HausaTv:
2025-11-16@19:52:36 GMT

DRC: An Kulla Yarjejeniyar Zaman Lafiya A Tsakanin Gwamnati Da Kungiyar M23

Published: 16th, November 2025 GMT

Gwamnatin kasar ta DRC da kuma kungiyar ‘yan tawaye ta M23 sun rattaba hannu akan wasu takardu da su ka kunshi yadda za a kai ga samun zaman lafiya mai dorewa a gabashin kasar.

A jiya Asabar ne dai bangarorin biyu su ka rattaba hannu akan  takardun a birnin Doha na kasar Qatar domin kawo karshe fadace-fadacen da ake yi a gabashin kasar da ya ci rayukan dubban mutane da kuma tilastawa wasu yin hijira a cikin shekara daya kacal.

Karamin ministan harkokin wajen kasar Katar Muhammad Bin Abdulaziz Al-Khulaifi ya ce, rattaba hannu da bangarorin biyu su ka yi share fage ne zuwa ga zaman lafiya.

Haka nan kuma ya ce; Shi zaman lafiya ba a iya tilasta shi ta hanyar amfani da karfi,sai dai ta fahimtar juna.”

Sai dai kuma duk da cewa ana tattaunawar zaman lafiya a tsakanin banbarorin biyu a kasar Katar, fadan da ake yi a can gabashin DRC bai tsaya baki daya ba. A ranar juma’ar nan da ta shude ma dai an kashe mutane 28 a wani hari da kungiya mai ikirarin jihadi ta kai a Kivu ta Arewa.

A cikin watan Janairu na wannan shekarar ne dai kungiyar ta M23 ta shimfida ikonta a cikin birnin Goma da shi ne mafi girma a gabashin kasar, daga can kuma ta kame yankunan Kivu ta Arewa da ta kudu.

Gwamnatin Kinshasha dai tana tuhumar makwabciyarta Rwanda da taimakawa kungiyar ta M23 da makamai da kuma mayaka. Sai dai Rwanda ta sha musanta zargin.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka An Yi Kira A Bai Wa ‘Yan Hijira Saboda Sauyin Muhalli November 16, 2025  An Amince Da  Sauye-sauye A Tsarin Mulkin Kasar Benin November 16, 2025 Isra’ila Ta Kai Wa Sojojin MDD Hari A Kasar Lebanon November 16, 2025 Makiya Sun Kulla Makirci kan Kasar Labanon Irin Wanda Suka Kulla Kan Siriya November 16, 2025  Kasar Afghanistan Na Kokarin Karkata Akalar Kasuwancinta Zuwa Iran November 16, 2025 Kanada Ta Tsare Tsohon Wakilin Majalisar Dinkin Duniya Mai Bincike Kan Laifukan Yakin Israila.   November 16, 2025  Zarfi: HKI Ce Kawai Take Ayyana Nukiliya Ba Bisa Kaida Ba A Yammacin Asiya. November 16, 2025 Shugaban kasar venuzuwela Yayi Tir Da Atisayan Soji Da Trinidad and Tobago Ke yi. November 16, 2025 IRGC ta kama wani jirgin ruwan dakon mai a gabar tekun kudancin Makran November 16, 2025 Iran : sojojin Amurka a yankin Caribbean barazana ne ga zaman lafiya  November 16, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: zaman lafiya

এছাড়াও পড়ুন:

Shugaban kasar venuzuwela Yayi Tir Da Atisayan Soji Da Trinidad and Tobago Ke yi.

Shugaban kasar venuzuwela Nicolas Maduro yayi suka game da atisayan soji  da Trinidad an Tobago ke yi, kuma ya bayyana shi a matsayin abin da bai dace ba kuma yana barazana ga zaman lafiyar yankin Caribbean.

Atisayan sojin yana kara tada hankali tsakanin kasar venuzuwela da daya daga cikin makwabciyarta ta kurkusa adaidai lokacin da ayyukan sojojin Amurka a yankin karebiya ya jefa yanki cikin zaman dar-dar.

Kasar Trinidad and Tobago ta tsara fara gudanar da atisayin soji na hadin guiwa a cikin ruwan dake kusa da kasar venuzuwela daga ranar 17 zuwa 20 ga watan nuwamba, atisayan yazo daidai da ayyukan tsaro da Amurka ke jagoranta a yankin karebiya wandaAamurka tace ya shafi yaki da masu safarar miyagun kwayoyi ne.

Sai dai maduro ya bayyana rashin amicewarsa da daukarsa a matsayin wasu dabarun ne na boye, na gurgunta gwamnatinsa.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka IRGC ta kama wani jirgin ruwan dakon mai a gabar tekun kudancin Makran November 16, 2025 Iran : sojojin Amurka a yankin Caribbean barazana ne ga zaman lafiya  November 16, 2025 Lebanon za ta kai karar Isra’ila a MDD kan gina Katanga a iyakarta November 16, 2025 AU ta sake watsi da ikirarin Trump cewa ana kashe Kiristoci a Najeriya November 16, 2025 Falasdinu ta yi wasan sada zumunci a Spain November 16, 2025  Amurka Ta Yi Gwajin Makaman Nukiliya A Watan Ogusta November 15, 2025 Adadin Ma’adanin “Colbat” Da DRC Ta Bai Wa Duniya Ya Kai Ton 1,000 November 15, 2025 Ma’ariv: Netanyahu Yana Tsoron Hukuncin  Da Kotu  Za Ta Yanke Akansa November 15, 2025  An Bayyana Sunayen Kasashen Da Su Ka Fi Sayar Wa “Isra’ila” Man Fetur A Lokacin Yakin Gaza November 15, 2025 MDD: Mutane 100,000 Ne Su Ka Fice Daga Birnin Al-Fasher Na Kasar Sudan November 15, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Makiya Sun Kulla Makirci kan Kasar Labanon Irin Wanda Suka Kulla Kan Siriya
  •  Kasar Afghanistan Na Kokarin Karkata Akalar Kasuwancinta Zuwa Iran
  • Shugaban kasar venuzuwela Yayi Tir Da Atisayan Soji Da Trinidad and Tobago Ke yi.
  • Iran : kasantuwar sojojin Amurka a yankin Caribbean barazana ce ga zaman lafiyar duniya  
  • Rasha Tace Bata Da Shirin Kai wa Kungiyar Nato Hari Amma Za ta Mayar Da Martani Kan Duk Wata Barazana
  • Gaza: Amurka na matsin lamba ga kwamitin tsaro don amincewa da shirin zaman lafiya na Trump
  • AU da MDD, sun karfafa dabarun tabbatar da zaman lafiya da tsaro
  • Ana Samun Kwararar ‘Yan Hijira Daga Mali Zuwa Kasar Cote De Voire
  • Tehran da Ankara sun jaddada muhimmancin zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin