2025-06-16@02:48:45 GMT
إجمالي نتائج البحث: 16

«yawon bude ido»:

    Wani mummunan hatsarin mota a hanyar Kaduna zuwa Zariya ya yi sanadin mutuwar mutum takwas ’yan gida daya, yayin da wasu mutum biyu ke can kwance a asibiti rai a hannun Allah. Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne wajen misalin karfe 6:00 na yammacin ranar Litinin a garin Barakallahu da ke kan hanyar Kaduna zuwa Zariya, ana tsaka da bukukuwan Babbar Sallah. A cewar rahotannin, lamarin ya faru ne lokacin da wata mota da ke tsala gudu ta kwace sannan ta danne mutanen da ke tsaye a gefen hanya bayan dawowarsu daga yawon sallah. Sojoji sun kashe kasurguman ’yan bindiga 3 a Zamfara Mutum ɗaya ya tsira da ransa cikin 242 a hatsarin jirgin India A cewar mahaifin mamatan,...
    Kimanin mutum bakwai sun riga mu gidan gaskiya bayan tarwatsewar wani abun fashewa da ake zargi mayaƙan Lakurawa sun dasa a Ƙaramar Hukumar Tangaza ta Jihar Sakkwato. Aminiya ta ruwaito cewa waɗanda lamarin ya rutsa da su da ke kan babura na hanyarsu ta dawowa daga yawon bikin sallah a ƙauyen Gwabro. Isra’ila ta ƙwace jirgin ruwa a hanyar kai agaji Gaza Sojoji sun kashe wani kwamandan ’yan ta’adda a Yobe Bayanai sun ce an dasa abun fashewar ne a ƙarƙashin wata itaciya da ke zaman wurin hutawar dakarun sojoji a lokacin da suka fito sintiri a yankin. Majiyiyo sun ce mutum shida sun mutu nan take yayin da ɗaya daga cikin wasu mata biyu yara da suka jikkata ta...
    Tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya bayyana dalilin da ya sa ya naɗa Nyesom Wike a matsayin Shugaban Ma’aikata a lokacin da yake Gwamnan Jihar Ribas, maimakon Kwamishinan Kuɗi. Amaechi, ya ce ya zaɓi Wike ne a matsayin Shugaban Ma’aikata domin ya samu damar sanya ido a kansa. Tinubu ya gana da Fubara a Legas Jami’an DSS sun kashe ’yan bindiga 45 a Neja “Na so ya zama shugaban ma’aikata ne saboda na riƙa sanha ido a kansa. “Ban ba shi kujerar kwamishinan kuɗi ba,” in ji Amaechi a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Arise da yammacin ranar Talata. Wannan martanin ya biyo bayan kalaman Wike ne, wanda yanzu shi ne Ministan Babban Birnin...
    Ta hanyar da za ki gano kuwa ita ce, ki kai mata ziyara ta wuni daya kuma idan kin je ki kula da yaya yanayin huldodinta da kuma gyaran jikinta suke a cikin gidanta, ta nan ne za ki fahimci matsalar rashin jituwarta da mijin na ta. Domin ita matsalar rashin kulawa da gyaran jiki wani namiji ba zai iya bude baki ya fada ba. Koda ita matar ma ba zai iya fada mata ba sai dai kurum ka ga ana rigima ita tana ta ganin yana yi mata wulakanci shi kuma ga abin da yake gani daban, don haka yana da matukar muhimmancin ga ma’aurata da su himmantu wajen gyara jiki ba su kadai ba, har da wanda ba...
    A cewar jami’ai, za’a tsara yadda tsarin fitar da barasar zai kasance ta hanyar tabbatar da cewar an ba da horo ga masu sayar da ita da kuma basu takardar lasisin sayar da barasar. Hakazalika, za a tsaurara ka’idoji akan sayar da barasa a kasar, gwamnati ta jaddada cewa ana gabatar da sauye-sauyen ne cikin taka-tsantsan tare da kula da al’adun al’ummar kasar.   “Manufar ita ce, maraba da duniya ba tare da rasa asalin al’adu ba, sanya Saudiyya a matsayin mai ci gaba, duk da haka mai mutunta taswirar yawon shakatawa na duniya,” in ji hukumomin Saudiyya a cikin wata sanarwa.   Matakin ya zo ne a daidai lokacin da Saudiyya ke neman yin gogayya da kasashe makwabta kamar...
