Gobara ta cinye gidan hakimi a Bauchi
Published: 5th, August 2025 GMT
Gobara ta ƙone gidan Barden Bauchi Hakimin Ƙasar Lere, Alhaji Sulaiman Muhammad da ke unguwar Gwallaga a cikin garin Bauchi.
Sa’in Tafawa Balewa Mallam Yunusa Ado ya tabbatar da faruwar lamarin, da cewa “Wannan gobara ta auku ne akamakon kawo wutan lantarki da hantsi ranar Litini 4/8/2025 lokacin Hakimin na Fadarshi dake garin Zwall.
Mallam Yunusa ya ce, “Gidan ya ƙone ƙurmus, an yi asarar dukiya mai tarin yawa amma an yi sa’a da hatsin ne ya faru, amma ba a samu asarar rai ba, kuma babu wanda ya jikkata.
Ya bayyana cewa makwabta da zuwan jami’an sun taimaka an aka fitar da motar da ke garejin zuwa waje, amma an tafka asara.
Sa’in yace “Muna addu’ar Allah Ya Maida masa mafi alherin abin da aka rasa, Ya kuma tsare na gaba.”
Ɗaliba ’yar shekara 15 daga Yobe ta lashe Gasar Muhawara ta Duniya NAJERIYA A YAU: Yadda Ayyuka Suka Ragu A Jihohi Bayan Kudin Shiga Ya Karuউৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Tsohon Dan Majalisar Taraba Usman Ya Fice Daga APC
Tsohon dan majalisa mai wakiltar mazabar tarayya ta Wukari/Ibi ta jihar Taraba a majalisar wakilai, Hon. Shiddi Danjuma Usman ya fice daga jam’iyyar APC. Usman ya bayyana rikicin cikin gida na jam’iyyar da rashin bin ka’idojin dimokuradiyya a matsayin dalilinsa na ficewa daga jam’iyyar. ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane Da Dama A Kauyukan Zamfara Gwamnatin Kano Za Ta Mayar Da Gidan Gyaran Hali Na Kurmawa Gidan Tarihi Shiddi, wanda ya wakilci mazabarsa a majalisar wakilai ta 8 da ta 9, ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta wayar tarho da manema labarai a ranar Lahadi. Tsohon dan majalisar ya ce, matakin da ya dauka na ficewa daga jam’iyya mai mulki ya biyo bayan tunani na tsawon watanni da kuma kara nuna damuwa game da abin da ya bayyana a matsayin ficewar jam’iyyar APC daga dabi’un da suka zaburar da shi tsunduma cikinta a baya. Sai dai kuma, tsohon dan majalisar bai bayyana matsayinsa na siyasa na gaba ba duk da cewa an kada gangar zaben 2027 inda ‘yan adawa ke barazanar hambarar da jam’iyyar APC mai mulki daga mulki.Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp