PDP Ba Ta Mutu Ba Duk Da Rikicin Da Ta Ke Fama Da Shi – Anyanwu
Published: 18th, November 2025 GMT
“Lokacin da Wike, Makinde, Ugwuanyi, Ikpeazu da Ortom suka kafa G5, bana are da su. Amma duk da haka, Wike abokina ne sosai. Lokacin da PDP ta samu matsala Wike ne ya yi ƙoƙarin tallafa mata,” in ji Anyanwu.
Ya ƙara da cewa Wike bai fice daga PDP ba.
Anyanwu ya kira taron gangamin PDP da aka yi a Ibadan a matsayin ɓata lokaci, yana mai cewa ba a yi sa bisa ƙa’ida ba.
Ya ce dakatar da shi daga matsayin Sakataren jam’iyyar na Ƙasa ba a kan ka’ida yake ba saboda jam’iyyar ba ta bi umarnin kotu ba.
Ya kuma ce taron bai haɗa jihohi da dama ba, don haka bai samu cikakken goyon baya ba.
A yayin babban taron na PDP na 2025, jam’iyyar ta kori Wike, tsohon gwamnan Ekiti Ayodele Fayose, Samuel Anyanwu da wasu, bisa zargin cin amanar jam’iyyar.
Haka kuma ta rushe shugabancin jam’iyyar a Imo, Abia, Enugu, Akwa Ibom da Ribas.
Bode George, wani jigo a jam’iyyar PDP ne, ya gabatar da ƙudirin korar manyan mambobin 11, kan zarginsu da gudanar da abubuwan suka saɓa wa dok6 jam’iyya.
Shugaban PDP na Jihar Bauchi ya mara masa baya.
ShareTweetSendShare MASU ALAKAএছাড়াও পড়ুন:
NAF Ta Ragargaza Mafakar Ƴan Ta’adda A Zamfara, Ta Halaka Dama
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Wasu Mahara Sun Kashe Mata 2, Tare Da da Ƙona Gidansu A Tudun Yola November 15, 2025
Manyan Labarai Shugaban APC Na Kano Ya Nemi Afuwa Daga Al’ummar Fagge Kan Kalamansa November 15, 2025
Da ɗumi-ɗuminsa Tsohon Gwamnan Anambra, Willie Obiano, Ya Rasu Yana Da Shekaru 70 November 14, 2025