Amurka za ta binciki zargin yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Nijeriya ranar Alhamis
Published: 19th, November 2025 GMT
A ranar Alhamis, 20 ga watan Nuwamban 2025, ake sa ran Majalisar Wakilan Amurka za ta gudanar da zama na musamman domin bincikar zargin yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Nijeriya.
Kwamitin Majalisar Wakilan kan Afirka ya sanya ranar domin bitar fasalin da Shugaba Donald Trump ya yi kwanan nan na sanya Nijeriya a matsayin kasar da ake sa wa ido na musamman, CPC, kan zargin cewa ana yi wa Kiristoci kisan kiyashi.
Gidan Talabijin na Channels ya ruwaito cewa, an gayyaci mambobin Kwamitin Harkokin Waje na majalisar, wanda aka shirya za a yi tattaunawar da misalin ƙarfe 11:00 na safe a Ɗaki mai lamba 2172 na Ginin Ofishin Gidan Rayburn, sannan kuma za a iya kalla ta intanet kai-tsaye, wanda wakili Chris Smith (R-NJ) ne zai jagoranta.
Za a gabatar da kwamitoci biyu na shaidu, ciki har da manyan jami’an Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka da shugabannin addinai na Nijeriya.
Gayyatar tana cewa, “Ana roƙonku da girmamawa da ku halarci zaman sauraron ƙararraki na Kwamitin Harkokin Waje da ƙaramin kwamiti kan Afirka zai gudanar da shi da ƙarfe 11:00 na safe a ɗaki mai lamba 2172 na ginin Ofishin Rayburn House.”
Trump ne ya fara sanya Nijeriya a matsayin kasae da ake sa wa ido na musamman, CPC a shekarar 2020, kafin magajinsa, Shugaba Joe Biden, ya cire ƙasar daga jerin sunayen bayan ya kayar da Trump.
Masu sauraron za su haɗa da Babban Jami’in Ofishin Harkokin Afirka, Jonathan Pratt, da Mataimakin Mataimakin Sakatare na Ofishin Dimokuradiyya, ’Yancin Dan’Adam, da Aiki, Jacob McGee.
Za a yi zaman tattaunawa ta biyu da Daraktan Cibiyar ’Yancin Addini, Ms Nina Shea; Bishop Wilfred Anagbe na Makurdi Catholic Diocese a Nijeriya; da Ms Oge Onubogu ta Cibiyar Dabaru da Nazarin Ƙasashen Duniya.
Ana sa ran zaman tattaunawa ta majalisar zai sake duba girman zargin cuzguna wa masu wani addini a Nijeriya.
Za a kuma yi nazarin irin martanin manufofi da za a iya ɗauka, ciki har da takunkumin da aka yi niyyar ƙaƙabawa da taimakon jinƙai, da haɗin gwiwa da hukumomin Nijeriya don hana ƙarin tashin hankali.
Za a kuma gabatar da ƙudirin a gaban Majalisar Dattawan Amurka, wanda Sanata Ted Cruz ya ɗauki nauyinsa.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Nijeriya
এছাড়াও পড়ুন:
AU ta sake nanata cewa “Babu kisan kare dangi a arewacin Najeriya
Shugaban Kwamitin Tarayyar Afirka ya yi watsi da zargin da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi cewa ana wa Kiristoci kisan kare dangi a arewacin Najeriya.
Da yake jawabi a wani taron Majalisar Dinkin Duniya a New York, ya ce irin wadannan kalamai kan iya gurbata matsalolin tsaro mai sarkakiya.
Da yake magana tare da Sakataren Majalisar Dinkin Duniya António Guterres a ranar Alhamis, Mahmoud Ali Youssouf ya jaddada cewa Tarayyar Afirka ta riga ta fayyace matsayinta kuma ta yi kira da a yi taka tsantsan a cikin harshen da ake amfani da shi wajen bayyana rikice-rikicen da ke faruwa a nahiyar.
“Babu kisan kare dangi a arewacin Najeriya,” in ji Youssouf. “Mun fitar da wata sanarwa a fili da ke nuna cewa abin da ke faruwa a arewacin Najeriya ba shi da alaka da ta’addancin da muke gani a Sudan ko a wasu sassan gabashin DRC.”
Musulmai da Kiristoci, dukkansu abin ya shafa inji shi…
Ya kara da cewa tashin hankalin da ake yi a arewacin Najeriya, wanda galibi kungiyoyin ta’addanci na Boko Haram da ISIS a Yammacin Afirka ke haifarwa, ya shafi Musulmai da Kiristoci.
“Ina ganin lamarin arewacin Najeriya ya kamata mu yi taka tsantsan kafin mu yi irin wadannan kalamai,” in ji Youssouf.
“Musulmai ne suka fara shan wahala a hannun Boko Haram, ba Kiristoci ba, kuma ina faɗin haka ne bisa bayanai da muke dasu.”
A kwanan baya ne shugaba Trump na Amurka ya bayyana cewa zai doki matakin soji a Najeriya bisa zargin cewa gwamnatin kasar na kauda kai a game da kisan da y ace ana wa Kiristoci a kasar batun da Najeriya ta musanta.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Falasdinu ta yi wasan sada zumunci a Spain November 16, 2025 Amurka Ta Yi Gwajin Makaman Nukiliya A Watan Ogusta November 15, 2025 Adadin Ma’adanin “Colbat” Da DRC Ta Bai Wa Duniya Ya Kai Ton 1,000 November 15, 2025 Ma’ariv: Netanyahu Yana Tsoron Hukuncin Da Kotu Za Ta Yanke Akansa November 15, 2025 An Bayyana Sunayen Kasashen Da Su Ka Fi Sayar Wa “Isra’ila” Man Fetur A Lokacin Yakin Gaza November 15, 2025 MDD: Mutane 100,000 Ne Su Ka Fice Daga Birnin Al-Fasher Na Kasar Sudan November 15, 2025 Jakadan Iran A Majalisar Dinkin Duniya Yace Iran Ba za Ta Taba Mika Wuya Ga Duk Wata Barazana Ba November 15, 2025 Kasashen Latin Amurka Sun Shirya Tsaf Don Mayar Da Martani Kan Wuce Gona Da Irin Amurka Kan Venuzuwela November 15, 2025 Rasha Tace Bata Da Shirin Kai wa Kungiyar Nato Hari Amma Za ta Mayar Da Martani Kan Duk Wata Barazana November 15, 2025 Shugaban Iran Da Prime Ministan Iraqi Sun Tattaunawa Kan Batun Zabe Da Kuma Alakar Dake Tsakaninsu. November 15, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci