NELFUND ya raba wa ɗalibai tallafin karatu na Naira Biliyan 116
Published: 17th, November 2025 GMT
Asusun Lamunin Ilimi na Najeriya (NELFUND) ya bayyana cewa ya raba jimillar kuɗi Naira biliyan 116 domin tallafa wa dalibai a faɗin ƙasar nan wajen biyan kuɗin makaranta da kuma kula da rayuwarsu ta yau da kullum.
Shugaban NELFUND, Akintunde Sawyerr ya bayyana a Abuja cewa, daga cikin kuɗin, an tura Naira biliyan 65 aka tura kai tsaye zuwa makarantu 239 na tarayya — jami’o’i, kwalejojin fasaha da kwalejojin ilimi — domin biyan kuɗin makarantar ɗaliban da aka amince da buƙatar lamuninsu.
Sauran Naira biliyan 51 kuma an tura ne kai tsaye ga ɗaliban a matsayin tallafin kula da rayuwa na wata-wata.
Ya ce: “Mun raba Naira biliyan 65 ga makarantu da kuma Naira biliyan 51 ga ɗaliban domin tallafin rayuwa. Jimillar kuɗin da aka fitar ya kai Naira biliyan 116.”
Sawyer ya ce har zuwa yanzu NELFUND biya dalibai 624,000 da suka riga suka fara karɓar kuɗin makaranta da tallafin rayuwa.
Shugaban NELFUND ya bayyana shirin a matsayin ɗaya daga cikin manyan shirye-shiryen saka jari na zamantakewa da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta aiwatar.
Ya ce manufar shirin ita ce kawar da matsalolin kuɗi da ke hana ɗalibai ci gaba da karatu, tare da tabbatar da cewa babu ɗan Najeriya da zai bar makaranta saboda rashin kuɗi.
Sawyer ya tabbatar da cewa NELFUND za ta ci gaba da gudanar da shirin cikin gaskiya da inganci, musamman ganin yadda yawan ɗaliban da ke amfana yake ƙaruwa a kullum.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Ɗalibai Najeriya Naira biliyan
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnati, UNICEF da ’yan jarida sun haɗa don yaƙar cututtukan da aka manta da su a Gombe
Gwamnatin Tarayya, tare da haɗin gwiwar UNICEF da gwamnatin Jihar Gombe, sun shirya taron wayar da kai da ’yan jarida domin yaƙi da cututtukan da ba a cika kula da su ba.
Ofishin UNICEF na Bauchi ya haɗa kai da ’yan jarida da JPHCDA da wakiliyar Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya, Hauwa Abubakar, domin tattaunawa kan yadda za a rage yaɗuwar cututtukan a jihar.
Sanusi II ne kaɗai halastaccen Sarki a Kano — Kwankwaso Babu Janar ɗin da ISWAP ta kama a Borno — SojojiA taron, ’yan jarida sun samu damar jin bayanai daga masana da kuma yadda aikace-aikacen yaƙi da cututtukan ke tasiri a cikin al’umma.
Gwamnatin Jihar Gombe tana ware Naira miliyan 25 duk shekara domin yaƙi da NTDs, amma har yanzu akwai wuraren da ake buƙatar ƙarin tallafi.
Ƙungiyar Amen Health Care and Empowerment Foundation, ta ce tun 2015 ake samun ci gaba wajen yaƙi da cututtuka kamar onchocerciasis, lymphatic filariasis, da schistosomiasis.
Ƙungiyar ta kuma ce an yi wa waɗanda ke fama cututtukan tiyata kyauta.
Wakilin UNICEF, Hillary Adie, ya ce matsanancin talauci da rashin tsafta na taimaka wa yaɗuwar cututtukan.
Ya jaddada muhimmancin tsaftar muhallin zama.
Hauwa Abubakar, ta yi kira da a ƙara haɗa kai tsakanin gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki.
Ita kuwa Shugabar UNICEF ta Bauchi, Dokta Nuzhat Rafique, ta yaba wa Gombe kan ci gaban da ta samu, tare da roƙon ’yan jarida su ci gaba da wayar da kan jama’a game da cututtukan.