Kwamitin tsaron MDD zai kada kuri’a kan daftarin kudirin Trump kan Gaza
Published: 17th, November 2025 GMT
A wani lokaci yau Litini ce kwamitin tsaro na MDD, zai kada kuri’a kan daftarin kudirin zaman lafiya na shugaban Amurka Donald Trump na Amurka kan Gaza.
Kafin hakan Amurka ta sha matsin lamba ga kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya don amincewa da daftarin kudurin na Trump.
Amurkar da wasu kawayenta na kasashen Larabawa sun yi kira ga Kwamitin Tsaron da ya “yi sauri” ya amince da daftarin kudurin wanda ya amince da shirin zaman lafiya na Donald Trump kan Gaza.
Qatar, Masar, Hadaddiyar Daular Larabawa, Masar, Indonesia, Pakistan, Jordan, da Turkiyya sun bayyana goyon bayansu ga daftarin kudurin na Amurka wanda ya tanadi kafa kwamiti da zai kula da gwamnatin rikon kwarya a Gaza da rundunar kasa da kasa a yankin Falasdinu, tare da fatan amincewa da shi cikin sauri,” in ji su a cikin wata sanarwa ta hadin gwiwa.
A ranar Alhamis, Amurka ta yi gargadi game da hadarin rashin amincewa da daftarin kudurin, Yayin da kasashen Larabawa ke nuna fargabar darewar yankin falasdinun gida biyu.
Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da wasu daga cikin ministocinsa sun sake nanata adawarsu ga kafa kasar Falasdinu kafin kada kuri’ar da za a yi yau Litinin kan daftarin kudurin kan Gaza, wanda ke nuna yiwuwar samar da kasar Falasdinu a nan gaba.
Kungiyoyin Falasdinawa sun yi watsi da daftarin kudurin wanda kuma ya tanadi shawarar tura dakarun kasashen waje kusan 20,000 zuwa Gaza, suna kira ga Aljeriya, wacce ba memba ce ta dindindin a kwamitin Tsaron, da ta yi watsi da shi.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Ansarullah Ta Yi Allah Wadai Da Sabunta Takunkumin MDD Kan Yemen November 17, 2025 Afirka ta Kudu na Binciken shigar wasu ‘yan gudun hijirar Falasdinu 153 cikin kasar November 17, 2025 Najeriya ba za ta buga kofin duniya ba karo na biyu a jere November 17, 2025 DRC: An Kulla Yarjejeniyar Zaman Lafiya A Tsakanin Gwamnati Da Kungiyar M23 November 16, 2025 An Yi Kira A Bai Wa ‘Yan Hijira Saboda Sauyin Muhalli Kariya November 16, 2025 An Amince Da Sauye-sauye A Tsarin Mulkin Kasar Benin November 16, 2025 Isra’ila Ta Kai Wa Sojojin MDD Hari A Kasar Lebanon November 16, 2025 Makiya Sun Kulla Makirci kan Kasar Labanon Irin Wanda Suka Kulla Kan Siriya November 16, 2025 Kasar Afghanistan Na Kokarin Karkata Akalar Kasuwancinta Zuwa Iran November 16, 2025 Kanada Ta Tsare Tsohon Wakilin Majalisar Dinkin Duniya Mai Bincike Kan Laifukan Yakin Israila. November 16, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: da daftarin kudurin
এছাড়াও পড়ুন:
Lebanon za ta shigar da kara a kan Isra’ila a MDD game da gina Katanga a iyakarta
Gwamnatin Beirut ta ce za ta shigar da kara a kan Isra’ila gaban Majalisar Dinikin Duniya game da gida katangar siminti a kan iyakar Kudancin Lebanon.
A cikin wata sanarwa data fitar fadar shugaban Lebanon ta sanar da cewa Beirut za ta shigar da kara a Majalisar Dinkin Duniya game da gina katangar.
Shugaban Lebanon Joseph Aoun ya umarci Ministan Harkokin Wajen kasar Youssef Radji da ya umurci tawagar Lebanon ta Dindindin a Majalisar Dinkin Duniya da ta shigar da karar gaggawa a kwamitin Tsaro kan gwamnatin Isra’ila saboda gina katangar siminti a kan iyakar kudancin Lebanon, wadda ta wuce ‘’Layi Shuɗi’’ da aka zana bayan janyewar Isra’ila a shekarar 2000.
Hukumomin Lebanon sun ce katangar simintin da sojojin Isra’ila suka gina ta hana mazauna kudancin Lebanon shiga wani yanki mai fadin murabba’in mita 4,000 na yankin Lebanon.
Wani bincike da Rundunar Wucin Gadi ta Majalisar Dinkin Duniya (UNIFIL) ta gudanar a watan Oktoba ya nuna cewa katangar da sojojin Isra’ila suka gina ta ratsa Layin Shuɗi, kamar yadda Stéphane Dujarric, kakakin Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, ya sanar a ranar Juma’a.
An kuma gina wani sashe na biyu na wata katangar a kudu maso gabashin kauyen Yaroun na Lebanon, kuma ita ma ta ratsa Layin Shuɗi.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran : kasantuwar sojojin Amurka a yankin Caribbean barazana ce ga zaman lafiyar duniya November 16, 2025 AU ta sake nanata cewa “Babu kisan kare dangi a arewacin Najeriya November 16, 2025 Falasdinu ta yi wasan sada zumunci a Spain November 16, 2025 Amurka Ta Yi Gwajin Makaman Nukiliya A Watan Ogusta November 15, 2025 Adadin Ma’adanin “Colbat” Da DRC Ta Bai Wa Duniya Ya Kai Ton 1,000 November 15, 2025 Ma’ariv: Netanyahu Yana Tsoron Hukuncin Da Kotu Za Ta Yanke Akansa November 15, 2025 An Bayyana Sunayen Kasashen Da Su Ka Fi Sayar Wa “Isra’ila” Man Fetur A Lokacin Yakin Gaza November 15, 2025 MDD: Mutane 100,000 Ne Su Ka Fice Daga Birnin Al-Fasher Na Kasar Sudan November 15, 2025 Jakadan Iran A Majalisar Dinkin Duniya Yace Iran Ba za Ta Taba Mika Wuya Ga Duk Wata Barazana Ba November 15, 2025 Kasashen Latin Amurka Sun Shirya Tsaf Don Mayar Da Martani Kan Wuce Gona Da Irin Amurka Kan Venuzuwela November 15, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci