Leadership News Hausa:
2025-11-16@16:10:35 GMT

Hukumar DSS Ta Kama Wani Kan Zargin Ƙerawa Da Rarraba Makamai A Filato

Published: 16th, November 2025 GMT

Hukumar DSS Ta Kama Wani Kan Zargin Ƙerawa Da Rarraba Makamai A Filato

 

“An kama Abubakar da hannu dumu-dumu da wasu abubuwan fashewa, sinadarai, da kayan aiki, waɗanda jami’an DSS suka kwace,” in ji majiyar.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai A Zamanantar Da Tsarin Karatu A Makarantun Koyar Da Ilimin Addinin Musulunci – ECOWAS November 16, 2025 Labarai APOSUN Ta Jaddada Aniyarta Na Daƙile Hada-hadar Haramtattun Kuɗaɗe November 16, 2025 Labarai NNPP Tana Da Ƙwarin Gwiwar Riƙe Kano Da Lashe Jihohin Arewa A Zaɓen 2027 – Ajuji November 16, 2025.

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

HOTUNA: NDLEA ta ƙone tan dubu 52 na miyagun ƙwayoyi a Zariya

Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA), reshen Jihar Kaduna, ta ƙone fiye da tan 52,000 na miyagun ƙwayoyi a bainar jama’a a ƙauyen Karofi da ke Kufena, a kan tsohuwar hanyar Birnin Gwari da ke Zariya.

An gudanar da bikin ƙone kayan ne a wannan Alhamis ɗin, inda Birgediya Janar Buba Marwa (Rtd.), Shugaban NDLEA kuma Babban Jami’in Gudanarwa, ya jaddada cewa hukumar ta duƙufa domin kawar da barazanar miyagun ƙwayoyi daga cikin al’umma.

Ina girmama sojojin Nijeriya — Wike Bebejin Katsina, Alhaji Nuhu Yashe ya rasu

Ya bayyana cewa, “Miyagun ƙwayoyi suna lalata tarbiyyar matasa a hankali, ba tare da an farga ba. Kowace tan ɗaya da aka ƙone, an ceto rayukan mutane da dama daga halaka.”

Shugaban hukumar, wanda Mataimakin Daraktan Harkokin Miyagun ƙwayoyi, Suleiman Ningi, ya wakilta, ya yi gargadi ga masu safarar miyagun ƙwayoyi da su daina kasuwancin kayan haram, su koma safarar kayan halal, ko kuma su fuskanci hukunci mai tsanani.

Janar Marwa ya ce NDLEA na ci gaba da fatattakar manyan dillalan miyagun ƙwayoyi da ƙungiyoyin su, tare da ƙarfafa wayar da kai a kan illolin kayan laifi.

Ya yaba wa rundunar NDLEA ta Jihar Kaduna bisa ƙoƙarinta, tare da gode wa Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, saboda goyon bayan da yake bayarwa, ciki har da ba da motocin aiki da fili domin gina bariki ga hukumar.

Shugaban NDLEA ya roƙi iyaye, shugabannin al’umma da na addini, da su ƙara ƙaimi wajen wayar da kan mutane kan illar ta’ammali da miyagun ƙwayoyi, yana mai cewa, “Yaƙin da ake yi da miyagun ƙwayoyi yaƙin ceto rayuka da makomar ƙasa ne.”

Kwamandan NDLEA na Jihar Kaduna, Mohammed Tukur, ya bayyana cewa bikin ƙone miyagun ƙwayoyi na nuna jajircewar hukumar wajen kare al’umma daga illolin sha da safarar su.

Ya ce wannan mataki shi ne “ƙarshe a jerin matakan aiwatar da doka”, domin tabbatar da cewa waɗannan ƙwayoyi masu haɗari sun ɓace gaba ɗaya daga hannun mutane, don hana su cutar da matasa ko ƙarfafa ayyukan laifi.

Kwamandan ya bayyana cewa miyagun ƙwayoyin da aka ƙone sun haɗa da Tramadol, Wiwi (Cannabis), da Hodar Iblis da an kiyasta darajar su za ta kai Naira biliyan biyar.

Ya bayyana cewa wannan gagarumar nasara ta samu ne sakamakon ƙoƙarin jami’an NDLEA tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro irin su sojoji, hukumar kwastam, DSS, da ‘yan sanda.

Ya ce, “Wannan aiki shaida ce ta gaskiya, riƙon amana, da ƙwarewar NDLEA. A yau, muna sake tabbatar da sakonmu cewa Jihar Kaduna ba mafakar masu safarar ko masu amfani da miyagun ƙwayoyi ba ce.”

Tukur ya jaddada biyayyarsu wajen dawo da zaman lafiya da kare makomar matasan jihar.

A nasa jawabin, Gwamna Uba Sani ya yaba wa NDLEA bisa ƙoƙarinta wajen ganin cewa an tsarkake Jihar Kaduna daga miyagun ƙwayoyi.

Gwamnan ya ce yawan ƙwayoyin da aka ƙone na nuna tsananin ƙoƙarin da ake yi wajen tabbatar da doka a jihar, tare da jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da tallafa wa dukkan hukumomin tsaro wajen yaƙi da laifuka da duk wata barazanar tsaron al’umma a jihar.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • IRGC ta kama wani jirgin ruwan dakon mai a gabar tekun kudancin Makran
  • Sojoji sun kashe ’yan ta’adda, sun kama mutum 94
  • ’Yan bindiga sun kashe ’yanga 16 sun sace mutane 42 a Neja
  • ’Yansanda Sun Cafke Wani Da Ake Zargin Dan Ta’adda Ne A Jihar Kebbi
  • NAHCON Ta Ƙaddamar Da Kwamitin Da Zai Kula Da Shafin Nusuk Masar Na Hajjin 2026
  • NSCDC Ta Cafke Mutum Biyu Bisa Zargin Satar NAPEP Da Safarar Miyagun Kwayoyi A Kano
  • Kotu Ta Yanke Wa Mutum 4 Hukuncin Kisa Kan Kashe Wani Makanike A Kano
  • An kama ’yan Najeriya 3 a Kenya kan zargin aikata damfara
  • HOTUNA: NDLEA ta ƙone tan dubu 52 na miyagun ƙwayoyi a Zariya