Afirka ta Kudu na Binciken shigar wasu ‘yan gudun hijirar Falasdinu 153 cikin kasar
Published: 17th, November 2025 GMT
Shugaba Cyril Ramaphosa na Afirka ta Kudu ya ce kasarsa na binciken wani jirgin sama da ya kawo ‘yan gudun hijirar Falasdinawa 153 kasar ba tare da takardun shiga ba.
“Wadannan mutane ne daga Gaza wadanda, ta wata hanya, suka tsinci kansu cikin jirgin sama da ya tashi daga Nairobi (babban birnin Kenya) kafin su iso nan,” in ji Ramaphosa ga manema labarai, yana mai cewa hukumomin leken asiri da Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida na kasar suna binciken lamarin.
A ranar Alhamis, Afirka ta Kudu ta ba Falasdinawan su 153 mafaka ta kwanaki 90, duk da cewa an hana su shiga saboda sun gaza amsa tambayoyin da aka musu kuma fasfo dinsu ba su da tambarin tashi, ko tikitan komawa in ji Ma’aikatar Harkokin Cikin Gidan Afrika ta kudu a cikin wata sanarwa.
A halin yanzu, ofishin jakadancin Falasdinu a Afirka ta Kudu ya bayyana a shafukan sada zumunta cewa ‘yan Falasdinu 153 sun iso ba tare da wata sanarwa ko hadin gwiwa ba.
An bayyana cewa wata kungiyar mayaudara ce ta shirya jirgin.
Ofishin jakadancin ya ce kungiyar ta yi amfani da mummunan halin jin kai na al’ummar Gaza, ta yaudari iyalai, ta karbi kudi gare su, ta samar musu tafiyar ta hanyar da ba ta dace ba, saidai kungiyar agaji ta Gift of the Givers, ta shaida wa tashar talabijin ta Afirka ta Kudu SABC cewa Isra’ila ce ke da alhakin shigar ‘yan gudun hijirar Falasdinawa cikin kasar ba bisa ka’ida ba.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Najeriya ba za ta buga kofin duniya ba karo na biyu a jere November 17, 2025 DRC: An Kulla Yarjejeniyar Zaman Lafiya A Tsakanin Gwamnati Da Kungiyar M23 November 16, 2025 An Yi Kira A Bai Wa ‘Yan Hijira Saboda Sauyin Muhalli Kariya November 16, 2025 An Amince Da Sauye-sauye A Tsarin Mulkin Kasar Benin November 16, 2025 Isra’ila Ta Kai Wa Sojojin MDD Hari A Kasar Lebanon November 16, 2025 Makiya Sun Kulla Makirci kan Kasar Labanon Irin Wanda Suka Kulla Kan Siriya November 16, 2025 Kasar Afghanistan Na Kokarin Karkata Akalar Kasuwancinta Zuwa Iran November 16, 2025 Kanada Ta Tsare Tsohon Wakilin Majalisar Dinkin Duniya Mai Bincike Kan Laifukan Yakin Israila. November 16, 2025 Zarfi: HKI Ce Kawai Take Ayyana Nukiliya Ba Bisa Kaida Ba A Yammacin Asiya. November 16, 2025 Shugaban kasar venuzuwela Yayi Tir Da Atisayan Soji Da Trinidad and Tobago Ke yi. November 16, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Lebanon za ta shigar da kara a kan Isra’ila a MDD game da gina Katanga a iyakarta
Gwamnatin Beirut ta ce za ta shigar da kara a kan Isra’ila gaban Majalisar Dinikin Duniya game da gida katangar siminti a kan iyakar Kudancin Lebanon.
A cikin wata sanarwa data fitar fadar shugaban Lebanon ta sanar da cewa Beirut za ta shigar da kara a Majalisar Dinkin Duniya game da gina katangar.
Shugaban Lebanon Joseph Aoun ya umarci Ministan Harkokin Wajen kasar Youssef Radji da ya umurci tawagar Lebanon ta Dindindin a Majalisar Dinkin Duniya da ta shigar da karar gaggawa a kwamitin Tsaro kan gwamnatin Isra’ila saboda gina katangar siminti a kan iyakar kudancin Lebanon, wadda ta wuce ‘’Layi Shuɗi’’ da aka zana bayan janyewar Isra’ila a shekarar 2000.
Hukumomin Lebanon sun ce katangar simintin da sojojin Isra’ila suka gina ta hana mazauna kudancin Lebanon shiga wani yanki mai fadin murabba’in mita 4,000 na yankin Lebanon.
Wani bincike da Rundunar Wucin Gadi ta Majalisar Dinkin Duniya (UNIFIL) ta gudanar a watan Oktoba ya nuna cewa katangar da sojojin Isra’ila suka gina ta ratsa Layin Shuɗi, kamar yadda Stéphane Dujarric, kakakin Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, ya sanar a ranar Juma’a.
An kuma gina wani sashe na biyu na wata katangar a kudu maso gabashin kauyen Yaroun na Lebanon, kuma ita ma ta ratsa Layin Shuɗi.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran : kasantuwar sojojin Amurka a yankin Caribbean barazana ce ga zaman lafiyar duniya November 16, 2025 AU ta sake nanata cewa “Babu kisan kare dangi a arewacin Najeriya November 16, 2025 Falasdinu ta yi wasan sada zumunci a Spain November 16, 2025 Amurka Ta Yi Gwajin Makaman Nukiliya A Watan Ogusta November 15, 2025 Adadin Ma’adanin “Colbat” Da DRC Ta Bai Wa Duniya Ya Kai Ton 1,000 November 15, 2025 Ma’ariv: Netanyahu Yana Tsoron Hukuncin Da Kotu Za Ta Yanke Akansa November 15, 2025 An Bayyana Sunayen Kasashen Da Su Ka Fi Sayar Wa “Isra’ila” Man Fetur A Lokacin Yakin Gaza November 15, 2025 MDD: Mutane 100,000 Ne Su Ka Fice Daga Birnin Al-Fasher Na Kasar Sudan November 15, 2025 Jakadan Iran A Majalisar Dinkin Duniya Yace Iran Ba za Ta Taba Mika Wuya Ga Duk Wata Barazana Ba November 15, 2025 Kasashen Latin Amurka Sun Shirya Tsaf Don Mayar Da Martani Kan Wuce Gona Da Irin Amurka Kan Venuzuwela November 15, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci