Aminiya:
2025-11-17@15:15:17 GMT

’Yan Majalisar Dokokin Taraba 16 sun sauya sheka daga PDP zuwa APC

Published: 17th, November 2025 GMT

Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Taraba, Rt Hon. Kizito Bonzena, tare da ’yan majalisar 15 sun sauya sheka daga jam’iyyarsu ta PDP zuwa APC.

A saifyar Litinin ne Rt Hon. Kizito Bonzena ya gabatar da takardarsa ta ficewa daga PDP tare da sauran mambobin zuwa APC.

Ya bayyana cewa da sauyin shekar tasu, yanzu APC ce ke da daukacin kujeru 24 da ke Majalisar Dokokin Jihar Taraba.

Hakan na zuwa ne jim kadan bayan Gwamnan Jihar Taraba, Kefas ya sanar da shirinsa na komawa APC daga PDP.

Masu ibadar Umarah 42 sun mutu a hatsarin mota a hanyar zuwa Makka ’Yan ta’adda sun sace dalibai 25 a dakunan kwanansu a Kebbi

Sauran mambobin majalisar da suka sauya sheka sun hada da Mataimakin Shugaban Malisar, Hamman Adama Abdullai (Bali 2) da Shugaban Masu Rinjaye, Jethro Yakubu (Wukari 1). Sauran sun hada da Tafarki Eneme (Kurmi ); Akila Nuhu (Lau ); Musa Chul (Gassol 1);  da Josiah Yaro (Wukari 2).

Akwai kuma Tanko Yusuf (Takum 1), Veronica Alhassan (Bali 1), Anas Shuaibu (Karim Lamido 2), Nelson Len (Nguroje), Umar Adamu (Jalingo 1), Joseph Kassong (Yorro), John Lamba (Takum 2), Happy Shonruba (Ardo-Kola) da kuma Zakari Sanusi (Ibi Constituency).

Da yake sanar da sauyin shekar tasu, shugaban majalisar ya bayyana cewa sun yi hakan ne saboda bukatar al’umma ba don bukatar kansu ba.

Tsohon Shugaan Malisar Dokokin Jihar, Peter Diah, ya yi maraba da su a APC.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: yan majalisar

এছাড়াও পড়ুন:

Fasinjojin Da Kasar Sin Ta Yi Jigilarsu Ta Jirgin Kasa Daga Janairu Zuwa Oktoba Sun Kai Biliyan 3.95

Fasinjojin Da Kasar Sin Ta Yi Jigilarsu Ta Jirgin Kasa Daga Janairu Zuwa Oktoba Sun Kai Biliyan 3.95

An ba da labari cewa, yawan fasinjojin da aka yi jigilarsu ta jirgin kasa daga watan Janairu zuwa Oktoba na wannan shekara a kasar Sin ya kai biliyan 3.95, wanda ya karu da 6.4% idan aka kwatanta da na shekarar da ta gabata.

Bayanai masu alaka da hakan sun nuna cewa, a farkon watannin goma na wannan shekara, adadin fasinjoji da jiragen kasa na Sin suka yi jigilarsu ya kai matsayi mafi girma a tarihi a wannan lokaci, kuma a ranar 1 ga Oktoba kawai, yawan fasinjojin ya kai fiye da miliyan 23.13, wanda ya kai matsayi mafi girma a tarihi a rana daya a wannan bangare.(Amina Xu)

ADVERTISEMENT ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Babban Jirgin Ruwan Yaki Samfurin 076 Na Sin Ya Kammala Gwajinsa Na Farko A Teku November 16, 2025 Daga Birnin Sin Sin Ta Gargadi Philippines A Kan Ci Gaba Da Tayar Da Zaune Tsaye A Tekun Kudancinta November 16, 2025 Daga Birnin Sin An Yi Taron Karatun Sinanci Na Duniya Na 2025 A Beijing November 16, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kakakin Majalisar Taraba Da Ƴan Majalisa 15 Sun Fice Daga PDP Zuwa APC
  • Fasinjojin Da Kasar Sin Ta Yi Jigilarsu Ta Jirgin Kasa Daga Janairu Zuwa Oktoba Sun Kai Biliyan 3.95
  •  An Amince Da  Sauye-sauye A Tsarin Mulkin Kasar Benin
  • Na kusa komawa APC – Gwamnan Taraba
  • Kanada Ta Tsare Tsohon Wakilin Majalisar Dinkin Duniya Mai Bincike Kan Laifukan Yakin Israila.  
  • Wakilai Daga Jihohi 19 Sun Isa Ibadan Don Taron PDP Na Ƙasa
  • Jakadan Iran A Majalisar Dinkin Duniya Yace Iran Ba za Ta Taba Mika Wuya Ga Duk Wata Barazana Ba
  • ’Yansanda Sun Cafke Wani Da Ake Zargin Dan Ta’adda Ne A Jihar Kebbi
  • AU da MDD, sun karfafa dabarun tabbatar da zaman lafiya da tsaro