Za mu ceto ’Yan Matan GGCSS Maga cikin ƙoshin lafiya — Gwamnan Kebbi
Published: 18th, November 2025 GMT
Gwamna Ahmed Idris na Jihar Kebbi ya ba da tabbacin cewa jami’an tsaro za su ƙwato ’yan matan da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a Kwalejin ’Yan Mata ta GGCSS Maga da ke Ƙaramar Hukumar Danko Wasu ta jihar cikin ƙoshin lafiya.
Gwamnan ya bayar da tabbacin ne a yayin ganawarsa da iyayen ɗaliban kaɗan bayan harin ’yan bindigar a ranar Litinin.
Aminiya ta ruwaito cewar da asubahin ranar ’yan bindiga suka kusta cikin harabar makarantar kwana ta ’yan mata ta GGCSS Maga, suka kwashe ɗalibai 25 daga ɗakin kwanansu zuwa cikin jeji.
Maharan da suka riƙa harbi a iska kafin su shiga harabar makarantar sun bindige Matakin Shugaban Makarantar, Malam Hassan Yakubu Makuku, wanda ya yi ƙoƙarin hana su tafiya da yaran.
Sace Ɗalibai: Gwamnatin Tinubu ba ta shirya kawo ƙarshen ta’addancin ’yan bindiga ba — Amnesty Gobara ta laƙume rayukan yara biyu ’yan gida ɗaya a RibasA yayin ziyarar jaje da Gwamna Idris ya kai makarantar, bayan yanke ziyarar aiki da ya kai Abuja, ya ba wa iyayen ɗalibai tabbacin cewa gwamnatinsa da hukumomin tsaro za su yi dukkan abin da zai yiwu wajen ceto yaran.
Kana ya jaddada cewa za su ci ga da ƙoƙari wajen ganin bayan ayyukan ta’addanci a jihar.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan sanda sun kama ƙunshi 66 na Tabar Wiwi a Gombe
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe ta kama ƙunshi 66 na ganyen tabar wiwi a wani samame da ta kai a garin Deba, bayan samun wasu sahihin bayanan leƙen asiri.
Mai magana da yawun rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:30 na dare a ranar 16 ga Nuwamba, 2025, lokacin da aka hango wata mota mara lamba, ƙirar Toyota Corolla, da ake zargi tana ɗauke da kayan, a kan hanyar Kuri zuwa Deba.
Hauhawar farashi ya ƙara raguwa a Nijeriya — NBS An ɗaura auren Sanata Kawu Sumaila da wata jami’ar soji a KanoAminiya ta ruwaito cewa, bayan isar jami’an wurin da ake zargin akwai kayan laifin ne, sun lura da wasu mutum uku suna ƙoƙarin yi wa wani mutum lodi a kan babur, lamarin da ya sanya ababen zargin suka tsere bayan hango ’yan sandan.
Binciken farko da aka gudanar ya kai ga gano buhuna uku ɗauke da ƙunshi 66 na ganyen da ake zargin tabar wiwi ce.
An dai kwashe kayayyakin zuwa ofishin ’yan sanda, kuma an fara bincike don kamo waɗanda suka tsere.
Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Gombe, CP Bello Yahaya, ya jinjina wa jami’an da suka gudanar da wannan aiki, yana mai tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da fatattakar masu safarar miyagun ƙwayoyi a faɗin jihar.