A wani labari da kungiyar “ISWAP” mai alaka da “Isis” ta watsa, ta sanar da kashe wani babban jami’in sojan Najeriya a wani kwanton bauna da ta yi wa sojoji a kusa da kauyen Wajiroko dake Jahar Borno a ranar Juma’ar da ta gabata.

Sanarwar kungiyar ta “Isis” ya kuma kunshi cewa, baya ga Birgediya  janar Uba da su ka kashe, sun kuma kashe wasu sojojin 4.

Kamfanin dillancin labarun “Reuters” da ya tuntubi rundunar sojan kasar ta Najeriya domin samun Karin bayani akan abinda ya faru bai sami jawabi ba.

Sai dai rundunar sojan ta Najeriya ta ce labarin da ake watsawa na kama babban jami’i mai mukamin janar, ba gaskiya ba ne, kuma bai kamata ‘yan kasa su gaskata shi ba.

Mayakan kungiyar ta “Iswap” sun buga a shafinsu mai suna “A’amaq” cewa, sun kashe jami’in sojan, a wani kwanton bauna da su ka yi .

Jahar Borno tana fada da matsalar masu dauke da makamai da suke ikirarin jihadi, tun daga 2009, wanda ya zuwa yanzu ya ci rayukan dubban mutane da kuma mayar da wasu zama ‘yan hijira nesa da gidajensu.

Ita dai kungiyar “Iswap” ta balle daga Bokoharam, bayan da su ka sami sabani, da a karshe ya kai ga kashe magudun kungiyar Abubakar Shekau.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Najeriya ta Fara tattaunawa da Amurka kan zargin yi wa Kiristoci kisan kiyashi November 18, 2025 Hamas Ta yi Watsi Da Amincewa Da Kudurin Amurka Da Kwamitin Tsaro Ya yi Kan Gaza November 18, 2025 Afrika ta Kudu Ta yi Gargadi Game Da Duk Wani Yunkuri Na Fitar Da Falasdinawa Daga Yankin Gaza November 18, 2025 Tsohon jami’an MDD Yayi Tir Da Amincewa Da Kudurin Amurka A Kwamitin Sulhu Kan Gaza November 18, 2025 Mataimakin Shugaban Iran Na Daya Ya Gana Da Prime Ministan Rasha A Birnin Mosko November 18, 2025 Ministan tsaron Iran na Ziyara a UAE don karfafa dangantakar tsaro tsakanin kasashen yankin November 18, 2025 Masu shigar da kara na ICC sun bukaci hukuncin daurin rai da rai a kan kwamandan RSF November 18, 2025 MDD ta amince da kudurin tura dakarun kasa da kasa zuwa Gaza November 18, 2025 Congo ta tsawaita haramcin fataucin ma’adinai a gabashin kasar November 18, 2025 Rasha: An dakile wani yunkurin kisan gilla kan Sakataren Majalisar Tsaron kasa November 18, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Mayaƙan ISWAP sun kashe kwamandan soji a Borno

Mayaƙan ƙungiyar ISWAP sun kashe wani babban kwamandan rundunar sojin Najeriya bayan wani harin kwantan ɓauna da aka kai wa tawagarsa a hanyar Damboa–Biu da ke Jihar Borno.

Lamarin ya faru ne bayan da tawagar sojojin tare da dakarun haɗin gwiwa na Civilian Joint Task Force (CJTF) suka kai wani samame a yankin, inda suka gamu da harin ba-zata na ’yan ta’adda.

’Yan sanda sun kama ƙunshi 66 na Tabar Wiwi a Gombe Hauhawar farashi ya ƙara raguwa a Nijeriya — NBS

Kwamandan, wanda daga baya aka bayyana sunansa a matsayin Brigade Commander M. Uba, shi ne ya jagoranci rundunar da ta kai ɗauki ga wasu sojoji da suka yi ɓatan hanya kafin su faɗa tarkon mayaƙan ISWAP.

PRNigeria ta ruwaito cewa, kafin rasuwarsa, kwamandan ya aike da wani bidiyo ga manyansa yana bayyana irin nasarar da tawagarsa ta samu a wani farmaki da suka kai.

Sai dai bayan haka ne ISWAP ta bibiyi wurin da yake ta katse sadarwa, sannan ta kama shi.

Rahotanni sun ce mayaƙan sun kama shi ne da ransa, inda bayan sun yi masa tambayoyi, daga bisani kuma su kashe shi.

Da farko dai rundunar sojin Najeriya ta ce kwamandan yana cikin ƙoshin lafiya bisa hujjar bidiyon da ya aika yana tabbatar da irin nasarar da suke samu.

Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar sojin ƙasa, Laftanar Kanar Appolonia Anele, ta bayyana batun cafke kwamandan nata a matsayin “ƙazon kurege”, tana mai cewa duk da “harbe-harbe masu tsanani” da suka fuskanta daga mayaƙan yayin dawowarsu daga sintiri a gefen Sambisa, an yi nasarar tsira da kwamandan.

Sanarwar ta tabbatar da mutuwar sojoji biyu da jami’an sa-kai biyu a harin, amma ta ce kwamandan ba ya cikin waɗanda aka kama.

Sai dai daga bisani, wasu rahotanni na PRNigeria da jaridar PREMIUM TIMES sun tabbatar da cewa mayaƙan ISWAP sun kama kwamanda ne bayan ya yi ɓata hanya yayin guje wa harin farko.

ISWAP ta yi iƙirarin kashe kwamandan

A wata sanarwa cikin harshen Larabci da ISWAP ta wallafa ranar Litinin a jaridarta mai suna Amaq, ta nuna hoton kwamandan a lokacin da ya ke hannunta, yana fama rauni har jini na zuba a kafarsa.

Ƙungiyar ta ce: “Mun kama kwamandan rundunar Najeriya bayan ya tsere daga harin Wajiroko, daga nan muka yi masa tambayoyi sannan muka kashe shi.”

Ƙungiyar ta kuma yi wa rundunar sojin Najeriya gugar zana, tana mai bayyana bayanan farko da ta fitar a matsayin “ƙarya tsagwaronta da ke tabbatar da gazawarta.”

Kawo yanzu dai Rundunar Sojin Najeriya ba ta fitar da sanarwa a hukumance ba, amma majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa ana gudanar da bincike kan yadda aka bar kwamandan cikin haɗari bayan tserewa daga harin farko.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Lebanon: Mutum Daya Ya Yi Shahada Sanadiyyar Harin Sojojin “Sahayoniya A Garin Bint-Jubail
  • Najeriya ta Fara tattaunawa da Amurka kan zargin yi wa Kiristoci kisan kiyashi
  • Mayaƙan ISWAP sun kashe kwamandan soji a Borno
  • Na’im Dassim: Gwamnatin Lebanon Zata Yi Babban Kuskure Matukar Tabi Hanyar Sassauci
  • Rushewar Ramukan Hako Ma’adinai Ta Kashe Mutane 32 A Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango
  • Sojojin HKi Sun Kashe Wasu Falasdinawa Guda 2 A Sansanin Yan Gudun Hijira
  • Najeriya ba za ta buga kofin duniya ba karo na biyu a jere
  • Ɗan Najeriya ya kashe mahaifinsa, ya yanki ƙannensa da wuƙa a Amurka
  • AU ta sake nanata cewa “Babu kisan kare dangi a arewacin Najeriya