Aminiya:
2025-11-19@08:02:42 GMT

Gobara ta laƙume kasuwar Katako a Gombe

Published: 19th, November 2025 GMT

Wata mummunar gobara ta tashi cikin daren Laraba ta ƙone shaguna a kasuwar Katako da ke Gombe, lamarin da ya yi sanadin salwantar dukiya ta miliyoyin naira.

Shaidu sun ce gobarar ta fara ne wajen misalin ƙarfe 1:00 na dare sakamakon zargin matsalar wutar lantarki, inda ake kyautata zato cewa an bar wasu na’urorin lantarki ne a kunne bayan an rufe kasuwar.

DAGA LARABA: Hanyoyin Da Suka Kamata A Bi Wajen Ceto Daliban Kebbi Da Aka Sace Amurka za ta binciki zargin yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Nijeriya ranar Alhamis

Hakan a cewar shaidun ya haddasa tashin gobarar bayan wutar lantarki ta dawo.

Gobarar dai ta ci gaba da ƙone shaguna da kadarori iri-iri, lamarin da ya jefa ’yan kasuwa cikin damuwa da alhini.

Kasuwar Katako na daga cikin manyan cibiyoyin hada-hadar kasuwanci a jihar wacce jigo ce wajen samar wa dubban mazauna Gombe kudaden shiga.

Jami’an hukumar kashe gobara sun shiga aikin ceto da wuri domin dakile bazuwar wutar, sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, ba a tantance adadin shagunan da suka ƙone ko jimillar asarar da aka yi ba.

Muna tafe da karin bayani…

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Gobara

এছাড়াও পড়ুন:

Amurka za ta binciki zargin yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Nijeriya ranar Alhamis

A ranar Alhamis, 20 ga watan Nuwamban 2025, ake sa ran Majalisar Wakilan Amurka za ta gudanar da zama na musamman domin bincikar zargin yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Nijeriya.

Kwamitin Majalisar Wakilan kan Afirka ya sanya ranar domin bitar fasalin da Shugaba Donald Trump ya yi kwanan nan na sanya Nijeriya a matsayin kasar da ake sa wa ido na musamman, CPC, kan zargin cewa ana yi wa Kiristoci kisan kiyashi.

Gwamnan Taraba ya dakatar da ficewa daga PDP saboda sace ɗalibai a Kebbi Gwamnonin Arewa sun yi Allah-wadai da sace ɗalibai mata a Kebbi

Gidan Talabijin na Channels ya ruwaito cewa, an gayyaci mambobin Kwamitin Harkokin Waje na majalisar, wanda aka shirya za a yi tattaunawar da misalin ƙarfe 11:00 na safe a Ɗaki mai lamba 2172 na Ginin Ofishin Gidan Rayburn, sannan kuma za a iya kalla ta intanet kai-tsaye, wanda wakili Chris Smith (R-NJ) ne zai jagoranta.

Za a gabatar da kwamitoci biyu na shaidu, ciki har da manyan jami’an Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka da shugabannin addinai na Nijeriya.

Gayyatar tana cewa, “Ana roƙonku da girmamawa da ku halarci zaman sauraron ƙararraki na Kwamitin Harkokin Waje da ƙaramin kwamiti kan Afirka zai gudanar da shi da ƙarfe 11:00 na safe a ɗaki mai lamba 2172 na ginin Ofishin Rayburn House.”

Trump ne ya fara sanya Nijeriya a matsayin kasae da ake sa wa ido na musamman, CPC a shekarar 2020, kafin magajinsa, Shugaba Joe Biden, ya cire ƙasar daga jerin sunayen bayan ya kayar da Trump.

Masu sauraron za su haɗa da Babban Jami’in Ofishin Harkokin Afirka, Jonathan Pratt, da Mataimakin Mataimakin Sakatare na Ofishin Dimokuradiyya, ’Yancin Dan’Adam, da Aiki, Jacob McGee.

Za a yi zaman tattaunawa ta biyu da Daraktan Cibiyar ’Yancin Addini, Ms Nina Shea; Bishop Wilfred Anagbe na Makurdi Catholic Diocese a Nijeriya; da Ms Oge Onubogu ta Cibiyar Dabaru da Nazarin Ƙasashen Duniya.

Ana sa ran zaman tattaunawa ta majalisar zai sake duba girman zargin cuzguna wa masu wani addini a Nijeriya.

Za a kuma yi nazarin irin martanin manufofi da za a iya ɗauka, ciki har da takunkumin da aka yi niyyar ƙaƙabawa da taimakon jinƙai, da haɗin gwiwa da hukumomin Nijeriya don hana ƙarin tashin hankali.

Za a kuma gabatar da ƙudirin a gaban Majalisar Dattawan Amurka, wanda Sanata Ted Cruz ya ɗauki nauyinsa.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Amurka za ta binciki zargin yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Nijeriya ranar Alhamis
  • GGCSS Maga: Halin da iyaye ke ciki bayan sace ’ya’yansu
  • Ana Zargin ’Yan Ta’adda Sun Kashe Janar Ɗin Soji A Harin Kwanton-Ɓauna A Borno
  • Za mu ceto ’Yan Matan GGCSS Maga cikin ƙoshin lafiya — Gwamnan Kebbi
  • Gobara ta laƙume rayukan yara biyu ’yan gida ɗaya a Ribas
  • ’Yan sanda sun kama ƙunshi 66 na Tabar Wiwi a Gombe
  • ’Yan sanda sun kama ƙunshe 66 na Tabar Wiwi a Gombe
  • Gwamnatin Gombe ta bai wa alƙalai da Khadi-Khadi kyautar sabbin motoci 16
  • Hukumar DSS Ta Kama Wani Kan Zargin Ƙerawa Da Rarraba Makamai A Filato