An sanya hannu kan yarjejeniyoyin cinikayya na biliyoyin kudi, a yayin baje kolin hajojin fasahohin zamani na kasar Sin ko CHTF, wanda aka kammala a jiya Lahadi a birnin Shenzhen dake kudancin kasar Sin. Wannan ne karo na 27 da aka gudanar da baje kolin na CHTF, inda aka kai ga daddale huldodin cinikayya da ayyukan zuba jari 1,023, wadanda darajarsu ta haura kudin Sin yuan biliyan 170, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 24.

Baje kolin na wannan karo ya gudana ne bisa taken “Fasahohi masu jagorantar ci gaba da dunkulewar masana’antu”. Kazalika, taron na yini uku ya hallara kamfanoni da hukumomi sama da 5,000 daga kasashe da yankuna sama da 100, ya kuma samu halartar baki sama da 450,000.

Yayin baje kolin na CHTF, an nuna sabbin kayayyaki sama da 5,000, da fasahohi da ayyukan kirkire-kirkire da dama. Har ila yau, an samar da manyan yankunan nune-nune 22, ciki har da na muhimman na’urorin gudanar da ayyuka, da na fasahar AI da mutum-mutumin inji, da manyan kayan ayyukan na kasa, da kayan laturoni, da na’urorin sufurin sama dake zirga-zirga kusa da doron kasa, kayayyakin da suka shaida halartar manyan masu ruwa da tsaki a harkokin binciken kimiyya na duniya, da nasarorin da Sin ta cimma a fannonin kirkire-kirkire. (Saminu Alhassan)

ADVERTISEMENT ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Tsohon Firaministan Japan Ya Soki Kalaman Takaichi Dangane Da Batun Yankin Taiwan November 17, 2025 Daga Birnin Sin Fasinjojin Da Kasar Sin Ta Yi Jigilarsu Ta Jirgin Kasa Daga Janairu Zuwa Oktoba Sun Kai Biliyan 3.95 November 16, 2025 Daga Birnin Sin Babban Jirgin Ruwan Yaki Samfurin 076 Na Sin Ya Kammala Gwajinsa Na Farko A Teku November 16, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Babu Janar ɗin da ISWAP ta kama a Borno — Sojoji

Rundunar Soji ta ƙaryata rahotannin da ke cewa an yi garkuwa da kwamandan Bitget ta 25 da ke Jihar Borno a wani harin kwanton ɓaunan mayaƙan ƙungiyar ISWAP.

Ta buƙaci jama’a su yi watsi da wannan labarin ƙarya, tare da yin addu’ar samun nasarar sojojin Najeriya da ke bakin daga.

Rundunar ta ce sojojin sun murƙushe wani harin kwanton ɓauna da ISWAP ta kai musu a yayin da suke sintiri domin kare al’ummomin da ke kewaye da Wajiroko a yankin Azir Multe a Ƙaramar Hukumar Damboa da ke Jihar Borno.

Ta ce sojojin sun gamu da kwanton ɓauna ne daga ’yan ta’adda yayin da suke dawowa daga aikin sintiri a gefen Dajin Sambisa.

Mayaƙan ISWAP sun sace Janar sun kashe sojoji a Borno Yadda ’yan bindiga suka kashe banga 16 suka sace mutane 42 a Neja

Rundunar ta jaddada cewa Kwamandan Brigedi ta 25, Birgediya Janar M. Uba, shi ne ya jagoranci tawagar, wacce ta haɗa da mambobin CJTF, kuma sun koma sansaninsu lafiya.

Ta ce sojojin sun fuskanci harin ne cikin ƙwazo, inda suka yi musayar wuta da makiya har suka fatattake su.

Sanarwar rundunar, ta hannun muƙaddashin kakakinta, Laftanar-Kanar Appolonia Anele, ta ce a yayin arangamar, sojoji biyu da mambobin CJTF biyu sun kwanta dama.

Hedikwatar tsaro ta yaba da jarumtakar dakarun, tare da yin ta’aziyya ga iyalai da abokan aikin waɗanda suka rasa rayukansu.

Babban Hafsan Sojin Ƙasa, Laftanar-Janar Waidi Shaibu, ya jinjina wa jarumtar dakarun da ke ci gaba da aiki a ɗaya daga cikin yankunan da suka fi haɗari a ƙasar, yana mai cewa sadaukarwarsu abin karramawa ne a kullum wajen kare Najeriya.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Fasinjojin Da Kasar Sin Ta Yi Jigilarsu Ta Jirgin Kasa Daga Janairu Zuwa Oktoba Sun Kai Biliyan 3.95
  • Tsohon Minista Kabiru Turaki ya zama sabon shugaban PDP na ƙasa
  • Za A Wallafa Makalar Xi Game Da Gina Sabbin Ginshikan Samar Da Ci Gaban Kasa Masu Inganci
  • An Gabatar Da Sabuwar Hanyar Raya Hadin Gwiwar Tattalin Arziki Da Cinikayya A Tsakanin Sin Da Afirka
  • MDD: Mutane 100,000 Ne Su Ka Fice Daga Birnin Al-Fasher Na Kasar Sudan
  • Illolin Neman Kudi Ido Rufe Ba Tare Da Kula Da Halal Ko Haram Ba
  • Jakadan Sin A Japan Ya Bayyana Matukar Adawa Da Kalaman Firaminista Takaichi Dangane Da Kasar Sin
  • Babu Janar ɗin da ISWAP ta kama a Borno — Sojoji
  • Bangaren Sauka Na Kumbon Shenzhou-21 Ya Iso Doron Duniya