Aminiya:
2025-11-18@17:52:54 GMT

Barau FC ta doke Enugu Rangers a Firimiyar Najeriya

Published: 18th, November 2025 GMT

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barau FC ta doke Enugu Rangers da ci 2-0 a wasan mako na 13 na Firimiyar Najeriya da suka buga a filin wasa na Sani Abacha da ke Kofar Mata a Jihar Kano.

Umar Bala Mohammed ne ya fara zura ƙwallo ta farko a minti na 25, kafin Joseph Kemin ya ƙara ta biyu a minti na 72 bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.

HOTUNA: Fada ya barke a Hedikwatar Jam’iyyar PDP ’Yan bindiga sun sako mutane 45 bayan sulhu a Katsina

Wannan nasarar ce ta uku da Barau FC ta yi cikin wasanni 12 da ta buga a kakar bana, inda ta yi kunnen doki a wasanni huɗu, aka kuma doke ta a biyar.

Yanzu haka Barau FC ta hau mataki na 16 a teburin gasar da maki 13, yayin da Enugu Rangers kuwa ta koma mataki na 14.

A gobe Laraba, Barau FC za ta kece raini da Rivers United a kwantan wasan mako na biyar da za a buga a filin wasa na Sani Abacha.

A wani kwantan wasan mako na biyar, Kano Pillars za ta yi tattaki zuwa filin wasa na Remo Stars domin ɓarje gumi.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Barau FC Firimiyar Najeriya Kano Pillars Rangers Barau FC ta

এছাড়াও পড়ুন:

CAF ta fitar da ’yan wasa uku da suka rage a takarar gwarzon Afirka na bana

Hukumar ƙwallon ƙafar Afirka CAF, ta bayyana cewa bayan tankade da rairaya da ta yi, a yanzu ’yan wasa uku kacal ne suka rage a takarar gwarzon nahiyyar na bana.

A wata sanarwar da hukumar ta fitar a ranar Lahadi, ta bayyana Achraf Hakimi da Mohamed Salah da Victor Osimhen, a matsayin sauran ukun da suka rage a takarar gwarzon dan ƙwallon ƙafar Afirka na bana.

Gobara ta laƙume rayukan yara biyu ’yan gida ɗaya a Ribas Mayaƙan ISWAP sun kashe kwamandan soji a Borno

Hakimi, kyaftin din Morocco, ya lashe kofuna daga ciki har da Champions League a PSG — na farko a tarihin ƙungiyar — da Ligue 1, da European Super Cup, da kuma kai wa zagayen ƙarshe a FIFA Club World Cup da Chelsea ta lashe a Amurka.

Shi kuwa Mohammed Salah ya taka rawar gani a Liverpool a kakar da ta wuce da lashe Premier League, kuma shi ne kan gaba a zazzaga kwallaye mai 29 da bayar da 18 aka zura a raga, hakan ya sa ya karbi kyautar takalmin zinare, wato Golden Boot.

Mohammed Salah dan ƙasar Masar mai shekara 33 na fatan karbar kyautar gwarzon Afirka karo na uku bayan 2017 da kuma 2018.

Shi kuwa dan ƙwallon tawagar Super Eagles ta Najeriya, Victor Osimhen ya jagoranci Galatasaray ta dauki babban kofin tamaula na Turkiya da cin ƙwallo 26.

Osimhen ya taba zama gwarzon Afirka 2023 a lokacin da shi kuma Hakimi ya yi na biyu

To sai dai mai riƙe da kyautar a yanzu, wato Ademola Lookman na Nijeriya, bai kai bante ba a kakar nan sakamakon gaza taka rawar gani yadda ake buƙata.

Za a gudanar da bikin karrama gwarzon dan ƙwallon ƙafa na Afirka na bana ranar Laraba a birnin Rabat na Morocco.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • CAF ta fitar da ’yan wasa uku da suka rage a takarar gwarzon Afirka na bana
  • Shugaban Nukiliyar Iran Yace Amurka Da Israila Sun Shiga Sabon Mataki Mai Hadari
  • Nukiliya : Iran zata sake duba huldarta da IAEA idan aka dauki wani sabon mataki kanta
  • Najeriya ba za ta buga kofin duniya ba karo na biyu a jere
  • NAJERIYA A YAU: Matsayar Doka Kan Taron Da Jam’iyyar PDP Ta Gudanar
  • Yadda Za A Magance Yawan Faɗace-faɗace A Wasannin Gasar Firimiyar Nijeriya
  • Falasdinu ta yi wasan sada zumunci a Spain
  • Hukumar Kwallon Kafa Ta Kasar Turkiyya Ta Dakatar Da ‘Yan Wasa 1024 Saboda Laifin Caca
  • Ina Son Kasancewa Cikin Koshin Lafiya Kafin Buga Gasar Kofin Duniya Na Shekarar 2026 – Messi