aka sace, “Amma ban gaskata ba, sai da na zo makarantar na iske iyaye na ta koke-koke. Roƙona ga gwamnati shi ne ta taimaka ta ceto maka ’ya’yanmu.”
Kawai Altine, wanda shi ma ’yan bindiga sun sace ’yarsam ya ce, “Na miƙa komai ga Allah, kuma na yi imanin cewa Allah Zai dawo mana da ita nan ba da jimawa ba. Roƙona kawo shi ne gwamnati da jami’an tsaro kada su yi ƙasa a gwiwa, wajen bi sawu domin gano yaran namu.”
Wani shugaban al’umma a yankin, Malam Rabi’u Abubakar, ya ce harin ya girgiz al’ummar yankin, musamman iyayen ɗalibai.
Ya ce, “Muna da dalilin yin baƙin ciki, saboda sun tafi mana da ’ya’ya, kuma suka kashe mana Malam Yakubu Makuku, saboda ya nemi kada su ɗauki yaran. Haƙiƙa wannan babban rashi ne.”
Kakakin Gwamnan Jihar Kebbi, Abdullahi Idris Zuru, ya shaida wa Aminiya cewa an turo ƙarin jami’an tsaro daga Abuja zuwa jihar domin su taimaka a aikin da ake yi na nema da kuma ceto ɗaliban.
Tun da farko Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kebbi ta tabbatar da harin, tare da sanar da cewa tuni jami’an tsaro da mafarauta suka fara aikin ceto ɗaliban.
Aminiya ta ruwaito cewa Gwamna Jihar Kebbi, wanda labarin harin ya sa shi gaggawar yanke ziyarar aiki da ya kai Abuja, ya yi wata ganawa da iyayen ɗaliban, inda ya ba su tabbacin yin duk mai yiwuwa tare da jami’an tsaro domin kuɓutar da yaran.
Karo na biyu ke nan da ’yan bindiga suka kutsa cikin makarantar kwana ta ’yan a Jihar Kebbi suka yi garkuwa da gomman dalibai — na farko shi ne a Makarantar ’Yan Mata ta Gwamantin Tarayya da ke Birnin Yauri.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga yan mata ɗakin kwana Ɗalibai Garkuwa iyaye jami an tsaro a Jihar Kebbi yan bindiga ɗaliban da
এছাড়াও পড়ুন:
NELFUND ya raba wa ɗalibai tallafin karatu na Naira Biliyan 116
Asusun Lamunin Ilimi na Najeriya (NELFUND) ya bayyana cewa ya raba jimillar kuɗi Naira biliyan 116 domin tallafa wa dalibai a faɗin ƙasar nan wajen biyan kuɗin makaranta da kuma kula da rayuwarsu ta yau da kullum.
Shugaban NELFUND, Akintunde Sawyerr ya bayyana a Abuja cewa, daga cikin kuɗin, an tura Naira biliyan 65 aka tura kai tsaye zuwa makarantu 239 na tarayya — jami’o’i, kwalejojin fasaha da kwalejojin ilimi — domin biyan kuɗin makarantar ɗaliban da aka amince da buƙatar lamuninsu.
Sauran Naira biliyan 51 kuma an tura ne kai tsaye ga ɗaliban a matsayin tallafin kula da rayuwa na wata-wata.
Ya ce: “Mun raba Naira biliyan 65 ga makarantu da kuma Naira biliyan 51 ga ɗaliban domin tallafin rayuwa. Jimillar kuɗin da aka fitar ya kai Naira biliyan 116.”
Sawyer ya ce har zuwa yanzu NELFUND biya dalibai 624,000 da suka riga suka fara karɓar kuɗin makaranta da tallafin rayuwa.
Shugaban NELFUND ya bayyana shirin a matsayin ɗaya daga cikin manyan shirye-shiryen saka jari na zamantakewa da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta aiwatar.
Ya ce manufar shirin ita ce kawar da matsalolin kuɗi da ke hana ɗalibai ci gaba da karatu, tare da tabbatar da cewa babu ɗan Najeriya da zai bar makaranta saboda rashin kuɗi.
Sawyer ya tabbatar da cewa NELFUND za ta ci gaba da gudanar da shirin cikin gaskiya da inganci, musamman ganin yadda yawan ɗaliban da ke amfana yake ƙaruwa a kullum.