Aminiya:
2025-11-16@18:19:54 GMT

Gwamnatin Gombe ta bai wa alƙalai da Khadi-Khadi kyautar sabbin motoci 16

Published: 16th, November 2025 GMT

Gwamnatin Jihar Gombe ta raba sabbin motoci ƙirar SUV guda 16 ga Alƙalai na Babbar Kotu da Khadi-Khadi na Kotun Shari’a domin taimaka musu wajen gudanar da aikinsu yadda ya kamata a fadin jihar.

Motocin sun haɗa da motoci biyu ƙirar Toyota SUV samfurin 2025 da aka bai wa babban alƙal8 da Grand Khadi.

Na kusa komawa APC – Gwamnan Taraba Tsohon Minista Kabiru Turaki ya zama sabon shugaban PDP na ƙasa

Motocin guda 14 ƙirar GAC SUV samfurin 2025 da aka raba wa sauran alƙalai da khadi-khadi.

Da yake miƙa motocin, Mataimakin Gwamna Mannasah Daniel Jatau, ya ce gwamnatin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na ƙoƙari wajen samar da kayan aiki na zamani domin inganta ayyukan gwamnati, musamman a ɓangaren shari’a.

Ya ce gwamnati na magance matsalolin da ta gada, ciki har da biyan fansho da biyan albashi a kan lokaci.

Ya kuma yi kira ga waɗanda aka bai wa motocin da su yi amfani da su wajen gudanar da ayyukansu.

A nasa jawabin, Kwamishinan Kuɗi, Muhammad Gambo Magaji, ya bayyana cewa an kashe sama da Naira biliyan biyu wajen sayen motocin.

Ya ce tsawon sama da shekaru 10 ɓangaren shari’a bai samu sabbin motocin aiki ba.

Kwamishinan Shari’a, Barista Zubair Muhammad Umar, ya ce rabon motocin wani ɓangare ne na cika alƙawarin gwamnati na inganta ɓangaren shari’a.

Ya tunatar da cewa aikin gina sabon ginin Babbar Kotu na kimanin Naira biliyan 16 na ci gaba da gudana.

A jawabinsa na godiya, Babban Magatakardar Babbar Kotu, Barista Bello Shariff, ya yaba wa gwamnatin jihar bisa goyon bayan da ta ke bai wa bangaren shari’a.

Ya bayyana cewa za su yi amfani da motocin ta hanya mai kyau domin inganta ayyukansu.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Gwamnatin Gombe kyauta

এছাড়াও পড়ুন:

Ɗalibar BUK ta ci kyautar motar N35m a gasar MTN

Ɗalibar Aji uku a Sashen Nazarin Harkar Noma na Jami’ar Bayero ta Kano, Ramatu Yakubu, ta samu kyautar mota wadda kuɗinta ya kai Naira miliyan 35 a gasar da kamfanin MTN ya shirya a jami’ar.

Gasar wadda aka shafe kwanaki uku ana yi mai taken MTN “GoMAD on Campus,” wadda aka tsara domin tallafawa da nishaɗantar da ɗalibai ta hanyar wasanni, fasahar zamani da sauransu.

Cin ganda na sa Najeriya tafka asarar $5bn — Gwamnatin Tarayya Majalisar Wakilai ta dage lokacin fara yin jarabawar WAEC a kwamfuta zuwa 2030

Ramatu ta lashe manyan kyaututtuka bayan shiga gasa daban-daban, inda sauran ɗalibai ma suka samu kyautar kwamfuta, wayoyi da kuɗi.

Manajan Sashen Matasa na MTN a Najeriya, Femi Adesina, ya ce kamfanin na son tallafa wa matasa da ke karatu a manyan makarantu.

“Mun yadda da matasan Najeriya. Ba wai magana kawai muke ba, muna tare da su, muna goyon bayansu domin su zama nagartattu,” in ji shi.

Taron da aka yi a Kano ya ƙunshi rawa da waƙoƙi, wasannin kwamfuta da sauransu.

MTN ya kuma bai wa ɗalibai ’yan kasuwa 10 dandalin nuna kayayyakinsu ba tare da biyan kuɗi ba.

Ɗalibai sun bayyana taron a matsayin ɗaya daga cikin abubuwan da suka faranta musu rai a jami’ar, inda suka gode wa MTN saboda tallafin da suka samu.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Meke Kawo Yanke Hukunce-hukunce Masu Karo Da Juna Daga Kotuna?
  • Gwamnati, UNICEF da ’yan jarida sun haɗa don yaƙar cututtukan da aka manta da su a Gombe
  • Gwamnati na jefa makomar ilimi cikin hatsari — ASUU
  • Dalilin Asusun NADF Na Yin Hadaka Da Gwamnatin Jihar Jigawa
  • Ɗalibar BUK ta samu kyautar motar N35m a gasar MTN
  • Ɗalibar BUK ta ci kyautar motar N35m a gasar MTN
  • Bayan Barazanar Amurka: Sultan Ya Nemi Hadin Kan ‘Yan Nijeriya Wajen Yaki Da Ta’addanci
  • HOTUNA: NDLEA ta ƙone tan dubu 52 na miyagun ƙwayoyi a Zariya
  • Ina girmama sojojin Nijeriya — Wike