’Yan bindiga sun kashe mutum 3 sun sace 64 a Zamfara
Published: 17th, November 2025 GMT
’Yan bindiga sun kashe mutum 3 tare da yin garkuwa da wasu 64 a ranar Asabar a Karamar Hukumar Tsafe ya Jihar Zamfara.
Cikin waɗanda ’yan ta’addan suka kashe har da wani jigon jam’iyyar APC, Hon. Umaru Moriki wanda aka bindige a kan hanyar Gusau zuwa Tsafe, waɗanda aka yi garkuwa da su kuma har da mata da ƙananan yara a kauyen Fegin Baza.
Harin ta faru ne washegarin da Ministan Tsaro, Bello Matawalle ya ziyarci jihar, inda ya sanar cewa Hedikwata Tsaro ta girke ƙarin jami’an tsaro a jihar.
A yayin ziyarar ministan ya bayyana cewa zai gana da jami’an tsaro inda zai ba su umarni kar su raha wa ’yan ta’adda.
NAJERIYA A YAU: Matsayar Doka Kan Taron Da Jam’iyyar PDP Ta Gudanar Da amincewar hukumomi nake tattaunawa da ’yan bindiga — Sheikh GumiMinistan ya kuma zargi gwamnatin jihar kan abin da yake yi da kuɗaɗen da take samu daga Gwamnatin Tarayya.
Jihar, wadda ita ce mahaifar Matawalle, tana fama da matsalar hare-haren ’yan bindiga da suka hana ayyukan noma da sauran harkokin tattalin arziki.
Hare-haren bayan nan, kari ne a kan wasu da dama da suka addabi jihar, duk da ayyukan soji da dama domin daƙile matsalar.
Yadda abin ya faruRahotanni sun ce ’yan bindiga kusan 30 ne suka buɗe wuta kan motar Hon. Moriki yayin da yake kan hanyarsa zuwa Kaduna, inda suka kashe shi nan take.
Bayan haka, sun yi garkuwa da mazauna kauyen 64, suka tafi da su zuwa wani wurin da ba a sani ba.
Hon. Moriki, wanda ya taɓa tsayawa takarar kujerar Majalisar wakilai a Mazaɓar Zurmi/Shinkafi, shi ne Sarkin Fada na Moriki a halin yanzu.
Ɗan marigayin, Abubakar Umar Moriki, ɗalibi a Jami’ar Bayero ta Kano (BUK) ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya ce: “Baba ya yi ƙoƙarin yin u-turn bayan ya lura da ’yan bindiga, amma suka buɗe masa wuta. An harbe shi, ya rasu nan take. An yi masa jana’iza bisa tsarin Musulunci. Allah Ya gafarta masa, ya kuma sanya shi da Aljanna Firdaus.”
An gudanar da sallar jana’izar marigayi a Masallacin Juma’a na Federal Low-cost, Tudun Wada da ke Gusau, ƙarƙashin jagorancin Imam Alƙali Abdullahi Yakubu.
Ministan Tsaron Ƙasa, Alhaji Bello Mohammed Matawalle, ya halarci jana’izar tare da yin ta’aziyya ga iyalan marigayin.
Matawalle ya bayyana rasuwar Hon. Moriki a matsayin babban rashi ga jihar da ƙasa baki ɗaya, la’akari da ayyukan alheri da ya yi wa jama’a, musamman maƙwabta da ’yan uwa.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun APC na jihar, Yusuf Idris, ya fitar, Matawalle ya yi addu’ar Allah Ya saka masa da Aljanna Firdaus, ya kuma ba iyalansa ƙarfin zuciya wajen jure wannan rashi.
Ministan ya bayar da gudummawar Naira miliyan 10, buhunan shinkafa 50, buhunan masara 25 da buhunan gero 25 ga iyalan marigayin, tare da tabbatar musu da kulawa daga gwamnati.
A madadin iyalan marigayin, Ambassador Abubakar Hussaini Moriki ya gode wa ministan bisa kulawa da tausayi da ya nuna.
Ya ce sun san cewa ministan ya soke dukkan ayyukansa na yau domin halartar jana’izar, ya kuma yi tafiya daga garin Maradun zuwa Gusau don yin ta’aziyya da su a wannan lokaci na jarrabawa.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga Garkuwa Tsaro Zamfara yan bindiga Ministan ya
এছাড়াও পড়ুন:
Mayaƙan ISWAP sun sace Janar sun kashe sojoji a Borno
Rahotanni na nuni da cewa mayaƙan ƙungiyar ISWAP sun yi garkuwa da wani Janar ɗin sojan Najeriya tare da kashe sojoji da dama a wata Arangama a Jihar Borno.
Ayaraijn motocin sojojin ya faɗa a harin kwanton ɓaunan mayaƙan ISWAP ne a daren Juma’a a Jihar Borno.
Rahotanni na nuna cewa mayaƙan sun yi garkuwa da Janar ɗin tare da hallaka sojoji da dama da ke tare da shi, ciki har da mambobin CJTF.
Rahoton kafar HumAngle — cibiyar da ke mayar da hankali kan rikice-rikice da batutuwan jin ƙai — wanda PremiumTimes ta ruwaito, ya ce Janar ɗin da aka yi garkuwa da shi shi ne kwamandan wani bitget ɗin soji, kuma shi ne yake jagorantar dakarun a lokacin.
Idan ta tabbata, “wannan shi ne karo na farko da wata ƙungiyar ta taɓa kama wani Janar da ke kan aiki a fagen daga,” a cewar HumAngle.
Duk da cewa ’yan ta’adda sun kashe manyan jami’an soja a wasu hare-hare, amma ba kasafai ake samun labarin garkuwa da jami’an soja masu muƙami irin wannan ba.
Har yanzu hukumomin soji ba su fitar da sanarwa kan lamarin ba, kuma ba a tabbatar da adadin waɗanda suka mutu ba.
Kakakin Rundunar Sojin Najeriya, Laftanar-Kanar Onyechi Anele, bai amsa sakon tambaya da aka tura masa kan lamarin ba.
HumAngle ta ce tana bibiyar al’amuran, kuma za ta ci gaba da kawo sabon bayani idan ya samu.