Aminiya:
2025-11-19@07:00:02 GMT

DAGA LARABA: Hanyoyin Da Suka Kamata A Bi Wajen Ceto Daliban Kebbi Da Aka Sace

Published: 19th, November 2025 GMT

More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba

Batun kubutar da ɗalibai mata da masu garkuwa da mutane suka sace na makarantar GGCSS Maga dake karamar hukumar Danko Wasagu a jihar Kebbi na daya daga cikin abubuwan da alumma suka maida hankali a kai.

 

Iyayen wadannan yara, da sauran masu ruwa da tsaki na ganin ya kamata a yi dukkan mai yiwuwa don ganin an ceto wadannan yara ba tare da sun samu rauni ba.

NAJERIYA A YAU: Matsayar Doka Kan Taron Da Jam’iyyar PDP Ta Gudanar DAGA LARABA: Tasirin Da Tura Jami’an ‘Yan Sanda Kare Manyan Mutane Zai Haifar Ga Tsaron Al’umma

Wannan shine batun da shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari a kai.

Domin sauke shirin, latsa nan

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Danko Wasagu

এছাড়াও পড়ুন:

Sace Ɗalibai: Gwamnatin Tinubu ba ta shirya kawo ƙarshen ta’addancin ’yan bindiga ba — Amnesty

Ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Amnesty International ta yi kakkausar suka kan sabon harin da ’yan bindiga suka kai makarantar sakandare ta ’yan mata da ke garin Maga a Jihar Kebbi, wanda ya kai ga sace ɗalibai mata sama da 25 tare da halaka mai gadi da mataimakin shugaban makarantar.

A wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin, Amnesty ta bayyana lamarin a matsayin abin takaici da kuma nuna gazawar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu wajen kare rayuka da dukiyoyin ’yan kasa ballantana kawo ƙarshen ta’addancin ’yan bindiga.

CAF ta fitar da ’yan wasa uku da suka rage a takarar gwarzon Afirka na bana Gobara ta laƙume rayukan yara biyu ’yan gida ɗaya a Ribas

Ƙungiyar ta ce bincikenta ya gano cewar ’yan bindigar sun kai hari ne da misalin ƙarfe 5 na safiya, inda suka tilasta wani ma’aikacin makarantar ya nuna musu ɗakin kwanan daliban mata, sannan suka yi awon gaba da su.

Amnesty ta ce wannan harin ya sake nuna cewa, “gwamnatin Tinubu ba ta da wani ingantaccen tsari na kawo ƙarshen ta’addancin ’yan bindiga, duk da matakan da ake ce an ɗauka, domin babu wani gagarumin sauyi da aka gani a ƙasa.”

Ƙungiyar ta buƙaci gwamnati da hukumomin tsaro su ɗauki matakan gaggawa domin ceto ɗaliban cikin aminci, tare da gano musabbabin yawaitar sace-sacen mutane a sassan ƙasar, abin da ta ce yana barazana ga ilimi da zaman lafiyar al’umma.

Gwamnatin Najeriya ta yi Allah wadai da sace ɗaliban

A nata ɓangaren, gwamnatin Najeriya ta bayyana tsananin damuwa kan harin, inda ta ce ta bai wa jami’an tsaro umarnin gano da ceto ɗaliban cikin gaggawa.

Cikin wata sanarwa da Ministan Yaɗa Labarai, Muhammad Idris ya fitar, ya ce gwamnati za ta tabbata an kamo waɗanda suka kai harin domin su fuskanci hukunci.

Ya ƙara da cewa gwamnati na tare da iyaye da ’yan uwan waɗanda abin ya shafa, tare da jaddada cewa za a yi duk wani abu mai yiyuwa domin ganin yaran sun koma gida cikin aminci.

Za mu dawo da duk ɗaliban da aka sace —Jami’an Tsaro

Wata rundunar haɗin gwiwa ta jami’an tsaro da suka haɗa da sojoji da ’yan sanda, na ci gaba da laluben ɗaliban bayan ’yan bindiga sun awon gaba da su.

Da sanyin safiyar Litinin, 17 ga watan Nuwambar 2025, mahara suka shiga a makarantar ’yan matan, inda bayanai ke nuni da cewa an sace ɗalibai 25 tare da halaka mataimakin shugaban makarantar da wani maigadi kana suka jikkatar da dama.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnan Taraba ya dakatar da ficewa daga PDP saboda sace ɗalibai a Kebbi
  • Dole ku ceto daliban da aka sace a Kebbi Shugaban Sojoji
  • GGCSS Maga: Halin da iyaye ke ciki bayan sace ’ya’yansu
  • Za mu ceto ’Yan Matan GGCSS Maga cikin ƙoshin lafiya — Gwamnan Kebbi
  • Sace Ɗalibai: Gwamnatin Tinubu ba ta shirya kawo ƙarshen ta’addancin ’yan bindiga ba — Amnesty
  • Gobara ta laƙume rayukan yara biyu ’yan gida ɗaya a Ribas
  • Rashin Tsaro: Atiku Ya Yi Allah-wadai Da Harin Makarantar ‘Yan Mata Ta Kebbi
  • Ƴan Bindiga Sun Sace Ɗalibai Ƴan Mata, Sun Kashe Mataimakin Shugaban Makaranta A Kebbi
  • A Zamanantar Da Tsarin Karatu A Makarantun Koyar Da Ilimin Addinin Musulunci – ECOWAS