Aminiya:
2025-11-16@21:44:39 GMT

Da amincewar hukumomi nake tattaunawa da ’yan bindiga — Sheikh Gumi

Published: 16th, November 2025 GMT

Sheikh Ahmad Gumi ya yi martani kan kiraye-kirayen da ake yi na kama shi, inda ya ce masu yin kiran na yi ne domin kawar da rawar da yake takawa wajen magance matsalar ’yan bindiga a Arewa.

Gumi, ya ce duk ganawar da yake yi da ’yan bindiga yana yi ne domin samar da zaman lafiya, kuma hukumomin tsaro sun san da komai.

Ɗan Najeriya ya kashe mahaifinsa, ya yanki ƙannensa da wuƙa a Amurka Tsaro: Na kan yi kuka duk lokacin da na ji an kashe wani — Akpabio

Maganar ta sake fitowa fili ne bayan da ya sake jaddada cewa tattaunawa hanya ce da za ta iya kawo ƙarshen tashin hankali a karkara.

A cikin dogon saƙon da ya wallafa a Facebook a ranar Lahadi, Gumi ya soki masu cewa ya kamata a kama shi saboda ya ganawar da ya yi da shugabannin ’yan bindiga.

Ya bayyana kiran a matsayin don rai la’akari da irin ƙoƙarin da ya yi a baya domin daƙile matsalar tsaro a Arewa.

Ya ce ba shi niyyar goyon bayan masu laifi; kawai yana ƙoƙari rage tashin hankali da kuma shawo kan ’yan bindiga su miƙa wuya.

Gumi, ya ce ya yi muhimmin zama da mahara a Janairun 2021 a dajin Sabon Garin Yadi da ke Ƙaramar Hukumar Giwa a Jihar Kaduna.

Kuma ya ce tare da Kwamishinan ’Yan Sandan Kaduna ya je a lokacin d aka yi ganawar, wanda ya wakilci Sufeton ’Yan Sanda na Ƙasa.

Ya ce taron ya samu halartar ’yan bindiga da shugabanninsu sama da 600, kuma sun yi alƙawarin daina kai hare-hare idan gwamnati ta samar musu da wasu muhimman abubuwa.

“Na je dajin Sabon Garin Yadi tare da Kwamishinan ’Yan Sandan Kaduna.”

“Wannan zama ɓangare ne na aikin samar da zaman lafiya, inda muka yi wa ’yan bindiga sama da 600 da shugabanninsu wa’azi, suka kuma amince za su ajiye makamai idan gwamnati ta samar musu da tsaro da ingantaccen rayuwa,” in ji shi.

Gumi, ya ce duk abin da ya yi bisa ƙa’ida ya yi sa, kuma hukumomi sun san da komai.

Ya ce maimakon mutane su kai su soke shi, kamata ya yi su tambayi dalilin da ya sa gwamnati ba ta yi buƙatun ’yan bindiga ba.

Sheikh Gumi ya kuma tambayi dalilin da ya sa wasu ke son a kama shi, alhali manufarsa ita ce kawo ƙarshen tashin hankali a Najeriya.

“To me zai sa kama ni? Domin na yi kira su ajiye makamai… ko saboda na faɗakar da al’umma game da labarin ’yan bindiga?”.

Gumi ya zargi masu sukarsa da nuna wariya, inda ya tunatar da su cewa kundin tsarin mulki ya bai wa kowa damar faɗin albarkacin bakinsa.

“Shin faɗin ra’ayi ba haƙƙinmu ba ne na kundin tsarin mulki ba? Shin kira da suke yi na a kama ni ba nuna son rai ba ne kuma zai iya haifar da tashin hankali?”.

Ya bayyana cewa buƙatun ’yan bindigar suka nema waɗanda suka haɗa da ababen more rayuwa, kariya daga kame ba bisa ƙa’ida ba, da hanankai musu hari ba idan sun miƙa wuya.

Ya ce babu ɗaya daga cikin waɗannan abubuwan da aka aiwatar, wanda hakan ya wargatsa tattaunawar.

Gumi, ya ce kamata ya yi mutane su mayar da hankali kan mafita a aikace, ba zagi da fushi ba.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Bindiga Najeriya Tattauanawa Tsaro yan bindiga

এছাড়াও পড়ুন:

Babu Janar ɗin da ISWAP ta kama a Borno — Sojoji

Rundunar Soji ta ƙaryata rahotannin da ke cewa an yi garkuwa da kwamandan Bitget ta 25 da ke Jihar Borno a wani harin kwanton ɓaunan mayaƙan ƙungiyar ISWAP.

Ta buƙaci jama’a su yi watsi da wannan labarin ƙarya, tare da yin addu’ar samun nasarar sojojin Najeriya da ke bakin daga.

Rundunar ta ce sojojin sun murƙushe wani harin kwanton ɓauna da ISWAP ta kai musu a yayin da suke sintiri domin kare al’ummomin da ke kewaye da Wajiroko a yankin Azir Multe a Ƙaramar Hukumar Damboa da ke Jihar Borno.

Ta ce sojojin sun gamu da kwanton ɓauna ne daga ’yan ta’adda yayin da suke dawowa daga aikin sintiri a gefen Dajin Sambisa.

Mayaƙan ISWAP sun sace Janar sun kashe sojoji a Borno Yadda ’yan bindiga suka kashe banga 16 suka sace mutane 42 a Neja

Rundunar ta jaddada cewa Kwamandan Brigedi ta 25, Birgediya Janar M. Uba, shi ne ya jagoranci tawagar, wacce ta haɗa da mambobin CJTF, kuma sun koma sansaninsu lafiya.

Ta ce sojojin sun fuskanci harin ne cikin ƙwazo, inda suka yi musayar wuta da makiya har suka fatattake su.

Sanarwar rundunar, ta hannun muƙaddashin kakakinta, Laftanar-Kanar Appolonia Anele, ta ce a yayin arangamar, sojoji biyu da mambobin CJTF biyu sun kwanta dama.

Hedikwatar tsaro ta yaba da jarumtakar dakarun, tare da yin ta’aziyya ga iyalai da abokan aikin waɗanda suka rasa rayukansu.

Babban Hafsan Sojin Ƙasa, Laftanar-Janar Waidi Shaibu, ya jinjina wa jarumtar dakarun da ke ci gaba da aiki a ɗaya daga cikin yankunan da suka fi haɗari a ƙasar, yana mai cewa sadaukarwarsu abin karramawa ne a kullum wajen kare Najeriya.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Meke Kawo Yanke Hukunce-hukunce Masu Karo Da Juna Daga Kotuna?
  • Babu Janar ɗin da ISWAP ta kama a Borno — Sojoji
  • Masu Kokarin Kashe Kansu Na Kara Karuwa A Nijeriya
  • Shugaban Iran Da Prime Ministan Iraqi Sun Tattaunawa Kan Batun Zabe Da Kuma Alakar Dake Tsakaninsu.
  • Yadda ’yan bindiga suka kashe banga 16 suka sace mutane 42 a Neja
  • ’Yan bindiga sun kashe ’yanga 16 sun sace mutane 42 a Neja
  • ’Yansanda Sun Cafke Wani Da Ake Zargin Dan Ta’adda Ne A Jihar Kebbi
  • NSCDC Ta Cafke Mutum Biyu Bisa Zargin Satar NAPEP Da Safarar Miyagun Kwayoyi A Kano
  • Jan Aikin Da Ke Gaban Manyan Hafsoshin Tsaron Nijeriya