FG Za Ta Raba Naira miliyan 3.4m Ga Wadanda Suke Amfana Da Shirin ACReSAL
Published: 5th, August 2025 GMT
Gwamnatin tarayya ta ce tace a shirin ta sauya wuraren dake bushe a sassan arewacin Nijeriyaza a raba naira miliyan miliyan 3.4 kuma akasarin wadanda zasu amfana da wannan za su kasance mata ta hanyar Shirin ACReSAL.
Da yake jawabi a wajen bude taron kwanaki 10 na masu ruwa da tsaki kan tsarin kula da tsare-tsare (SCMP) na sabbin magudanan ruwa guda 11 a fadin Jihohi bakwai na tarayya a Ilorin, kodinetan ayyukan ACRESAL na kasa, Mista Abdulhamid Umar, ya ce za a gudanar da aikin ne ta hanyar shirin kawo sauyi na dogon lokaci.
Jami’in kula da ayyukan na kasa na ACRESAL Adamu Shettima wanda ya samu wakilcin kwararre a bangaren kula da ayyukan ruwa na gwamnatin tarayya, Adamu Shettima, ya bayyana cewa aikin yana da nasaba da dawo da martabar yankuna da suke bushe, daidaita yanayin muhalli da kuma karfafa miliyoyin al’umma a fadin Arewacin Najeriya.
Umar ya bayyana cewa bankin duniya ne ke taimaka wa aikin ta hannun kungiyar ci gaban kasa da kasa (IDA), ya kara da cewa wannan shi ne karon farko da gwamnatin tarayya ke samar da tsarin kula da ruwa mai girman irin wannan.
Ya yi nuni da cewa, dabarun da masu ruwa da tsaki za su mayar da hankali wajen yin mu’amala da masu ruwa da tsaki a dabarun da suka shafi Kwara, mai masaukin baki, Kaduna, Kebbi, Zamfara, Niger da FCT.
A nata jawabin, kwamishiniyar muhalli ta jihar Kwara, Hajia Nafisat Musa Buge, ta bayyana cewa hadakar masu ruwa da tsaki na daga cikin shirin inganta sha’anin ruwa, da inganta yanayin da ake ciki, da inganta rayuwa mai ɗorewa a yankunan da ke fama da wannan matsala a Najeriya.
Kwamishinan, ta ce sabon Shirin zai kasance ne tsakanin jihohi shida na Najeriya.
A nasa jawabin, Ko’odinetan shirin ACRESAL na jihar Kwara, Alhaji Shamsideen Aregbe, ya bukaci a hada kai da masu ruwa da tsaki wajen samar da tsare-tsare na kula da ruwan.
COV/ALI MUHAMMAD RABIU
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Kwara masu ruwa da tsaki
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Uba Sani Ya Bayyana Tsare-tsaren Ci Gaban Kaduna a Taron Duniya a Dubai.
Daga Abdullahi Shettima
Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya wakilci Nijeriya a taron ƙoli na biranen Asiya da ya gudana a ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), inda ya gabatar da kudirorin sauyin ci gaban Kaduna.
Taron ya samu halartar manyan baki daga ƙasashe sama da 150, ciki har da gwamnoni, shugabannin birane da jagororin kasuwanci daga Asiya, Fasifik, Turai da Afirka. Taken taron shi ne “Haɗin Gwiwa. Ƙarfafawa. Sauyi.”
A jawabinsa mai taken “Gina Haɗin Gwiwa Domin Ci Gaban Kowa,” Gwamna Uba Sani ya bayyana yadda Kaduna ke samun nasara a fannoni da dama kamar gyaran birane, bunƙasa noma da tallafawa jama’a. Ya ce tsarin ci gaban jihar yana dogara ne kan faɗaɗa damar tattalin arziki, kare marasa ƙarfi, da ƙarfafa jama’a su cim ma nasara a rayuwarsu.
Haka kuma, ya halarci baje kolin birnin Dubai mai taken “Sauya Arewa a Nijeriya: Jagoranci, Ƙirƙira da Tasirin Zamantakewa,” inda ya jaddada muhimmancin jagoranci mai nagarta da amfani da fasaha wajen buɗe damarmaki ga al’umma.
A yayin taron, Gwamnan ya gudanar da ganawa ta musamman da Marwan Bin Galita, Darakta-Janar na birnin Dubai, inda suka tattauna batutuwan kirkirar makamashin sharar gida, kula da sharar zamani, da tsare-tsaren gine-ginen birane na zamani.
Duk ɓangarorin biyu sun amince da zurfafa haɗin kai a fannin fasaha da musayar ƙwarewa domin tallafawa sauyin tattalin arzikin Kaduna zuwa mai ɗorewa.
Gwamna Sani ya bayyana cewa halartar Kaduna a taron (APCS 2025) na nuna shirin jihar na shiga sahun gaba wajen yin haɗin kai, ƙirƙira da zama abin koyi a fannin ci gaba mai ɗorewa — a Najeriya da duniya baki ɗaya.
Karshe.