Mayaƙan ISWAP sun kashe kwamandan soji a Borno
Published: 17th, November 2025 GMT
Mayaƙan ƙungiyar ISWAP sun kashe wani babban kwamandan rundunar sojin Najeriya bayan wani harin kwantan ɓauna da aka kai wa tawagarsa a hanyar Damboa–Biu da ke Jihar Borno.
Lamarin ya faru ne bayan da tawagar sojojin tare da dakarun haɗin gwiwa na Civilian Joint Task Force (CJTF) suka kai wani samame a yankin, inda suka gamu da harin ba-zata na ’yan ta’adda.
Kwamandan, wanda daga baya aka bayyana sunansa a matsayin Brigade Commander M. Uba, shi ne ya jagoranci rundunar da ta kai ɗauki ga wasu sojoji da suka yi ɓatan hanya kafin su faɗa tarkon mayaƙan ISWAP.
PRNigeria ta ruwaito cewa, kafin rasuwarsa, kwamandan ya aike da wani bidiyo ga manyansa yana bayyana irin nasarar da tawagarsa ta samu a wani farmaki da suka kai.
Sai dai bayan haka ne ISWAP ta bibiyi wurin da yake ta katse sadarwa, sannan ta kama shi.
Rahotanni sun ce mayaƙan sun kama shi ne da ransa, inda bayan sun yi masa tambayoyi, daga bisani kuma su kashe shi.
Da farko dai rundunar sojin Najeriya ta ce kwamandan yana cikin ƙoshin lafiya bisa hujjar bidiyon da ya aika yana tabbatar da irin nasarar da suke samu.
Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar sojin ƙasa, Laftanar Kanar Appolonia Anele, ta bayyana batun cafke kwamandan nata a matsayin “ƙazon kurege”, tana mai cewa duk da “harbe-harbe masu tsanani” da suka fuskanta daga mayaƙan yayin dawowarsu daga sintiri a gefen Sambisa, an yi nasarar tsira da kwamandan.
Sanarwar ta tabbatar da mutuwar sojoji biyu da jami’an sa-kai biyu a harin, amma ta ce kwamandan ba ya cikin waɗanda aka kama.
Sai dai daga bisani, wasu rahotanni na PRNigeria da jaridar PREMIUM TIMES sun tabbatar da cewa mayaƙan ISWAP sun kama kwamanda ne bayan ya yi ɓata hanya yayin guje wa harin farko.
ISWAP ta yi iƙirarin kashe kwamandanA wata sanarwa cikin harshen Larabci da ISWAP ta wallafa ranar Litinin a jaridarta mai suna Amaq, ta nuna hoton kwamandan a lokacin da ya ke hannunta, yana fama rauni har jini na zuba a kafarsa.
Ƙungiyar ta ce: “Mun kama kwamandan rundunar Najeriya bayan ya tsere daga harin Wajiroko, daga nan muka yi masa tambayoyi sannan muka kashe shi.”
Ƙungiyar ta kuma yi wa rundunar sojin Najeriya gugar zana, tana mai bayyana bayanan farko da ta fitar a matsayin “ƙarya tsagwaronta da ke tabbatar da gazawarta.”
Kawo yanzu dai Rundunar Sojin Najeriya ba ta fitar da sanarwa a hukumance ba, amma majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa ana gudanar da bincike kan yadda aka bar kwamandan cikin haɗari bayan tserewa daga harin farko.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: ISWAP kwamanda rundunar sojin Najeriya tabbatar da
এছাড়াও পড়ুন:
Yadda ’yan bindiga suka kashe banga 16 suka sace mutane 42 a Neja
’Yan banga 16 sun kwanta dama a yayin da ’yan bindiga suka yi garkuwa da mutane 42 a wani hari na daban a Ƙaramar Hukumar Mashegu da ke Jihar Neja.
Aminiya ta samu rahoton cewa ’yan bindiga sun kai hare-haren ne daga ranar Alhamis zuwa Asabar, lamarin da ya sa mutane da dama yin ƙaura daga ƙauyuka
Wani mazaunin yankin ya shaida wa wakilinmu cewa maharan sun fara kai farmaki ne a ƙauyen Dutsen Magaji, inda suka yunwa mutane 22 kisan gilla.
“Da suka kawo hari, ’yan banga sun bi su, ɓangarorin suka yi musayar wuta, amma suka kashe ’yan Banda biyar, wasu uku na karɓar magani a Asibiti.”
Ya ce daga baya ’yan bindiga suka kawo sabon hari da asuba, ranar Alhamis a yayin da ake Sallar Asuba a ƙauyen Magama, suka yi garkuwa da mutane 20.
“Nan ma da ’yan bindiga suka bi su, ashe sun yi kwanton ɓauna, suka kashe ’yan banga 13, suka jikkata wasu da dama.”
Sakataren Yaɗa labaran Shugaban Ƙaramar Hukumar Mashegu, Isah Ibrahim Bokuta, ya tabbatar da hare-haren, tare da jinjina wa ’yan bangar bisa yadda suka sadaukar da ransu domin kare al’umnarsu.
Wakilinmu ya yi ƙoƙarin jin ta bakin mai magana da yawun ’yan sanda na Jihar Neja, Wasiu Abiodun, amma ya ce zai tuntuɓe shi daga baya, idan ya bincika.
A gefe guda, mazauna yankin sun shaida mana cewa tun ranar Litinin al’ummomi da dama sun yi gudun hijira zuwa Mashegu, Kawo-Mashegu, Manigi da wasu wurare. Wasu kuma sun fake a gidajen ’yan uwansu a nesa domin tsira.
Majiyoyi sun ce cikin ƙauyukan da aka watse har da Dutsen Magaji, Borin Aiki, Gidan Ruwa da Magama.
Hakazalika har yanzu masu garkuwa da tsohon Shugaban Hukumar SUBEB ta Jihar Neja, Alhaji Alhassan Bawa Niworo, ba su sake shi ba, makonni bayan rahoton cewa iyalansa sun biya kuɗin fansa na Naira miliyan 70.
An yi garkuwa da Niworo ne a ranar Litinin, 29 ga Satumba, 2025, tare da Kwamishina na Dindindin II na Hukumar Zaɓe ta Jihar Neja (NSIEC), Barrister Ahmad Mohammed, direbobinsu da wasu matafiya a kan titin Mokwa–New Bussa, a Karamar Hukumar Borgu.