An ɗaura auren Sanata Kawu Sumaila da wata jami’ar soji a Kano
Published: 17th, November 2025 GMT
An ɗaura auren Sanatan Kano ta Kudu, Abdulrahman Kawu Sumaila, da Aisha Isah, wata jami’ar soji a Rundunar Sojin Sama ta Najeriya, a wani ɗan ƙwarya-ƙwaryan biki da aka gudanar sali-alin a Rano.
Ɗaurin auren wanda jama’a kaɗan ne suka halarta ya gudana ne da safiyar Litinin ɗin nan a fadar Sarkin Rano da ke Jihar Kano, lamarin da ya nuna cewa ba a yi wata sanarwa ta musamman ba kafin bikin.
Mai taimaka wa sanatan kan harkokin yaɗa labarai, Muttaqa Babire, ya tabbatar da auren a shafinsa na Facebook, inda ya wallafa hoton sanatan tare da amaryar cikin kayanta na jami’an soji.
Shi ma wani na hadiminsa, Ahmad Tijjani Kiru, ya wallafa a shafin Facebook cewa: “Alhamdulillah, yau 17-11-2025, an ɗaura auren Sanata S.A. Kawu Sumaila OFR, PhD a Rano. Allah Ya albarkaci rayuwar auren Ya kawo zuri’a ɗayyiba.”
Kawu Sumaila, wanda shi ne shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Albarkatun Mai, a bayan nan ne ya sauya sheƙa daga jam’iyyar NNPP zuwa APC.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Rano Sanata Kawu Sumaila Kawu Sumaila
এছাড়াও পড়ুন:
Fasinjojin Da Kasar Sin Ta Yi Jigilarsu Ta Jirgin Kasa Daga Janairu Zuwa Oktoba Sun Kai Biliyan 3.95
Fasinjojin Da Kasar Sin Ta Yi Jigilarsu Ta Jirgin Kasa Daga Janairu Zuwa Oktoba Sun Kai Biliyan 3.95
An ba da labari cewa, yawan fasinjojin da aka yi jigilarsu ta jirgin kasa daga watan Janairu zuwa Oktoba na wannan shekara a kasar Sin ya kai biliyan 3.95, wanda ya karu da 6.4% idan aka kwatanta da na shekarar da ta gabata.
Bayanai masu alaka da hakan sun nuna cewa, a farkon watannin goma na wannan shekara, adadin fasinjoji da jiragen kasa na Sin suka yi jigilarsu ya kai matsayi mafi girma a tarihi a wannan lokaci, kuma a ranar 1 ga Oktoba kawai, yawan fasinjojin ya kai fiye da miliyan 23.13, wanda ya kai matsayi mafi girma a tarihi a rana daya a wannan bangare.(Amina Xu)
ADVERTISEMENT ShareTweetSendShare MASU ALAKA