Babban Hafsan Hafsoshin Sojan Iran ya jaddada cewa: Idan makiya suka sake yin kuskure, za su fuskanci mayar da martani da karfi

Babban hafsan hafsoshin sojan kasar Iran Manjo Janar Abdulrahim Mousavi ya jaddada cewa: Idan makiya suka sake yin wani kuskure, to za su fuskanci mayar da martani mai karfi da zai wurga su cikin nadama kuma martini mai gauni ne fiye da na baya.

A yayin ganawarsa da gungun mayakan sojojin sama, Manjo Janar Mousavi ya mika sakon jinjina ga shahidan daukaka da karfin Jamhuriyar Musulunci musamman shahidi Major Janar Hajizadeh. Ya yaba da rawar da ya taka wajen ciyar da shirye-shiryen rundunar Sojan sararin samaniya da bunkasa karfin makamai masu linzami da jirage  marasa matuki ciki na kasar, ya kuma yi la’akari da kokarinsa a matsayin mai karfi da zaburarwa ga al’ummomi masu zuwa kuma masu dauke da ruhin kare kasarsu.

Mousavi ya bayyana rundunar Dakarun kare juyin juya halin Musulunci ta IRGC a matsayin rundunar da ke haifar da alfahari da mutuntawa, yana mai cewa, “Bayyana wannan karfin da sojojin sararin samaniya suka gwada a lokacin yakin kwanaki 12 da aka kakaba wa Iran ya zarce duk abin da aka tsammata, kuma girman kokari da suka nuna ya fi muhimmanci fiye da manyan ayyukan da aka yi a lokacin tsaro mai alfarma.”

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Manoma a Jigawa Sun Jinjinwa Kungiyar Sasakawa Africa Bisa Bada Tallafi a Harkar Noma

Daga Usman Muhammad Zaria

 

Kananan manoma a jihar Jigawa sun yabawa kungiyar Sasakawa Africa dangane da tallafin da take samarwa a fannin inganta noma.

Yayin tattaunawa da wasu daga cikin wadanda suka ci moriyar shirin musamman manoman shinkafa a garin Chandam dake karamar hukumar Birnin Kudu, sun bayyana cewa tallafin Sasakawa ya habaka noman shinkafar su tare da samun karin kudade.

Manoman sun bayyana cewar shirin ya taimaka masu wajen bunkasa harkokin noma tare da tallafawa al’ummomin su.

Daya daga cikin wadanda suka amfana da shirin a yankin Chandam dake karamar hukumar Birnin Kudu, Buhari Nafi’u, yace Sassakawa Africa ta samar masu da tallafin  noma daban daban.

A cewar sa tallafin sun hada da horo wanda ya taimakawa kananan manoma wajen ganin sun kara samun kudade tare da inganta rayuwar maza da mata a yankin.

Yace a wannan shekarar sun noma amfanin gona mai yawa sakamakon horon da suka samu karkashin shirin, inda suka hadu sukayi noman a kungiyance a yankin Birnin Kudu.

Buhari ya kara da cewar, a shekarun baya suna daukan kwanaki casa’in kafin su girbe shinkafa amma zuwan Sassakawa ya sa sun yi noma tare da girbe amfanin gonan su a cikin kwanaki saba’in saboda irin da kungiyar ta basu.

Yace yanzu haka sun fara amfani da shinkafar da suka noma a gidajen su.

Yace an basu takin zamani kyauta tare da sauran kayayyakin feshi.

Ya godewa tallafin na Sassakawa, yana mai cewar zai cigaba da amfani da irin da aka basu tare da koyar da mazauna yankin abubuwan da aka horar da su akai.

Shi ma Malam Rufai Nasiru daga yankin na Chandam  yace sun kara samun ilimi akan sabbin dubarun noma wanda suka samu daga kungiyar ta Sassakawa.

Yace a bana ya noma buhun shinkafa 8 ba kamar a baya ba da yake noma buhu biyar, yana mai cewa shirin yana da inganci kuma zai cigaba da amfani da irin da kungiyar ta basu.

A garin Chuwasu  dake karamar hukumar Taura, Aminu Babanyara ya bayyana cewar sun ci moriyar shirin ta hanyar samun iri masu inganci da takin zamani da kuma horo akan sabbin dubarun noma.

Yace wasu daga cikin abubuwan da suka koya sun hada da amfani da shara wajen yin taki a gida inda suka ce hakan yasa sun samu karin shinkafa da geron da suke nomawa idan aka kwatanta da shekarun baya.

Babanyara, yace sabbin dubarun da suka koya da kuma irin da Sassakawa suka basu, ya basu damar ninka abin da suka saba nomawa a damina sau uku.

Yace da farko suna da shakku akan amfani  da sabbin irin da sabbin dubarun noman, amma kuma bayan sun gwada a shekaru biyu na farko sun ga alfanun hakan wajen bunkasa amfanin gonan da suke nomawa.

Manoman sun kuma yi kira ga kunyiyar ta Sassakawa ta samar masu da injinan casa domin saukaka masu al’amura.

Malama Amina Abdulrahman wacce tayi jawabi a madadin kungiyar mata manoma a Karamar  Hukumar Taura, tace shirin tallafin Sassakawa ya kawo sauyi a rayuwar su musamman a fannin samun kasuwanci da amfanin gonar da ake sarrafawa don yin abinci mai gina jiki na yara.

A cewar ta an horar da su akan yadda za su samar da abinci mai gina jiki a yankuna tare da yadda za su yi aiki a kungiyance don inganta noma.

A don haka, tayi kira ga kungiyar Sassakawa ta samar masu da injinan sarrafa amfanin gona na zamani.

Yankunan da aka ziyarta sun hada da Chandan dake Birnin Kudu da kuma Sabon Gari shi ma a karamar hukumar Birnin Kudu.

Sauran sun hada da Baranda dake Dutse da kuma Chuwasu dake karamar hukumar Taura.

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Shin Mene Ne Matsalar Liverpool A Wannan Kakar?
  • Amurka : zamu dauki matakin soja idan Najeriya ta gaza kawo karshen kashe Kiristoci
  • Iran Ta Gargadi Isra’ila Kuma Tasha Alwashin Kare Shirinta Na Nukiliya
  • Gwamnatin Jihar Kwara Ta Kafa Kwamitoci 2 Don Tantance Wadanda Suka Yi Ritaya
  • Iran Ta Sanya  Da Ranar 30 Ga Watan Nuwamba A Matsayin Ranar Kasa Ta Tsibirai 3
  • Gwamnatin Yobe ta ƙaddamar da shirin amfani da ma’adanai
  • Real Madrid zata nemi diyyar Dala bilyan 4 daga UEFA
  • Manoma a Jigawa Sun Jinjinwa Kungiyar Sasakawa Africa Bisa Bada Tallafi a Harkar Noma
  • Rundunar Sojin Nijeriya Ta Shirya Wa Janar Musa Faretin Gama Aiki
  • An raba wa iyalan jami’an ’yan sandan da suka rasu a bakin aiki a Borno N63.4m