An Yi Kira A Bai Wa ‘Yan Hijira Saboda Sauyin Muhalli
Published: 16th, November 2025 GMT
Kungiyar kasa da kasa mai kula da ‘yan hijira ( IOM) tana yin kira ga shugabannin kasashen duniya da su bayar da kariya da kare hakkokin wadanda suke rayuwa a yankunan da suke fama da matsalar sauyin yanayi.
A taron da ake yi a yanzu haka a garin Belem na kasar Brazil kungiyoyi masu zama kansu dake fafutuka da rajin kare muhalli suna gabatar da shawarwari akan yadda za fuskacin matsalolin da duniya take fuskanta.
Kiran kungiyar ya ambato mutanen da sauyin yanayi ya tilasta musu yin hijira, ‘yan asalin kasa a cikin karkara da ‘yan gargajiya.
Ibtila’oin dabi’a irin su ambaliyar ruwa, zafi mai tsanani, fari da mahaukaciyar guguwa, suna tilastawa miliyoyin mutane barin gidajensu a kowace shekara. Da akwai da dama da ba su iya tsallake iyakokin kasashensu, suna ci gaba da zama a wasu yankuna nesa da gidajensu.
Kungiyar tana son ganin an taimakawa wadannan bangarorin na mutane a karkashin kare muhalli.
Masana suna bayyana cewa a nan gaba, za a sami wasu kasashen da za su nitse a karkashin tekuna da suke kara cikowa,ko kuma su zama wuraren da ba za za iya rayuwa a cikinsu ba.
Mataimakin Babbar darakta na kungiyar ( IOM), Ughoci Daniels ya bayyana cewa, samar da tsarin yin gargadin gaggawa, da ayyukan hidima a cikin yankunan da aka fi fuskantar hatsari, yana da matukar muhimmanci domin karfafa mutane su ci gaba da rayuwa a inda suke.
Daniels ya kuma ce; Da dama daga cikin wadanda su ka fice daga cikin muhallinsu saboda sauyin yanayi, suna fadin cewa sun fiifta komawa zuwa gidajensu. Sai dai kuma garuruwan nasu sun tashi daga yadda su ka san su a baya saboda sauyin yanaki. A dalilin haka, abinda ake da bukatuwa da shi, shi ne samar da abubuwan da za su karfafa su.”
A dalilin haka, Daniel ya yi fatan ganin taron da ake yi na kasar Brazil akan muhalli ya zama wanda zai daura dan Ba, a fagen samar da sauyi da kuma biyan asarar da aka samu saboda sauyin yanayin.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka An Amince Da Sauye-sauye A Tsarin Mulkin Kasar Benin November 16, 2025 Isra’ila Ta Kai Wa Sojojin MDD Hari A Kasar Lebanon November 16, 2025 Makiya Sun Kulla Makirci kan Kasar Labanon Irin Wanda Suka Kulla Kan Siriya November 16, 2025 Kasar Afghanistan Na Kokarin Karkata Akalar Kasuwancinta Zuwa Iran November 16, 2025 Kanada Ta Tsare Tsohon Wakilin Majalisar Dinkin Duniya Mai Bincike Kan Laifukan Yakin Israila. November 16, 2025 Zarfi: HKI Ce Kawai Take Ayyana Nukiliya Ba Bisa Kaida Ba A Yammacin Asiya. November 16, 2025 Shugaban kasar venuzuwela Yayi Tir Da Atisayan Soji Da Trinidad and Tobago Ke yi. November 16, 2025 IRGC ta kama wani jirgin ruwan dakon mai a gabar tekun kudancin Makran November 16, 2025 Iran : sojojin Amurka a yankin Caribbean barazana ne ga zaman lafiya November 16, 2025 Lebanon za ta kai karar Isra’ila a MDD kan gina Katanga a iyakarta November 16, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban kasar venuzuwela Yayi Tir Da Atisayan Soji Da Trinidad and Tobago Ke yi.
Shugaban kasar venuzuwela Nicolas Maduro yayi suka game da atisayan soji da Trinidad an Tobago ke yi, kuma ya bayyana shi a matsayin abin da bai dace ba kuma yana barazana ga zaman lafiyar yankin Caribbean.
Atisayan sojin yana kara tada hankali tsakanin kasar venuzuwela da daya daga cikin makwabciyarta ta kurkusa adaidai lokacin da ayyukan sojojin Amurka a yankin karebiya ya jefa yanki cikin zaman dar-dar.
Kasar Trinidad and Tobago ta tsara fara gudanar da atisayin soji na hadin guiwa a cikin ruwan dake kusa da kasar venuzuwela daga ranar 17 zuwa 20 ga watan nuwamba, atisayan yazo daidai da ayyukan tsaro da Amurka ke jagoranta a yankin karebiya wandaAamurka tace ya shafi yaki da masu safarar miyagun kwayoyi ne.
Sai dai maduro ya bayyana rashin amicewarsa da daukarsa a matsayin wasu dabarun ne na boye, na gurgunta gwamnatinsa.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka IRGC ta kama wani jirgin ruwan dakon mai a gabar tekun kudancin Makran November 16, 2025 Iran : sojojin Amurka a yankin Caribbean barazana ne ga zaman lafiya November 16, 2025 Lebanon za ta kai karar Isra’ila a MDD kan gina Katanga a iyakarta November 16, 2025 AU ta sake watsi da ikirarin Trump cewa ana kashe Kiristoci a Najeriya November 16, 2025 Falasdinu ta yi wasan sada zumunci a Spain November 16, 2025 Amurka Ta Yi Gwajin Makaman Nukiliya A Watan Ogusta November 15, 2025 Adadin Ma’adanin “Colbat” Da DRC Ta Bai Wa Duniya Ya Kai Ton 1,000 November 15, 2025 Ma’ariv: Netanyahu Yana Tsoron Hukuncin Da Kotu Za Ta Yanke Akansa November 15, 2025 An Bayyana Sunayen Kasashen Da Su Ka Fi Sayar Wa “Isra’ila” Man Fetur A Lokacin Yakin Gaza November 15, 2025 MDD: Mutane 100,000 Ne Su Ka Fice Daga Birnin Al-Fasher Na Kasar Sudan November 15, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci