Ana Mai Da Hankali Kan Dabarun Kasar Sin A Fannin Tinkarar Sauyin Yanayin Duniya A Taron COP30
Published: 16th, November 2025 GMT
Yanzu haka ana gudanar da taron bangarorin da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar tinkarar sauyin yanayin duniya ta Majalisar Dinkin Duniya, karo na 30, wato “COP 30” a takaice, a birnin Belem na kasar Brazil, inda a ranar Juma’a 14 ga wata aka kira wani taro a gefe mai taken “Dabarun Kasar Sin Na Tinkarar Sauyin Yanayin Duniya”, don bayar da fasahohin Sin a fannin daidaita al’amura a kokarin sabawa da sauyin yanayi.
A wajen taron, shugaban tawagar kasar Sin a taron COP30, kana mataimakin ministan muhallin halittu na kasar, Li Gao, ya ce sauyin yanayin duniya wani babban kalubale ne da daukacin bil Adama ke fuskantarsa, inda a nata bangare, kasar Sin ta tsaya kan mai da hankali kan dukkan bangarorin dakatar da sauyin yanayi, da kokarin sabawa da shi. Kana kasar tana gudanar da gwaje-gwaje a biranenta 39 ta fuskar daidaita tsare-tsare don sabawa da sauyin yanayin duniya. Ban da haka, jami’in ya ce, kasar Sin na son karfafa hadin gwiwa tare da sauran kasashe, a kokarin tinkarar sauyin yanayi, da inganta fannin sabawa da sauyin yanayin duniya a kasashe daban daban.
Duk dai a wajen taron, Francesco Corvaro, wakilin kasar Italiya mai kula da batun sauyin yanayi, ya yi yabo ga kasar Sin bisa nasarorin da ta samu a kokarin sabawa da sauyin yanayin duniya, inda ya ce ci gaban da kasar Sin ta samu ya nuna makomar aikin tinkarar sauyin yanayi a duniya, kuma yana sa ran ganin Sin ta zama tamkar wata gada mai hada dukkan bangarorin kasashe masu tasowa da masu sukuni, ta yadda za a tabbatar da hadin gwiwar daukacin bil Adama a kokarin tinkarar sauyin yanayin duniya. (Bello Wang)
ADVERTISEMENT ShareTweetSendShare MASU ALAKAকীওয়ার্ড: tinkarar sauyin yanayin duniya sabawa da sauyin yanayi tinkarar sauyin yanayi
এছাড়াও পড়ুন:
Kasar Afghanistan Na Kokarin Karkata Akalar Kasuwancinta Zuwa Iran
Gwamntin daliban ta kasar Afghnistan ta sanar da sauya akalar harkokin kasuwancinta ta hanyar iran da tsakiyar asiya, domin rage dogaro da kasar Pakistan a lokacin da zaman tankiya ya kara Kamari tsakanin makwabtan guda biyu da ya kai ga rufe iyakokinsu.
A wani yunkuri na kewaye kasar Pakistan da kuma kaucewa matsalolin da ake samu a iyakarta da Pakistan, kasar Afghanistan ta kara yawan lokacin aikewa da kayayyakinta zuwa tashar jigin ruwa ta chabahar ta kasar iran.
Kakakin ma’aikatar kasuwanci ta kasar Afghanistan Abdus salam Jawad Akhundaze Ya ce a tsawon watanni 6 kasuwancinsu da iran ya kai dala biliyan 1.6. fiye da dala biliyan 1 na kayayyakin da take fitarwa ta hanyar Pakistan .
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kanada Ta Tsare Tsohon Wakilin Majalisar Dinkin Duniya Mai Bincike Kan Laifukan Yakin Israila. November 16, 2025 Zarfi: HKI Ce Kawai Take Ayyana Nukiliya Ba Bisa Kaida Ba A Yammacin Asiya. November 16, 2025 Shugaban kasar venuzuwela Yayi Tir Da Atisayan Soji Da Trinidad and Tobago Ke yi. November 16, 2025 IRGC ta kama wani jirgin ruwan dakon mai a gabar tekun kudancin Makran November 16, 2025 Iran : sojojin Amurka a yankin Caribbean barazana ne ga zaman lafiya November 16, 2025 Lebanon za ta kai karar Isra’ila a MDD kan gina Katanga a iyakarta November 16, 2025 AU ta sake watsi da ikirarin Trump cewa ana kashe Kiristoci a Najeriya November 16, 2025 Falasdinu ta yi wasan sada zumunci a Spain November 16, 2025 Amurka Ta Yi Gwajin Makaman Nukiliya A Watan Ogusta November 15, 2025 Adadin Ma’adanin “Colbat” Da DRC Ta Bai Wa Duniya Ya Kai Ton 1,000 November 15, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci