United za ta yi wasanni 6 a jere babu Benjamin Sesko
Published: 19th, November 2025 GMT
Dan wasan gaban Manchester United, Benjamin Sesko zai yi jinyar makonni huɗu, lamarin da zai hana shi buga wa ƙungiyar wasanni shida a jere.
Šeško mai shekaru 22, ba zai samu damar taka leda ba a wasan da United za ta karɓi baƙuncin Everton a Old Trafford mako mai zuwa.
Gwamnan Taraba ya dakatar da ficewa daga PDP saboda sace ɗalibai a Kebbi Mutane 7 sun mutu a hatsarin mota a JigawaHaka kuma ba zai haska ba a sauran wasannin da za su biyo baya da Crystal Palace, West Ham, Wolves, Bournemouth da kuma Aston Villa.
Ana sa ran dan wasan na ƙasar Slovenia zai dawo cikin ƙungiya ne a lokacin da Manchester United za ta karɓi baƙuncin Newcastle United a gida.
Sesko ya ji raunin ne a wasan da Manchester United ta tashi 2–2 da Tottenham a ranar 18 ga Oktoba, 2025.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Ansarullah Ta Yi Allah Wadai Da Sabunta Takunkumin MDD Kan Yemen
Kungiyar Ansarullah a Yemen ta yi Allah wadai da sabunta takunkumin Majalisar Dinkin Duniya Kan kasar tare da dake tabbatar da goyon bayanta ga Falasdinu.
Kungiyar ta yi tir da matakin da Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya Ya Dauka Na sabunta takunkumin Kan Yemen na wata Shekara, ta kuma yi Allah Wadai da son zuciyar kasashen Yamma.
A cikin wani sako a shafin X, Mohammed al-Farah, wani babban jami’i a ofishin siyasa na Ansarullah, ya jaddada kudurin Sana’a na mayar da martani ga duk wanda ya yi yunkurin kai hari ga muradun al’ummar Yemen.
Ya kara da cewa ‘yan Yemen ba za su yi wata-wata ba don kare hakkokinsu, addininsu, da mutuncin kasa, ta kowace hanya da ta dace.
Al-Farah ya kuma kira shawarar da Majalisar Dinkin Duniya ta yanke da “mafi muni a karo na biyu,” yana mai kokawa da cewa hukumar ta yi biris da kisan kiyashin Falasdinawa a Gaza yayin da take goyon bayan gwamnatin Isra’ila a laifukan da take aikatawa da kuma yin watsi da da cin zarafin da take yi wa Yemen.
Babban jami’in ya bayyana Majalisar a matsayin wani dandali da ke biyan muradun Yamma da kuma kare muradun Amurka.
A wani bangare na jawabinsa, ya yaba wa Rasha da China saboda kin sabunta takunkumi kan Yemen, da kuma fahimtar hadarin manufofin Amurka wadda ke amfani da takunkumi ga kasashe masu iko.
Al-Farah ya kuma soki kasashen yamma da Amurka saboda goyon bayansu na soja, kudi, da siyasa ga Isra’ila, yana mai jayayya cewa takunkumin da aka sabunta wa Yemen don biyan bukatun ‘yan Sahayona ne da kuma hukunta al’ummar Yemen saboda juriyarsu, da kuma goyan bayan Gaza.”
Ya kuma sake jaddada goyon bayan Yemen ga Gaza da al’ummomin da ake zalunta a duk fadin yankin, tare da shan alwashin ci gaba da kalubalantar zalincin kasashen Yammacin duniya da Amurka a kan kasashe da al’ummomin yankin.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Afirka ta Kudu na Binciken shigar wasu ‘yan gudun hijirar Falasdinu 153 cikin kasar November 17, 2025 Najeriya ba za ta buga kofin duniya ba karo na biyu a jere November 17, 2025 DRC: An Kulla Yarjejeniyar Zaman Lafiya A Tsakanin Gwamnati Da Kungiyar M23 November 16, 2025 An Yi Kira A Bai Wa ‘Yan Hijira Saboda Sauyin Muhalli Kariya November 16, 2025 An Amince Da Sauye-sauye A Tsarin Mulkin Kasar Benin November 16, 2025 Isra’ila Ta Kai Wa Sojojin MDD Hari A Kasar Lebanon November 16, 2025 Makiya Sun Kulla Makirci kan Kasar Labanon Irin Wanda Suka Kulla Kan Siriya November 16, 2025 Kasar Afghanistan Na Kokarin Karkata Akalar Kasuwancinta Zuwa Iran November 16, 2025 Kanada Ta Tsare Tsohon Wakilin Majalisar Dinkin Duniya Mai Bincike Kan Laifukan Yakin Israila. November 16, 2025 Zarfi: HKI Ce Kawai Take Ayyana Nukiliya Ba Bisa Kaida Ba A Yammacin Asiya. November 16, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci