Kwalejin Kiwon Lafiya ta Najeriya ta fara taron shekara-shekara karo na 19 na kimiyya da nufin yin amfani da sabbin fasahohi da kirkire-kirkire wajen kawo sauyi a fannin likitanci a kasar.

 

Da yake yiwa manema labarai jawabi gabanin taron a Sokoto, shugaban kwalejin na kasa, Dokta Peter Ebeigbe ya ce taron zai tattauna hanyoyin da za a bi domin tunkarar manufofi aiwatarwa mai inganci da shigar da kamfanoni masu zaman kansu a fannin ilimin likitanci na gaba da digiri na biyu.

 

Gidan Rediyon Najeriya dake Sokoto ya ruwaito cewa, ana sa ran taron zai kuma tattauna kan ingancin aikace-aikacen kirkirariyar fasaha ta Artificial Intelligence (AI) da illolinsa na isar da sahihanci mai inganci.

 

Shugaban na kasa ya kara da cewa ana sa ran masu hannu da shuni hudu ne zasu jagoranci taron.

 

Nasir Malali

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Sakkwato

এছাড়াও পড়ুন:

Zamfara Ta Tashi Daga Matsayi Na 36 Zuwa Na 17 A Shekara Biyu Ƙarƙashin Gwamna Lawal — Rahoton BudgIT

A shekarar 2023 lokacin da Gwamna Lawal ya hau mulki, Zamfara ta kasance a ƙasan jadawalin a matsayi na 36.

 

Rahoton ya nuna cewa kuɗaɗen shiga na jihar sun ƙaru da kashi 182.34%, daga naira biliyan 87.44 a 2023 zuwa naira biliyan 246.88 a 2024. Haka kuma jimillar kuɗaɗen shiga gaba ɗaya ta ƙaru zuwa naira biliyan 315.53, ƙaruwar kusan kashi 118%. Haraji da jihar ta tara ya kai kusan kashi 10.31% na jimillar kuɗaɗen shiga a 2024.

 

BudgIT ta bayyana cewa wannan ci gaban yana nuna Zamfara ta fara rage dogaro ga kuɗin kason asusun tarayya, kuma idan za a yi hasashe, jihar na da ƙarfin kai da kai idan za a kalle ta a matsayin ikon tattalin arziki mai zaman kansa.

 

A bangaren haraji, jihar ta samu naira biliyan 25.46 a 2024, ƙaruwa ce ta kusan kashi 15% daga naira biliyan 22.16 a shekarar da ta gabata. Har ila yau, kuɗaɗen FAAC sun ƙaru da sama da kashi 239%, daga naira biliyan 65.28 a 2023 zuwa biliyan 221.42 a 2024.

 

Rahoton ya kuma yi hasashe kan habakar kuɗaxen shiga marasa haraji, inda aka samu ƙaruwa sosai a bangaren lasisi, kuɗin biyan takardu da wasu hanyoyin samun kuɗaɗe. Misali, kuɗaɗen lasisi sun tashi da fiye da kashi 5,900% a shekarar 2023.

 

A ɓangaren kashe kuɗi, musammam a fannin lafiya da ilimi, rahoton ya nuna ƙarin kuɗaɗen da gwamnati ta zuba, duk da cewa akwai ƙalubalen ingantacciyar aiwatarwa. Jimillar kashe kuɗin lafiya ta tashi daga naira biliyan 4.29 a 2022 zuwa biliyan 11.88 a 2024, inda kashe kuɗi kan mutum ɗaya ya ninka fiye da biyu.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Sabon Muƙaddashin Shugaban PDP Ya Sha Alwashin Maido Da Martabar Jam’iyyar Kafin 2027 November 3, 2025 Manyan Labarai Mayar Da Martani Kan Barazanar Amurka Ga Nijeriya: Fadar Shugaban Ƙasa Ta Yaba Wa Kwankwaso  November 3, 2025 Labarai NARD Ta Yi Fatali Da Iƙirarin Gwamnatin Tarayya Na Ba Ta ₦43bn, Kuma Yajin Aiki Na Nan November 3, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Zamfara Ta Tashi Daga Matsayi Na 36 Zuwa Na 17 A Shekara Biyu Ƙarƙashin Gwamna Lawal — Rahoton BudgIT
  • Girgizar kasa ta yi ajalin gomman mutane a Afghanistan
  • Marasa Lafiya A Nasarawa Sun Koka Game Da Yajin Aikin Likitoci
  • Gidauniyar IRM Da KADCHMA, Ta Ƙaddamar Da Inshorar Lafiya Kyauta Ga Mutane 200 A Kaduna
  • Pezeshkian: Bunkasa Masana’antar Makamashin Nukiliyar Iran Don Inganta Rayuwar Al’ummar Iran Ne
  • A Kan Wa Trump Ke Son Kaddamar Da Hari a Najeriya?
  • Kisan Kiristoci: Lauyoyi sun nemi Gwamnatin Tarayya ta tattauna da Amurka
  • Dalilin Gwamnatin Jihar Kuros Riba Na Raba Wa Manoma Taraktoci
  • An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Duniya Kan Kirkire-Kirkire Da Bude Kofa Da Ci Gaba Na Bai Daya A Nijeriya
  • Xi Jinping Ya Tattauna Da Shugaban Koriya Ta Kudu Lee Jae-myung