HausaTv:
2025-11-17@07:58:47 GMT

Najeriya ba za ta buga kofin duniya ba karo na biyu a jere

Published: 17th, November 2025 GMT

Jamhuriyar Congo ce za ta wakilci Afirka a sauran wasan cike gurbin shiga gasar kofin duniya, bayan da ta yi nasara a kan Najeriya da cin 4-3, bayan da suka tashi kunnen doki 1-1.  

Congo za ta fafata da Bolivia da New Caledonia da Iraki da Jamaica da kuma Panama da za su kece raini a birnin Guadalajara da Monterrey a Mexico a watan Maris.

Super Eagles ta kai gasar kofin duniya shida daga bakwai tsakanin 1994 zuwa 2018, kuma wannan shi ne karon farko da Najeriya ba za ta buga kofin duniya ba karo biyu a jere tun 1990, bayan kasa zuwa 2022 a Qatar. 

Wannan shi ne karon farko da Congo DR za ta je babbar gasar tamaula ta duniya da zarar ta samu gurbin, bayan 1974 a Jamus, amma a lokacin ana kiranta Zaire.

Za a buga gasar kofin duniya tsakanin tawaga 48 a Amurka da Canada da Mexico a 2026.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka DRC: An Kulla Yarjejeniyar Zaman Lafiya A Tsakanin Gwamnati Da Kungiyar M23 November 16, 2025 An Yi Kira A Bai Wa ‘Yan Hijira Saboda Sauyin Muhalli Kariya November 16, 2025  An Amince Da  Sauye-sauye A Tsarin Mulkin Kasar Benin November 16, 2025 Isra’ila Ta Kai Wa Sojojin MDD Hari A Kasar Lebanon November 16, 2025 Makiya Sun Kulla Makirci kan Kasar Labanon Irin Wanda Suka Kulla Kan Siriya November 16, 2025  Kasar Afghanistan Na Kokarin Karkata Akalar Kasuwancinta Zuwa Iran November 16, 2025 Kanada Ta Tsare Tsohon Wakilin Majalisar Dinkin Duniya Mai Bincike Kan Laifukan Yakin Israila.   November 16, 2025  Zarfi: HKI Ce Kawai Take Ayyana Nukiliya Ba Bisa Kaida Ba A Yammacin Asiya. November 16, 2025 Shugaban kasar venuzuwela Yayi Tir Da Atisayan Soji Da Trinidad and Tobago Ke yi. November 16, 2025 IRGC ta kama wani jirgin ruwan dakon mai a gabar tekun kudancin Makran November 16, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: kofin duniya

এছাড়াও পড়ুন:

An Yi Kira A Bai Wa ‘Yan Hijira Saboda Sauyin Muhalli

Kungiyar kasa da kasa mai kula da ‘yan hijira ( IOM) tana yin kira ga shugabannin kasashen duniya da su bayar da kariya da kare hakkokin wadanda suke rayuwa a yankunan da suke fama da matsalar sauyin yanayi.

A taron da ake yi a yanzu haka a  garin Belem na kasar Brazil kungiyoyi masu zama kansu dake fafutuka da rajin kare muhalli suna gabatar da shawarwari akan yadda za fuskacin matsalolin da duniya take fuskanta.

Kiran kungiyar ya ambato mutanen da sauyin yanayi ya tilasta musu yin hijira, ‘yan asalin kasa a cikin karkara da ‘yan gargajiya.

Ibtila’oin dabi’a irin su ambaliyar ruwa, zafi mai tsanani, fari da mahaukaciyar guguwa, suna tilastawa miliyoyin mutane barin gidajensu a kowace shekara. Da akwai da dama da ba su iya tsallake iyakokin kasashensu, suna ci gaba da zama a wasu yankuna nesa da gidajensu.

Kungiyar tana son ganin an taimakawa wadannan bangarorin na mutane a karkashin kare muhalli.

Masana suna bayyana cewa a nan gaba, za a sami wasu kasashen da za su nitse a karkashin tekuna da suke kara cikowa,ko kuma su zama wuraren da ba za za iya rayuwa a cikinsu ba.

Mataimakin Babbar darakta na kungiyar ( IOM), Ughoci Daniels ya bayyana cewa, samar da tsarin yin gargadin gaggawa, da ayyukan hidima a cikin yankunan da aka fi fuskantar hatsari, yana da matukar muhimmanci domin karfafa mutane su ci gaba da rayuwa a inda suke.

Daniels ya kuma ce; Da dama daga cikin wadanda su ka fice daga cikin muhallinsu saboda sauyin yanayi, suna fadin cewa sun fiifta komawa zuwa gidajensu. Sai dai kuma garuruwan nasu sun tashi daga yadda su ka san su a baya saboda sauyin yanaki. A dalilin haka, abinda ake da bukatuwa da shi, shi ne samar da abubuwan da za su karfafa su.”

A dalilin haka, Daniel ya yi fatan ganin taron da ake yi na kasar Brazil akan muhalli ya zama wanda zai daura dan Ba, a fagen samar da sauyi da kuma biyan asarar da aka samu saboda sauyin yanayin.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka  An Amince Da  Sauye-sauye A Tsarin Mulkin Kasar Benin November 16, 2025 Isra’ila Ta Kai Wa Sojojin MDD Hari A Kasar Lebanon November 16, 2025 Makiya Sun Kulla Makirci kan Kasar Labanon Irin Wanda Suka Kulla Kan Siriya November 16, 2025  Kasar Afghanistan Na Kokarin Karkata Akalar Kasuwancinta Zuwa Iran November 16, 2025 Kanada Ta Tsare Tsohon Wakilin Majalisar Dinkin Duniya Mai Bincike Kan Laifukan Yakin Israila.   November 16, 2025  Zarfi: HKI Ce Kawai Take Ayyana Nukiliya Ba Bisa Kaida Ba A Yammacin Asiya. November 16, 2025 Shugaban kasar venuzuwela Yayi Tir Da Atisayan Soji Da Trinidad and Tobago Ke yi. November 16, 2025 IRGC ta kama wani jirgin ruwan dakon mai a gabar tekun kudancin Makran November 16, 2025 Iran : sojojin Amurka a yankin Caribbean barazana ne ga zaman lafiya  November 16, 2025 Lebanon za ta kai karar Isra’ila a MDD kan gina Katanga a iyakarta November 16, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An Yi Kira A Bai Wa ‘Yan Hijira Saboda Sauyin Muhalli
  • Kanada Ta Tsare Tsohon Wakilin Majalisar Dinkin Duniya Mai Bincike Kan Laifukan Yakin Israila.  
  • Falasdinu ta yi wasan sada zumunci a Spain
  • Ina Son Kasancewa Cikin Koshin Lafiya Kafin Buga Gasar Kofin Duniya Na Shekarar 2026 – Messi
  • Mali ta Dakatar da Tashoshin Talabijin na Faransa TF1 da LCI
  • Adadin Ma’adanin “Colbat” Da DRC Ta Bai Wa Duniya Ya Kai Ton 1,000
  • Limamin Juma’a Ya Bukaci Ganin An Kai Karar Donald Trump A Kotunan Duniya
  • Wasu kasashen duniya sun nuna damuwa game da tsarin mulkin bayan yakin Gaza
  • Ronaldo Na Fuskantar Dakatarwar Wasanni Biyu Bayan Samun Jan Kati