    Wasu gidajen aure kuwa sai ka samu mijin mai tsananin gyaran jiki da kulawa har ka ga ya tsaya bata lokaci yana gyara fuska da fatar jiki ke in kika gashin sai ki rantse mace ce ba namiji ba, saboda yadda fatarsa ke kyalli da haske, amma idan ka shiga gidansa sai ka tarar da matarsa tamkar mai aikin gidansa ita ma wacce ba ta damu da gyaran jiki ba. Don haka yana da matukar muhimmancin ga kowanne dan Adam ya lazamta wajen gyaran jikinsa, mace ko namiji musamman ma ga ma’aurata.   Za Mu Ci Gaba Mako Zuwa Idan Allah Ya Kai mu Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai...
    Babban darektan hukumar kula da tattara bayanai da yada su ta bangaren teku ta kasar Sin, Shi Suixiang, ya bayyana cewa, manufofin tallafi da aka bullo da su a matakai na tsakiya da na kananan hukumomi sun karfafa ci gaban yawon shakatawar.   Ya kara da cewa, gwamnatin tsakiya ta inganta fadada hanyoyin jiragen ruwa da kayayyakin yawon shakatawa yayin da kuma ake kara daidaita tsarin rajistar jiragen ruwa da kuma shigar da su cikin hada-hada.   Wasu manazarta dai sun bayyana cewa, a sa’ilin da lokacin goshin damina ke gabatowa, ana sa ran yawon shakatawa na bakin teku da tsibirai a yankin kudu maso gabashin kasar Sin ya bunkasa, tare da kara samun balaguro ta ruwa da nufin cin...
      Kasar Sin tana kara bude kofa ga kasashen waje, don haka masu zuba jari na kasashen waje za su gane wa idonsu irin damammakin da aka samar. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    An naɗa mace ta farko a matsayin mai magana da yawun rundunar sojin Nijeriya. Appolonia Anaele mai muƙamin Laftanar Kanar ce za ta karɓi muƙamin daga hannun Manjo-Janar Onyema Nwachukwu. An taƙaita zirga-zirgar babura da haramta kiwon dare a Filato Matashin da ya yi iƙirarin kashe mutane ya kai kansa ofishin ’yan sanda a Kano Bayanai sun ce muƙamin nata zai fara ne a ranar Talata 22, ga watan Afrilun da muke ciki. Shekaru sama da 50 ke nan da kafa rundunar sojin Nijeriya, kuma babu wata mace da ta taɓa riƙe wannan muƙami. Duk da cewa kawo yanzu tana a matsayin mai riƙon muƙami ne, amma duk da haka wannan shi ne karon farko.
    Namibiya ta janye bayar da biza ga Amurka, Burtaniya, da wasu kasashe sama da 30. Matakin, wanda majalisar ministocin Namibiya ta yanke tun a watan Yuli, ya fara aiki ne a ranar 1 ga Afrilu. Ya zuwa yanzu, galibin kasashen Turai, ciki har da Jamus, babbar tushen yawon bude ido a Namibiya, sun ci gajiyar shigowa kasar ba tare da biza ba. Sabuwar shugabar Namibiya da aka rantsar, Netumbo Nandi-Ndaitwah, tana ci gaba da shirye-shiryen soke bizar shiga kasar ga wasu Karin kasashe, ta yadda ‘yan kasashen za su iya shiga Namibia ba tare da biz aba. Manufar hakan dai ita ce kafafa harkokin kasuwanci da yawon bude ido a kasar ga yan kasashen ketare, da kuma karfafa kawance da...
    Minista mai kula da al’ada da yawon bude ido da kuma sana’o’in hannu na Iran Ridha Salihi wanda ya gana da jakadan Tunisiya a Iran,Imad al-Rahmani ya bayyana bukatar hanyoyin bunkasa alakar yawon bude ido a tsakanin kasashen biyu, yana mai kara da cewa: Yarjejeniyar da aka cimmawa a tsakanin kasashen biyu dangane da yawon bude ido wani yunkuri ne mai matukar muhimmaanci. Kamfanin dillancin labarum “Iran” ya ambato; Ridha Salihi Amiri yana mai yin ishara da tarihin alakar kasashen biyu ta fuskar al’adu, sannan ya kara da cewa; Kasar Tunis ta samu ci gaba sosai a tsakanin kasashen Lrabawa ta fuskar inganta harkokin yawon bude ido. Haka nan kuma ya yi ishara da yadda Iran take da wuraren bude...
