’Yan sanda sun kama ƙunshi 66 na Tabar Wiwi a Gombe
Published: 17th, November 2025 GMT
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe ta kama ƙunshi 66 na ganyen tabar wiwi a wani samame da ta kai a garin Deba, bayan samun wasu sahihin bayanan leƙen asiri.
Mai magana da yawun rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:30 na dare a ranar 16 ga Nuwamba, 2025, lokacin da aka hango wata mota mara lamba, ƙirar Toyota Corolla, da ake zargi tana ɗauke da kayan, a kan hanyar Kuri zuwa Deba.
Aminiya ta ruwaito cewa, bayan isar jami’an wurin da ake zargin akwai kayan laifin ne, sun lura da wasu mutum uku suna ƙoƙarin yi wa wani mutum lodi a kan babur, lamarin da ya sanya ababen zargin suka tsere bayan hango ’yan sandan.
Binciken farko da aka gudanar ya kai ga gano buhuna uku ɗauke da ƙunshi 66 na ganyen da ake zargin tabar wiwi ce.
An dai kwashe kayayyakin zuwa ofishin ’yan sanda, kuma an fara bincike don kamo waɗanda suka tsere.
Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Gombe, CP Bello Yahaya, ya jinjina wa jami’an da suka gudanar da wannan aiki, yana mai tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da fatattakar masu safarar miyagun ƙwayoyi a faɗin jihar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: jihar Gombe Tabar wiwi
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan bindiga 5 Sun shiga hannun ’yan sanda a Kebbi
’Yan sanda sun yi nasarar kama wasu ’yan bindiga biyar tare da ƙwace tarin makamai a hannunsu a yankin Zuru–Tadurga da ke Jihar Kebbi.
Rundunar ’yan sanda ta musamman da ta kama su, ta bayyana cewa, ’yan bindiga suna cikin waɗanda suka kai hare-hare a kan al’ummomin Zuru a kwanakin baya.
Ta ƙara da cewa dukkansu ’yan asalin kauyen Birnin Tudu ne da ke cikin ƙananan hukumomin Bukkuyum da Gummi a Jihar Zamfara.
Kakakin ’yan sanda a jihar, CSP Nafiu Abubakar, ya ce makaman da aka ƙwato daga hannun ’yan bindigar sun haɗa bindigogi AK-47 guda 7 a wata ƙaramar gida guda 1 da harbi-ruga guda uku.
’Yan bindiga sun kashe mutum 3 sun sace 64 a Zamfara Da amincewar hukumomi nake tattaunawa da ’yan bindiga — Sheikh GumiSauran sun haɗa da kurtun albarusan AK-47 guda 3 da harsashi 89 da kuma tsabar kuɗi Naira miliyan 2.6
Ya ƙara da cewa an miƙa waɗanda ake zargin zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka (SCID) da ke Birnin Kebbi domin ci gaba da bincike da kuma gano sauran abokan aikinsu.
Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Kebbi, Bello M. Sani, ya yaba da jarumta da jajircewar jami’an rundunar tare da ƙarfafa su da kada su yi ƙasa a gwiwa har sai an kawar da matsalar ’yan bindiga da garkuwa da mutane daga jihar.