    Bisa ga yadda wasu fina-finan kasar Sin ke samun karbuwa a kasuwannin kasa da kasa, ciki har da fim din “Ne Zha 2”, a yau Litinin an kaddamar da bikin “Tafiya a kasar Sin bisa fina-finan kasar” a gidan tarihi na fina-finai na kasar Sin dake nan birnin Beijing, wanda hukumar kula da fina-finai ta kasar Sin da babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) suka shirya, kuma gidan talabijin na kasa da kasa na kasar Sin (CGTN) da cibiyar shirye-shirye ta tashar fina-finai suka karbi bakuncinsa. Bikin wanda ya fi mayar da hankali kan gudanar da ayyukan tallata fina-finai da yawon shakatawa ta hanyar nuna fina-finan kasar Sin a ketare, da shirya bikin nune-nunen fina-finan kasar...
    Wani kifi jinsin Shark da mamallakin Kamfanin Airbnb da ya shahara a duniya mai tsawon kafa 25 ya fusata, inda ya fito daga rufin gidan da yake saboda matakin da aka ɗauka na tilasta rufe gidan da aka ajiye shi. Mamallakin Kamfanin wanda yake mazaunin Birtaniya ne, mai suna Dakta Magnus Hanson-Heine ya rasa wani shirin neman alfarma daga Karamar Hukumar Oxford na hana shi amfani da wurin zama na ɗan gajeren lokaci na cikin kadarorinsa da aka fi sani da Shark House (wato inda yake kiwon kifin). Mazabar Tsanyawa/Kunchi ta shafe shekara guda ba tare da wakilci ba Yadda za a yaƙi talauci a Arewa maso Gabas  — Shettima Ya yi iƙirarin cewa bai samu ƙorafi ko ɗaya daga...
    Duk da cewa akwai sauran lokaci kafin babban zaben 2027, ana ci gaba da musayar yawu kan shirye-shiryen manyan ‘yan siyasa da ke hamayya da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu, inda suke tarurruka tare da tuntuɓar juna kan yadda za su kayar da Jam’iyyar APC mai mulki a Zaɓen 2027. Fadar Shugaban kasa ta mayar da martani kan kalaman da wasu daga cikin ‘ya’yan jam’iyyun adawa da na cikin gidanta suke yi, inda suka zarge ta da sauka daga kan turbar da jam’iyyar take. Katsina ta zama cibiyar haɗin kan ƙabilun ƙasa a Arewa — Gwamna Radda Ta kashe saurayinta saboda ya gaisa da tsohuwar abokiyar karatunsa Fadar Shugaban kasa na mayar da martani ne bayan wani taro da jagororin hamayya...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe ta haramta yawon dare, ta hanyar takaita zirga-zirga daga kare 12 na dare zuwa 5 na asubahi. Kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi ya sanar a ranar Alhamis cewa dokar za ta fara aiki ranar Juma’a, 7 ga Fabrairu, 2025. Ya bayyana cewa an kafa dokar takaita zirga-zirgar ne bayan samun rahotannin barazanar tsaro. Sanarwar ta ce, “takaita zirga-zirgar na da nasaba da karuwar barazanar tsaro da ke fuskantar al’ummar Gombe,” kuma a shirye rundunar take ta shawo kansu. NAJERIYA A YAU: Dalilin Faɗuwar Farashin Tumatur A Kasuwa Majalisa na son ƙirƙiro sabbin jihohi 31 a Najeriya Mutuwar Almajirai: Tinubu ya buƙaci a samar da matakan kare ɗalibai DSP Buhari ya kara da cewa rundunar za...
    Yayin da ake fuskantar matakan cin zarafi daga wata kasa daya tilo a duniya, kasar Sin ta lashi takobin daukar kwararan matakai don kare hakkoki da muradunta, kamar yadda mai magana da yawun ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin, He Yongqian ta bayyana a yau Alhamis. Mai magana da yawun ma’aikatar ta fada a wani taron manema labarai da aka gudanar cewa, kakaba karin haraji da Amurka ta yi ita kadai, ta yi matukar saba wa ka’idojin kungiyar kasuwanci ta duniya, wato WTO, wanda ke nuni baro-baro a fili da ra’ayi na kashin kai da gicciye kariyar ciniki. Don haka, a cewar jami’ar ma’aikatar, yunkurin na Amurka ya yi matukar kawo cikas ga tsarin gudanar da ciniki a tsakanin bangarori daban-daban,...
۱